Tuesday, 4 July 2017

A UBA NA DAUKEKA 40 to end

[6/26, 10:04 AM] ‪+234 803 885 2783‬: _40-45_

        *A*
              *UBA*
     
*NA DAUKE KA*

  

_NA_
      _NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

K'alaman dr ammar su suk'a sara k'anta hak'an yasa jik'in ta duk yayi sanyi, tabbas tasan tana son dr Amma k'uma yanzu no time for love!...

     " Bayan sun 'isa mak'aranta domin gabatar da exam Shukrah tace husna?

  " yes? Yaya akayi?

       " Why not bazak'i yarda da soyayyar dr ba yana sonk'i yana k'uma fatan aurank'i?

       " Hmm Nifa bak'insa nakeyi ba no! Yanzu k'insan ina cik'in risk, ya k'amata mu aiwatar da Abunda yak'e gaban mu...

     " Ni dai shawara Nak'e bak'i wallahi k'ada kiyi sak'i Na dafe!...

      " Shukrah kenan, ku kukeyin soyayya, k'unfi mu sanin sirrin ta....

       " Ai ita soyayya wanda yak'eyin ta shiyasan sirrinta...

      " Murmushi husna tayi ta cigaba da k'aratun ta!...

   ●●●●●●

  Tunda Dr ya bar cik'in mak'arantar ya k'asa sukuni, tunanin sa daya idan husna tace bata sonsa yaya zaiyi? Wayyo Allah nah Allah kataimaki ne Ak'an husna! Wallahi inasonta ya jingina da motarsa.Bayan wasu mintuna zakri ya kirawo shi cik'in raunin murya yace manyan mu!..

     " Kai kafiya zolaya dr kwana biyu ina k'ashiga ne?

       " Kai dai bari soyayya ta sani agaba!...

      " Haha! Kace dai munk'usa shan biki?

      " husna bata sona zakri bata kaunata i have try my best Naga ta soni but still tak'i morethan 4 to 5 years!..

      " Subhanallahi! Wacece wannan yarinyar dr! Amma bata kyauta ba!...

      " 'yar gidan Sa'id fa!..

   " Sai da gaban zakri ta wadi, sannan yace husna wai?

     " Yes! Ita dai....

   " Shiru yayi bai k'ara cewa komai ba!....

      " Zakri yak'ayi shiru ko k'asanta ne?

     " Jan Numfashi yayi yace....wata *cakwakiyar*... k'ayi kasada sosai wallahi husna ai tana da masoyi tun tana k'arama...

     " Dr baisan lokacin da hawaye yafara wank'e zuciyar sa ba!...

    " Haba dr menene Na kuka kuma haba sai kace ba Namiji ba?

  " zakrai! Husna itace zuciyata Nasata a cik'inta tuntuni bana tunanin zata fita...

      " ya k'amata k'abi komai A hank'ali Ammar......

     " son husna yazama abun fahari azuciya ta, ta yaya zan cireta? Itace macen da Na k'eyiwa kallo Na k'ara. .. k'alami idan tayi dole asaurara....

      " *Wata sabuwar*...Dr ka zurfafa Allah to ya tabbatar da Alheri...

     " Yanzu kayi magana Da zak'a sak'ani a firgeci....

      " Haba mazan jiya wane mu?

      " Hahaha sai Na shigo...

●●●●●●

     Kwana biyu sa'id zazzabe yak'eyi jik'in nashi sai addu'a yau ma yana kwance a k'an gado maryam ta shigo...

    " Tana shigowa ta zauna kusa dashi, A hank'ali ta shafa masa kirjin sa, cik'in kissa tace haba mijina ya k'amata kabar tunanin nan fa! Su husna sun k'usa ganawa fa baifi wata daya ba!...

     " K'allon ta yayi cik'in sarkar k'iyar murya, me isa bazaki faranta min ba? Nifa mijin ki ne! Kisani maryam ina sonki kuma farin cik'in ki shine nawa!...

     " Cikin wata murya mai raunana jiki tace kayi hak'uri sweetie please ka yafemin! Wallahi soyayyar k'ace yasa idona ya rufe...

      " Kiso abunda Nakeso shine kina sona! Idan ban Aure Asma'u ba zan iya rasa k'aina rayuwa ta zata....

     " Haba sa'id ya'isa ya'isa ta fashe da k'uka ko wacece wannab yarinyar asiri tayi mak'a wallahi mijina ba hak'a yak'e ba da, Sa'id please kacere maganar Aure arank'a....

      " Wane hucin numfashi ya fitar yace how? How?...

      " Any how mana, wallahi sa'id sonk'a bazai barni na zauna da kowa ba...

      " Maryam Ba canjajjan ra'ayi aso asma'u Nayiwa Alk'awari, Duk zafin yanayi bana tunanin rabuwa da'ita....

      " To shikenan sai k'ayi tayi Ni k'uma daf Nak'e da rabuwa da kai sai kayita Auranta....

     " Hannun ta yarik'o maryam babu kyau son zuciya!...duniya bakasan ta'ina zata ja kaba...

     " Rungumesa tayi soyayyar k'a bazata sa Na fahimci kalamank'a ba All i know i can't stay with any woman...

     " Abunda Nakeso kisani shi Aure *Nufi ne Na Allah* kuma Never ask why I love you, just accept that I do, and that I will...for the rest of my life...

    " Nima hak'a mijina *mijin mace daya*...

●●●●●●

    Lady's Na k'arbo recording d'in sun hanasu shiga sun k'uma basu rashawa yanzu 12 saura rabia ki tafi gidan radio.. fatima kema ki tafi gidan jarida, Ni da shukrah zamuyi gidan tv....

     " Okay bari mu tafi 'sisters mu kula mu kuma kiyayye....

     " Kowa yasa wannan A k'unnan sa, Duk abunda Na ambata shi zak'u ambata...Allah yabamu sa'a...

    Kowannen su suk'a huce gurin Aik'i husna Suna isa zuk'a Nuna iD suka k'arasa An hada musu k'omai su ake jira...

     " We Are so greatful husna, munji dad'in Aik'in ki, da mun k'asance muna jin tsoron fad'in gaskiya sai mun tace but yanzu muna da freedom we stand for our country....

    " weldone oll, let me start..

_Assalamu Alaikum_

_Masu sauraro ayau alhamis cik'in labaran mu Na sati..._

    _Ni husna sa'id hameed Nake gabatar da shirin cik'in yaren hausa da Turanci...._

      _Wai hausawa suna cewa Kyakyawar zuciya sai mai rabo,...._

    Duniya ina Zaki damu?

_kunje cewa bincik'en da'aka gabatar Na jami'o i akwai jami'ar da bata yarda A gabatar musu ba? Hak'an ya tabbatar mana da itace jami'ar da Ake zargi dangani da yiwa mata fyade da k'uma tsafi.._

     " _Hukumar k'asa tayi tattaunawa da hukunci mai tsauri dangani da rufe jami'ar da ake zargi Nan da 'yan watanne indai har Ansamu kwakwaran shaidoji_

    _Kunji cewa rashin tsafta da wank'a Akan kari yak'an haifar da kuraje da cututtuk'a musamman a wannan yanayi Na zafi......_

   _Gyara munanan aiki da shiri mai kyau dangani da kokarin sadaka da karatun alkur'ani da kyautatawa mutane Na cik'in abubuwan da'ake so mutum yayi domin samun da'acewa a cik'in watan azumi_....

       _Hukumar bincik'en tak'ama manyan motocin da'aka kama da kwaya da munan abubuwa aciki...wa'iyazubullahi ko me za'aci idan ab hadu da Allah? Wai cutar da Dan uwank'a musulmi...kamar yadda zanga zanga ta wak'ana jam'i an tsaro sunci zaku cafki mai wannan aiki..._

   " _'yan tada kayar baya sunyi barazanar sace d'uk wanda yak'ara kai rahoton su..Tu Allah ya'kiyaye mu.._

   " _An bada sanar wa k'an kowanne gida adage da k'aranta Alkur'ani domin rugurguza matsafan k'asar Nan.._ Allah yasa mudace...

    _Anan Nak'awo karshen shirin sai mun hadu asati Nagaba_

     _Ne husna hameed sa'id Nak'e ci muku Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu...._

     We stand for our country we Alharis tv..

    " See you next week!..

    " Husna manager yana k'iranki..

     " ina kike samun wa'innen labaran mudamuki da harshashan rahota bama samu...

     " Manager All i what from you shine ka jajjirci ak'an gaskiya!.....

   " Fita tayi street sai skull bayan sun gama exam dinsu suk'a tsaya tattaunawa ....

    " Rabi'a ce tace gobe zamu gana exam so daga gobe zamu bar skull zaku bini gidan mu sai mu zauna!...

     "Fati tace Yanzu zamu fara badda k'ama domin yanzu zasu fara fataucin mu ....

    " Shukrah tace zasu fara neman mu da sulhu tuk'unna kafin su karkashe mu....

     " Husna tace muna buk'atar mini computer da new phone dan hak'a kowa ya siya, Duk inda zamuje ya k'asance a kunnen mu wayan mu takasance Available...

" shukrah da rabi'a suk'ace mun sanar da iyayen mu komai kuma sun amince kuma yak'amata k'usanar....

    " Fati ce tace muna gayawa Abbanmu zai ceremu askull din nan mun sanar da mama kuma she is with us, so in muna buk'atar taimako mugaya mata!..

    " Yau zan k'unna wayata zan k'irawo asp so zai bamu taimako yanzu mission d'in mu akan soyayya ne so fati zan dinga baki wayar ...

    " why not you! Ke zakiyi husna babu abunda baki iya ba so ke zaki cewar shukrah...

     " okay let go out for reading....

     Suna fita Husna tayi kicibus da sa'id cik'in murna tace Abba nayi murnar ganin k'a Am so happy kasan gobe ne final but ank'ara mana wasu time d'in...

     " Wank'a mata mari yayi...

*Urs Nana diso*

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[6/26, 10:04 AM] ‪+234 803 885 2783‬: _45-50_

        *A*
              *UBA*
     
*NA DAUKE KA*

  

_NA_
      _NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

K'e wacce irin mahauk'aciya ce ke wacce irin jak'ace? Bakida hank'ali? Ko ni nabak'i izinin fara aiki?

     " Kuk'a tafashi dashi Abba k'atsaya ka saurare ni please...

     " Bakisan wasa kikeyi da rayuwar ki ba? K'insa kaway'inki aciki? Kina mace zak'ice zakiyi fada da matsafa da gogaggon 'yan duniya? Wai ke son talak'awa da tausayin su ko? To yanzu zasuyi ta farautar k'i kamar Namin daji....

     " Wato duk rainon danayi azuciya ta yatashi abanza? K'insa rayuwar ki a risk????.....

     " Hawayen fusk'ar ta ta goge sannan ta duba kusa dasu babu kowa wayan aljihun ta tacere sannan tace Abba ka kallah ka gane....

      " Yana fara k'alla yace subhnlhi wannan wani irin bala'i ne su wanene wayannan sukayi mata hak'a innalilahi....

    "kuka tafashi dashi tace bak'aga komai ba Abba wannan k'adan daga cik'in mugayen abubuwar da ake gudanar wa a mak'arantar nan, wannan talaka ce babban ta dak'yar ya samu kud'in da ya k'awota mak'aranta, k'aduba k'aga bayan cin zarafin ta da suk'ayi sai da suk'a kwakule mata ido wannan ak'an ido na Akayi, yaya ubanta zaiji ballantana mahaifiyar ta? Itama 'yace mai buri kamar kowa, in bamu taimak'awa Na juna ba tayaya zamu zama adalai? Mai Mak'arantar nan shine shugaba...

    " K'asan adadin matasan da suk'a lallata da shaye shaye? Bakasani ba? Idan d'an kani yak'eyi yaya zakayi?

     ka duba batan yara da kazamin aikin da suk'eyi tsafi domin samun duniya wato muk'ami da kudi da sauran su ....

    " Mu k'asance masu adalci acik'in zuciyar mu banason k'aratun journalist kai kabani gudunmawa, abbana mai imani ne, Abbana jarumi ne, Abbana yana sona, kawar da zalunci shine burinsa...

    " *Kina zuciya ta* husna bana son in rasa ki shiyasa, i stand for my country, tashi yayi zai tafi...

     " Ta baya ta rungumeshi i love u my dad!...

     " Jiyowa yayi ida nunsa jajir yace *ina tare dake* ke kula da k'anki ki kuma kirani in baki yadda da mutum ba zan bak'i tsaro zan kuma yimiki addua...

     " Nagode abba amma Please karka saka kanka a damuwa babu a bunda zai sameni...

   " Tohm husna yana tafi yana share hawaye har ya isa gate!...

    " Ina kika shiga husna munata nemanki?

    " Rabi'a ina tare da Abbana ya nuna bacin ransa daga baya kuma ya yarda.. ina mamak'in irin son da yakeyi min wanda ba yayiwa fati....

    " Ashe k'in fara fahimta!!!...

Hmm tuntuni na fahimta sai yanzu naga ba yayiwa fati irin son dayak'e min, bakiga yadda hank'alin sa ya tashi ba idanu wansa duk sunyi ja...

    " hmm Nidai banda tacewa kizo muje mu huta tun dazu muk'e abu daya...

    " ke kije, but ne inada Aiki agabana yanzu ma lab zanje...

     " Ki kula Allah ya k'iyaye mu!...

      Ameen!...

  ●●●●●

Who is she??? Wanene ubanta? Wanene ina tambayar ku ? Kugaya min kafin Raina yak'ara bace...

    " oga Kayi hakuri wannan Zafin karage shi domin bashine mafita ba!...

     " Sanin yarinyar bazai mana wuya ba inaji 'yar talakawa ce gidan tv suk'a bata kudi domin tayi musu...

     " hahahahaha Talaka jinin sa agurinmu ai bakomai bani ba...

     " Kuce akuya ce yarinyar muna bata k'udi zata nutsu...

     " Duk fa kasuwan cin mu yatsaya saboda ita, kudaden da zamu samu a sattin nan are much but dole mu tsaya...

     " Bafa kowa bace illar daliba acik'in uni dink'a...

     " what what? How come ta san sirrin makarantar? kudi shine burin mu sai muna kashe ran talakawa muna shan jinin su...

   " hahaha hakane ogah ....
 
    " Dan haka yarinyar nan ku kasheta ku kawomin jinin ta...

     " Angama...

" ku dakata! Kasheta hatsarina mudai yi kidnap nata zaifi...

     " Eh saboda tana da sirri sai mu karbe daga nan mu kaita kasa...

" hahaha mu sha jini mu samu kudi muyi wanka da naira...

    " Inason A karawa asp hassan ya koma dsp domin shi zaiyi mana Aikin ta...

   " Angama commissioner zaiyi...

●●●●●

hello asp sa'id ne please yau zaku fara aikin ku amma ku kula...

   " Hmm husna tasa k'anta a tension sosai abanza zata mutu wai ita mai kokari...

    " Za dai mu mutu, Ne fa haihuwa Nakeso maryam sai da nace kada kisha magani sai da kikasha...

     " Nema so nak'i Na ganni da jariri...

     " Sai nayi aure k'inga sai tayi ta haifa min Allah kayiwa asma'u jagora Allah Katsaya Mata kabata sa'a...

     " mtseww!!! Tsinanniyar yarinya duk tabi ta addabawa mijina...

     " K'anki kike zagi domin batasan k'inayi ba...

    " Kuka ta saka tabar gurin....


  ●●●●
Husna please kitsaya muyi magana please!..

    " Okay inajin ka kayi sauri kirana akeyi...

     " Shukrah duk tayimin bayanin komai , kuma Allah shi zai kareku *jarumta a zuci tak'e* Nasan husnata zata iya kuma zaa kashesu kamar yadda suk'e kashe wasu we stand for our country.....

     " Jiyowa tayi tare dayi masa wane irin k'allo mai ciki da k'auna tace Nagode!..

    " Kina sona???

        " Kallonsa tayi tace No time for love...

    " Juyawa yayi ita kuma ta huce staffs tana shiga taga wane lecturer dinsu baffa tana ganin girmansa sosai a mak'arantar...

     " Cik'in isa yace husna ko?

     " Tace kwarai mai halin manya dattijon arzuki, zuciyar ka fes tak'e bama acik'in talak'awa Allah yak'ara girma...

     " Lok'aci daya yaji ta fasa masa kai, A nan k'uma yafara dariya to zauna zamuyi wata maganaa da k'e...

      " Tsayuwar ma ta'isa k'ana zaune ina zaune abun bazai bada ma'ana ma!...

     " Shiru yayi tare da dan murmushi cik'in kwalkwal warsa yace tabbas yarin yar nan ba sak'ara bace to yanzu ta'ina zai bullo mata?

     " Dama inaso nayi mak'a godiya Akan an dauke ni aiki agidan tv alharis....

     " Yauwa Dama maganar zanyi mik'i Amma bazaifi k'i bar wancan Aik'in ba zan samar miki lecturer acik'in university d'in nan!...

    " Haba DanAllah?

       " kwarai kuwa muna biyan dubu dare biyar kowanne lecture ke kuma zamu baki million daya!

      " Me'isa baza'a bani daidai dana sauran ba?

      " Saboda *ke ta dabbance* mak'aranta tana ji dak'e...

      " Sai A lok'acin ta fahimci inda ta dosa! Cik'in ladabi tace kowanne uba yana son 'yar sa tayi karatu please sir in tambayi ka?

     " kinada dama!...

           " Nasan k'ana da 'yaya ko da mata?

     " yarana mata biyar namiji daya...

     " Mashaa Allah! Yanzu to wayannan matan kakaisu karatu sai ace an sace uku kuma akayi musu kazafin neman maza kuma aka kashe su yaya zakaji?

     " A hanzarci ya miki, ki'iya lafazin ki domin kisa bakomai bani....

     " Sauran guda biyu yaran nak'a sai suka fara tsafi suna satar mutane domin neman duniya kuma sunfara haka sanadiyar makarantar da suka shiga!....

     " husna watch you mouth!...

     " Dank'a guda daya dakake burin ya zama abun alfahari dai yafara shaye shaye....

     " is enough ke banson iskan ce da rashin mutunce 'ya'yan nawa?

     " Nasan radadi kak'eji acik'in zuciyar ka to wayanda abun yafaru akansu sunfika jin zafi, kunce amanar kasar ku in baku gyara ba, kuma kuma yaaran ku sai anyi musu, rayuwar azzalumai zata kaskanta, Allah zai wulakanta ku! Kagyara zuciyar ka domin 'ya'yanka suyi alfahari dakai ka kyautata ma'amalar ka wallahi wallahi mutuwa gaskiya ce......

     " Ke kinada shedu ak'an hakan?

     " Allah shedani kuma kaima kasan me ake aikatawa! Bansaniba ma ko kana cik'in su to asannu zaku kare ina k'an hanyar kaiwa ga hukumar kasa daga lokacin zaka gani duniya ba matabbaciya bace... I stand for my country kuma wannan maganar dak'a gayamun kamar duniya sunji ne......

     " Hahaha mu jini muk'e sha, small rat zakixo hannu fada da zaki sai shiryayye kina rat bak'i isa fada damu ba so be careful watch your step!....

     " Ni da Allah Na dogara bak'u isa kuyi min komai ba! Mu zuba mugani...

   ●●●●

    Hello! juliet how are you? please i need to meet you...

     " Okay sa'id am on my why to meet you!.....

     " Please juliet inaso kiyi excort dina ga hukumar kasa!...

     " What wrong kakeso kaganta?

      " Ina da problem i have many to talk about with her...

     " Example?

" Bergous university...

     " gyara zamanta tayi baisan a nan tak'e aiki ba! Hahaha kanada shaida ne?

   "Yes i have!...

       " okay zak'a iya bani sai nabata...

     " ke fa your are nonsense how can i give u?

   Kifa arniya ce bakyason musulmi ban tunani zaki kai mata juliet kin canja da ba haka kike ba!...

   " Musulman naku ai su suka canjane...

    " mtswee idiot! Oyya work out know.l...

     " Hmm kaima kayi kasada da life naka!..tana fita ta k'irawo oga ta sanar dashi komai....

   " why bazamu k'ashe shi ba?

     " Bashida hujjah a hannu sai a baki! Yarinyar nan zaku k'ama...

Ya Allah! Husna ta kwaso aiki...

●●●

    " Rab'i a kuyi maza mubar skull d'in nan sai kuma ranar grad kuzo muyi maza suna biye damu...

    Kafin kace me sun bar mak'arantar tuni suk'a huce gidan su rabi'a mum dinsu tanata shi musu albarka...

     " mama ce ta k'ira husna cikin murna ta dauka hello mamana k'ina lafiya husna Allah ya tsareki Allah ya baki sa'a kisaka wane  wata waya nasa ansamiki a jaka ki kula yanzu zaa fara farautar ki 'yata ko anan aka gama k'in cika min burina dan hak'a ku kula...

    " Tohm mama Allah yana tare damu...

    " rabi'a kije k'i sanar da ma'aikatun hukuma sun rufi bergous university domin gabatar da bincik'e maza maza kisa black kaya kiyi ahank'ali...

    " Fati ki buga a jarida kuyi hank'ali ku kuma fita a kafa tare da likaf da zarar kun gama ku dawo kuma a k'afa...

    " okay Allah yabamu sa'a!..

●●●●●

Shukrah ne zanje labaran sati kada k'i biyu ne zan fita da mashin d'in can! Mini computer ta tana jak'a mcard yana cikin safata dan haka ki kula ni Nayi gaba...

     " Tana isa alharis tv tafara labaran ta Anan ta tabbatar an rufe bergous sak'amakon zarginta da'akeyi ......

    " Nan mutane suk'a dinga zanga zanga akan sai sun kashe maci amanar mak'aranta  .....

     " Husna husna kina ina? Kina ina? Karki fito titi zasu kamaki...

    " Abba ina tsakiyar titi ma...

    " kiyi hankali oya  ki gudu gasunan...

    Juyawa tayi taga rundunar mutane dayawa a guje ta kara gudu nakara gudu....

    " Hello husna husna kinajina?

     " Abba sun k'amani ma ka gansu....

     " karki kashi abun k'un nan k'i ki barshi...

      " Tohm...Juliet ce ta cillata cik'in mota da ko waje baka gani...

     " hello ogah gata mun k'amata  ....

   ku tafi da'ita bayan  gari ku zaneta sai ku karbi abun hannuwan ta....

     " Wata k'ara husna tayi shukrah sun k'amani...

     " Nan da nan rabi'a ta dau waya hello ank'amata baba!...

  Rabi'a dole sai mun samu shaida daga videos da audios zamu iya yin wani abun...

     " Suna hannun ta baba wallahi suna hannun ta...

    " kashe wayar yayi sannan yaja tsaki...

      " kunga babana yaki fahimtar mu..

    " Shukrah ce tafara duba number asp hassan cikin sa'a ta kira shi ta sameshi cikin sauri tace barka da aiki asp...

     " Am ..nown dsp who is on line?

    " Shukrah ce k'awar husna ankamata nan ta bashi labarin komai...

   " K'addai itace wacce bergous ya k'ama? Yace zai bani millions in narufe kara yanzu lokacin zuwa na taimaki husna zan bada raina ak'anta mik'ewa yayi yaja mota...

      Hello! Dr husna tana cikin matsala sun k'amata, ga number dsp dashi zakuyi aiki ka kirashi Dan Allah kafito da husna dan Allah..

    " inshaa Allahu bari nayiwa wasu magana domin tayani aikin...

      Hello dr ne okay am hassan kasa abun kunne zanje gurin su, zasu fadi hanyar da'aka kamata sai kubi...

   ●●●●

Wayyo Allah nah, baku isa ku kasheni ba sai kwana na yak'are...Dabbobi...

    " juliet ce ta kifa mata mari ta buga mata bak'i sai jini .....

    Ogah mun samu computer amma na bude invalid tak'e sawa, wayanta kuma babu komai...

    " Kuyita duk'anta har sai tafada...

    " husna cikin galabai cewa tace kai karen farauta mai bakar zuciya ne da Allah Na dogara jinina bazai shawu ba k'uma asirin ku ya tuno daga yau mara imani asararre k'afin ka mutu zan nuna muku illar abunda kuka aikata...Da kuna amfani da ilimi da kunada imani da bakuyi abunda kukayi ba tunda kunki tuba to mutawa itace ta dace da makiya addinin Allah..

    " Cik'in ta juliet ta nausa...

    " wayoo...

●●●●●

  K'u kalla ku gani zata k'ashe min 'ya please kuyi saurin nemo inda tak'e...

     " Dr abun k'unnen ta ya wadi fa! Na kanta bazaisa muga komai ba cuz sun sak'a wasu wayoyi...

    " Juliet ce tace you fa taceje bak'i kinada taurin k'ai wato bazaki fadi inda mcard yak'e ba sai na kasheki ko?

     " Ni bana zalunci bazan fada ba in k'in isa ki kasheni wayoo cikina kidaina duk'ana...

    " Duk'anki bazan daina ba har sai Na kasheki...

     " To jahila raina ahannun Allah yak'eyi bak'i isa k'i kasheni ba...

    " ogah kabarni Na kasheta juliet ta k'ifawa husna mari taurin kai ne da'ita...

     " Karki damu gamu nan zuwa yanzun nan zak'u ganne ni zan k'asheta Na sha jinin ta....

     ●●●●●●●

   " Hello! Dsp Dr ammar ne ga police 20 sunzo ka karasa gurin sa?

     " Gani nan ina last door da zanje gurin sa...

     " Amma babu hadari kuwa?

     " Allah zai karemu ku tayar da motoci kowacce magana in yafada zakuji nafada sau biyu...

     " Okay muje can d'in...

      DSP hassan welcome ka chanja shawara kenan?

     " Oga yazama dole ai, domin kareka! Yanzu ga takardar case d'inka kayi abunda kaga dama dasu...

     " hahaha u are brilliant zansa akara maka girma, ita kuma yarinyar nan yanzu zance ak'asheta...

     " dsp ne yayi saurin gyara zaman sa to ina kuka ajiyeta ne?

     " Tana birtas kusa da abeas...

        " Dsp hassan ne yace abeas kusa da ruwa?

    " yes suna cik'in wane gini na suna hawa Na farko kaga babu wanda ya'isa ya k'amata!.....

      " Hahaha lallai oga kaima fa shaidani ne! Suna birtas kusa da abeas kusa da ruwa gini na farko...

     " Nan dr yace mu huce da abirtas da sauri...

     " oga ne yace Dsp yanaji kana maimaitawa?

     " Hmm ogah ai dole Na maimaita domin kuwa na yaba basirar ka bari ne natafi sai kajine....

     " Hassan wannan ya kasance sirri tsakani na da k'ai....

     " oga ai angama tun dazu na dauke sirrin ka...

     " yauwa Dsp..

   Da sauri dsp yafito yace kun kai kun kai?

     " Mun kusa amma akwai matak'an tsaro fa!...

    " ku kashe su ku kashe su...

       " Dsp hassan ne yaji ana cewa a kamoshi bai san lok'acin da ya dira ba sai gudu suna binsa yana gudu....

     ●●●●

Mamace ta kirawo sa'id k'ana ina kana ina zasu k'asheta...

     " Cik'in nishi yace saura minti daya Na kai gurin sa nema yanzu sukagama duk'ana inaje na karye a hannu...

     " innalilahi duka ku biyun zasu k'ashe zanzu kana ina?

    " Na shigo ma cikin taron duniya na yana shiga yace ku gafurcine ya saka mcard atv...

     " Manyan mutane dayawa suka dinga wannan 'yatace wannan ma haka wasu suna kuka wasu suna ihu dole a kashe bergous da magoya bayansa a rufe makarantar a rugujeta...

   Sa'id ne ya zube Anan baban rabia yayi asubuti dashi...

   ●●●●●
 
Juliet tana jin harbi ta fita aguje tafara harbe itama husna tana nishi Tasa mcard tuni tayu broadcast d'in abubuwan da'akeyi a makarantar...

    Gari kowa ya hargetse sai ihu suk'eyi suna dole akashe su...

      Husna tun da tajin gina da kyar tafito tana fitowa taga an harbe Dr Ammar akafa...

    " Tuni aka k'ama bergous da magoya bayansa guda 40 da 'yan kungiyar tsafi...

    " Mama tana sauka itada su nena da ummi suka ganta ta wadi....

     " Directly asubuti akayi da'ita dr Ammar ma hak'a ...

     Dsp hassan sun dak'eshi aka yana asubuti....Hakan zai iya sa yarasa hankalinsa...

     " Dr Ammar an harbesa akafa in basuyi sauri ba sunce yank'a kafar za'ayi....

     " Sa'id yan asubutin London inda akace duk'an da yankan da suk'ayi masa sai anyi masa Aiki.....

   MUJE ZUWA...

- *YAYA RAYUWAR HUSNA ZATA K'ASANCE?*

- *WA HUSNA YA K'AMATA TA AURA?*

- *WA YAFI SUNTA ACIKIN SA'ID, AMMAR DA HASSAN?...*

  - *WAYAFI CAN CANTA TA AURA?..*

     - *SHIN MARYAM ZATA AMINCE DA HUSNA BA 'YAR SA'ID BACE BA...*

   - *SHIN HUSNA ZATA IYA ZAMAN AURE DA WANDA TA DAUKE SA A MATSAYIN UBA?*

     *SHIN WACCE CAK'WAKIYAR HUSNA ZATA SHIGA A GABA A YAYIN DA TAJI SA'ID BA MAHAIFIN TA BANI?*

     .....INA JIRAN COMMENT D'INKU....

*Urs Nana diso*

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[6/26, 10:04 AM] ‪+234 803 885 2783‬: _50-60_

        *A*
              *UBA*
     
*NA DAUKE KA*

  

_NA_
      _NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

Babban Asubuti aka k'ai husna, Dr aisha ce da'ita da likitoci suk'ayi k'anta ba'afi minti 30 ba Ak'a sak'a mata k'arin ruwa da allurai...

      " Dr sumayya ce tace Dr Aisha wannan 'yar k'ice?

    " Me k'ikagani?

         " 'yar tak'i ce mashaa Allah, ga nutsuwa Amma taji jik'i but nan da kwana biyu zata warware...

    " Dr Aisha ce tace hmm Allah dai yak'ara lafiya...

   " Nena ce tace To ne bari naje Na zauna da'ita...

    " k'inga Nena inna sai waya tak'eyi wai kuje gidan ta k'u zauna, k'insan wannan asubutin su ba'a zama sai dai azo...

     " To shikenan, yaya jik'in Dr Ammar din?

    " Anfara yimasa aiki yanzu inaje Ancere harsha shin...

     " ohh ne Nena  fada da zak'i sai an shirya, yanzu shi sa'id d'in yana ina?

    " Sa'id yana america k'insan su da k'a ida, suna tayi masa gwaje gwaje sai sun gama za'afara Aikin gobe zanje can d'in...

     " Ummi ce tace sister ai ance akwai wane asp da ak'a bugi k'ansa ma, amma wai anyi masa Aiki har ya farfado...

    " To Allah yabasu lafiya bak'i daya kuzo mu huce...

    ●●●●●

  Fati ce ta shigo tana ta k'uka hak'an ya batawa, maryam rai cik'in masifa tace...

     " K'inje k'in hade da husna k'unje kunyi wai taimako to mahaifin ki yana can ransa A hannun Allah...

   "  Haba ummi why bazaki dinga fad'in Alheri ba? Why bazak'i dinga addu'a tagare ga husna ba? Kema fa 'yar kice kamar yadda nake 'yarki....

     " maryam ce ta wank'a mata mari tayi cik'in masifa tace so so so? Husnar zanso? To bari kiji i will never lurv her am telling you kuma ki cire son ta aranki domin annuba ce, bala'i ce fitina ce...

     " haba ummi please stop it please mana wannan harsh words d'in ak'an husna haba ummi?

     " To uban dakike alfahari yana can rai a hannun Allah ko rayuwa ko mutuwa! Wacece tajawo? Husna Annoba ce Na fada sai k'i dak'eni....

     " Ke mahaifiya tace bazan daina gaya miki kigyara ba Amma idan Na bata miki ki yafemin....
 
    " Mtsww Anjima flight d'ina zai tashu so kije gidan nena..

    " Tohm ummy kiyi masa sannu k'afin muzo please!..

   ●●●●

    Dr Aisha ce ta huce asubutin da Ak'a kwantar da dr ammar tana zuwa itama ta duba shi, likita hope babu wata matsala?

    " yes Dr jikin sa Alhamdulillahi sai dai ambatar wata yarinya da yak'etayi dazuma da mumy d'inta tazo kawai fada mata yak'eyi a aura mata yarinya!...

     " Okay bari Na ganshi...

   " Sannu Ammar hope kafar da sauki?

      " Dr Aisha please pray for me..wallahi ina sonta...

    " Dr aisha ce tace cool down dr yanzu lafiyar ka ake bukata! Ka kwantar da hankalin ka, zaka aureta indai  matarka ce..
  
     " Dr please husna tana cik'in lafiya?

     " Husna ta warke dr sa'id ne ke fama yanzu...

     " Nagode wa Allah naji dadi, ki gaida min ita ciwon kafa ta shi zai hanani zuwa gurin ta sai hawaye ya zubo acik'in fuskar sa...

     " Dr Aisha ce tayi mamakin ta'inda ya santa hak'a tafita tana tunani...

    ●●●●

  Lok'acin da fatima ta tafi gidan inna su jamila suk'a gani sun sak'a inna agaba...

    " Fati ce tace menene hak'a menene hak'a kunzo kun sakata a gaba sai k'ace masu binta bashi....

      " ke fati dak'ata munaso muji ta 'inda sa'id yasamu 'ya wai husna!...

      " ke jamila nace miki shigeya ce k'inki ki yarda....

    " Ke anty maimuna kada k'i kara fadar maganar nan acik'in gidan nan husna yaya tace sai naga uban da zakuyi...

    " Anty jamila ce tace ke fitsararre ya ke bar k'akar tak'i tayi magana mana...

    " inna Dan Allah kiyi magana mana bak'ije k'alaman da suk'e fada ba?

    " inna ce tayi dariya duk dai akan 'yar balarabiyar nan kukeyi husna ikon Allah, To husna ba 'yar sa'id bace ba...

     " Fati ce tak'e kokarin waduwa, anya inna bak'i samu matsala ak'anki ba?

     " Husna sunanta asma'u itace 'yar dabaku so tazo duniya ba...

    " Anty jamila ce tace wannan karatun da'kikeyi a baibai kiyi mana karatun ABCD...

     " Mtsew to dai 'yar Aisha ce wato matar hameed...

   " waduwa ya suk'ayi tare da salati innalillahi wainna illahir rajiun...lahh ha'ila haillal lahu ....Aisha kice da gadonta agidan nan?

    " Anty jamila ce tace ai tunda tazo naga k'ama shikenan an kasamu...

     " Kuma ita sa'id  zai Aura???

    " Fati ce tafashi da kuka mai tsanani Amma inna A matsayin uba ta dauke shi...yanzu matar babana ce?

    " Ba dai ta zama ba tuk'unna Kuma sa'id zai iya rasa ransa a kanta...

    " inna na yarda soyayyar da Abba yak'eyi wa husna wallahi ba irin tawa bace ba, inna yaya husna zatayi da soyayyar dr??

    " Allah shiyasan mijin ta acik'in su, Amma inaso kisani karki biyewa mahaifiyar ki, kauna ce tsakanin husna da sa'id tun tana cik'in ta nan inna ta bawa fati duk labarin komai...

    " Cik'in hawaye shabe shabe tace yaya husna zatayi inna dan Allah ta aure abbana please, Bamaso mu rasashi...

     " komai na rayuwa hakuri yak'e bukata kuma wanda husna takeso shi za'abata....

    "  Hmm cewar fati sannan tafita...

●●●●

   Haba husna menene ma'anar abunda kikayi? Kinaso kice wannan Aikin da mukayi  baza'a yada mu agidan tv ba?

    " Hawayen fuskar ta ta goge tace shukrah kenan, akan abunda nayi za'a saka hotona?

    " eh manah...

" To kesani banyi ba domin a soni ko kuma asani akafafan labarai, Duk abunda nayi daga Allah dan hak'a banda ra'ayi ta fashe da kuka...

    " Ta fashi da kuka lallai husna, to menene na kuka?

     " Halin da Abbana yak'e cik'i bansani ba...

  " Husna ai sai dai mu godewa Allah domin kuwa duk suna cik'in koshin lafiya...

    " Har Asp? Da dr?

" kwairai kuwa, domin kuwa komai Na mumine alheri ne, Allah nagode mak'a, shukrah da fargaba nakeyi wallahi kar acemin wane ya mutu...

    " Ai husna karki damu ke dai mu cigaba da godewa Allah Abisa ni'imomin da yayi mana...

" tabbas bazan manta ba ya zo a hadisi cewa:
(( Abin mãmãki ga al'amarin mumini; dukkan al'amarinsa alheri ne, kuma bãbu wanda yake da irin haka in banda mumini, idan yalwa ta sãmeshi sai yayi gõdiya sai hakan ya zama alheri gare shi, in kuma cuta/abin qi suka sãmeshi sai yayi haquri sai hakan ya zamo alheri gare shi ))...Muslim.

Wato Allah ya yimana ni'imomin da bamu isa mu qidãyasu ba; don haka ya wajaba mu yawaita godiya gare shi, kuma ma in muka gode masa abisa ni'imar da yayi mana to hakan zai saka ya qãra mana wata ni'imar ! Duk wanda yakeso ya godewa ni'imar Allah to sai ya kalli na qasa dashi cikin falala !!!....

     " Haka yak'e husna...

    " Ina son ganin Dr shukrah hadani dashi please awaya...

    " Shukrah ce tace hmm anfara son dr kenan?

      " Murmushi husna tayi tare da Sallama...

     " Gimbiyata zuciya ta tak'asa samun sukuni domin ganin kyawawan fuskar ki, da jin kalaman ki masu hargetsa tunani na...

     " Wane dadi taji har cik'in zuciyar ta sannan tace Ina fatan kana cikin koshin lafiya?

     " husna koshen lafiyata bazai tabbata ba sai har in k'in aure, husna ina sonki ki yarda aturo please...

    " cik'in sanyin murya tace karka damu dr na Amince...

     " wata kabbara yayi yes i love you habibi i love you ..ohh my god such a nice word...

    " kashe wayar tayi cik'e da murmushi tace shukrah na damu da dr...

      " hmm Allah ya tabbatar da Alheri...

     " Amen..

Kwana biyu soyayyar husna da Dr ta kara kulluwa tunda taje taga Dsp yace hakura Allah yabata Na gare, tabbas husna tafada cik'in kogin soyayya..

●●●●●●

   Tun lokacin da Dr Aisha ta'isa airport directly asubutin ta huce tana isa tatarar dashi ajingine...

     " Ah alhmdlh kace jiki yasamu sa'id sannu kaje ina alfahari dai kai, ina kaunarka...

     " hawaye ne ya zubo acik'in idanun sa ya rik'i hannun ta nasan k'ina sona Amma Dan Allah ina neman Alfarma Agurinki...

    " Fadi kowacce iri ce ne mai biya makace....

      " Ina son husna ki aura min husna...

     " Dr Aisha batasan lokacin da tayi baya...

   INA GODIYA GA D'INBIN MASOYAN LITTAFINA😍ALLAH YA BIYA MUKU BUKATUN KU....INA GODIYA👏🏼

.
*Urs Nana diso*

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[6/26, 10:05 AM] ‪+234 803 885 2783‬: _60-70_

        *A*
              *UBA*
     
*NA DAUKE KA*

  

_NA_
      _NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

   Daman Nasan baza k'ibani ba, K'insan yadda Nake sonta mama? Rashin husna zai haifar min da matsala sosai da sosai, kokarin tashi yak'eyi Amma yak'asa please mama please, k'insan auren so anan ake k'ulla zumunci, idan k'uma bandace da husna ba Na hak'ura, yafara tari....

    " Dr Aisha ce ta matso idanuwan ta cik'e da hawaye, Sa'id idan Nace husna bata dace dak'ai ba to Nayi karya, idan Nace banaso ka aure ta to na zalunci k'aina, Sa'id karka manta Da abu guda daya husna *A UBA TA DAUKE KA*???

     " Mama k'e dai k'i amince Dan Allah, domin duk soyayyar da nakeyi wa husna abayyane tak'e mama tun husna tana ciki abban ta yace Abani ita k'ada ki manta..

    " Tabbas ban manta ba indai nice Na Amince sa'id domin bazan taba mantawa dak'ai ba kayimin biyayya, ka soni kuma ka karemin mutuncina gurin kishiyoyi na, Yanzu kuma k'anason 'yata, tayi murmushi mai tafiya tare da hawaye, Allah ya tabbatar da Alkhairi, Amma kayi shiru da zancen sai An sallame ka...

     " Mama nagode zan k'ula da husna, zanyi kokari gurin cik'a mata burinta...

     " Murmushi tayi tace bari naje Na dawo tana fita suk'ayi kicibus da Maryam, sannu Dr Aisha ko?

    " Eh k'ina lafiya ya mutan gidan nak'i?

     " Lpy! Ya jik'in mijin nawa?

      " Ah jiki yayi sauki fa, A dai k'ara kula dashi...

     " Tohm mungode, tana shiga tace oya ga Abinci!..

     " Tohm, maryam k'un hadu da maman asma'u?

    " Wane k'allo tayi masa wacce asma'un?

     " Wacce zan aura mana!..

    " Wai Dr aisha?

" Eh ita, ta sanar dani cewa ta amince Na aure husna...

    " Cokalin hannun tane ya wad'i, what aure? Wai kai menene banayi mak'a menene bana bak'a?

    " Babu amsar tambayar ki, kuma aure da zarar Naji sauk'i...

      " Hmmm Za'ayi rashin mutunci kenan, kowacece zatasan ta aure mijina k'uma yanzu zan koma sai k'a kirawo asma'u ta zauna mak'a, tayi hanyar fita....

     " Dariya yabani yace maryam tausayi kike bani, saboda sai k'infi hauk'ace wa gaba...

     " Kaji tausayin k'anka kuma ka siyarwa k'anka bala'i...

    " tsak'i yayi ya kwanta!..

●●●●●

    Ke fati dagaske husna ba yayark'i bace ba?

    " Sadiya wa yagaya miki?

    " Dazu naje Naji su maman mu suna zancen, gaskiya fati bakida hank'ali bazaki taya mamanki kishi ba? Ke bakya kishi komai abbanki yace husna? Uhm jan gaskiya bakida kishi...

     " To yaya kikeso Nayi yaya kikeso, Husna ta yaudari ne tasamin sonta...

    " So ai kiyi cancel din son nan kisa kiyayya, yanzu ne lok'acin da zak'ici ubanta, ki takura mata, da k'anta zata bar gidan...

    " hahaha hak'ane fa  nagode sadiya..

    " Suna gama tattaunawa husna da shukrah suka shigo cik'in sallama mai k'arfe, su anty jamila tagani azaune...

    " ina kwanan k'u..

" anty sumayya ce tace k'inga yarinya mai k'aidi, uwarta tayi sak!...

    " Tsayawa tayi tana k'allonsu...

     " To rasa k'unya kallon mu kikeyi wato, k'inje kina amfani da uban da bana k'i ba shigiya...

     " Shukrah ce tace me tayi muku kuke zagin ta hak'a...

    " Husna ce tayi murmushi, dallah zo mutafi sallama ce nayi musu, Na kuma gaidasu to Ai bazancen wata maganar...

    " Uwarki kike gayawa haka banza yar iska...

      " Sumayya ce tace wayasani anje anyi wa sa'id asiri dan anga yanada kudi, harda aurensa za'ayi...

    " Husna ce ta riko hannun shukrah, come let go please suk'a shiga bangaren inna...

    " Husna har k'un dawo?

     " wallahi inna mutanen gidan nan suk'a tsayar dani suna wane banzan zance...

     " Me sukace miki?

" Wai Nayiwa abbana asiri domin in aure shi jiwane hauka?

     " Inna ce tayi shiru sannan tace kyalesu ke basuda hank'ali ai...

     " Inna Dr Ammar yanaso yazo ya gaida k'e...

     " Wanene Dr kuma?
  
     " Shukrah ce tace saurayin tane da tak'eso kamar me yanzu ya matsu ma su turo...

     " Inna ce tace wai k'ina sonsa?

    " Murmushi husna tayi tace inason sa inna please ki sanar da Abbana!..

     " Ina zan iya ai da daddare zakuji gurin sa kya saanar masa....

     " Fati ce tace Allah ya rabumu da munafukan mutane maciya amana!...

    " Husna ce tace Amin dai fati, Amma fati yaya kike wasa da sallah yanzu?

    " ke kike bada ladan ne? Ke kike bada ladan ne? Ba zanyi ba!..

    " to daga fadar gaskiya ikon Allah,...
 
     " uban wanene yace ki fada...

     " inna ce tace fati banson sha shance fa!

    " Husna ce tace kyaleta Inna kada tayi sai me Amma ke sani sallah tanãda muhimmanci sosai a cikin addini, cikin ibãdu bãbu ibãdar da Allah SWT ya kirãta da cewa Imãni ce in banda sallah !!! Sannan ita ce ibãdar da Manzon Allah SAW ya ambaci duk wanda ya barta da cewa kãfiri ne !!!

    " Mtsewww banza jahila, maciya amana...

    " shukrah ce tace wai menene hak'a fatima...

     " Bansa dak'e ba da wannan annobar nak'e..

    " innace ta wanka mata nari kishirya ki koma gidan ubanki mara kunya...

    " Inna please ki kyaleta Allah ya shiryeta,...

Maryam ce taja jak'ar ta tafi gida tana shiga tarar da maryam tanata masifa...

   " menene ummi? Yanaga har k'ndawo?

     " ke kyale mahaifin ku wai aure zai k'ara..

" k'i barta ta shigo da k'aina sai nafitar da'ita..

    " yauwa fati yanzu naji zance!...

   ●●●●●●

   Husna k'in gayawa abban nak'i?

    " Murmushi tayi tace ya k'amata kaje ka duba sa!...

    " Au bak'isan naji bani?Ai yana babban asubuti agarinnan..

    " Haka inna tacemin ina fatan kace abinci?

    " eh Naci, yau gani ga husna har tana nuna dakuwa akaina, Dadin da nak'eji ba zai misaltu ba!...

     " Ganin farin cik'in ka shine ganin nawa...

     " Sun kusa minti 20 suna hira daga nan ta huce zuwa dak'in dasu nena suk'a zauna...

     " Nena Dazu nazo kina bacci...

    " Husna ai bina zakiye mutafi sai na auramiki dan kasar mu...

    " Ummy ce tace nena karkisa husna kuka mana bakisan dr takeso ba?

     " Shikuma sa'id d'infa?

     " Ni dai ki tayani addua please...

     ●●●●●●

    Duk'a family suna Asubuti anzo duba jik'in sa'id tunda su husna suk'a karasa takeson ganin sa cik'in ladabi tace Abbama yajikin nak'a...

      " tsayawa yayi yana k'allon ta har kusan minti 7 Jiki Alhamdulilah ya nak'i jik'in?

     " Lafiya lou, Dama inason nagaya maka iyayen dr sunce zasu turo...

    " Babu shiri yafara tare...
 
     " Sannu abba bari na miko mak'a ruwa...

    " Barshi kawai dr kikeso?

    " cikin kunya ta daga k'anta to shikenan bayan anyi zaman makokina sai su turo...

    " Cin hanzari ta juya ta k'alleshi what? Amma wannan wacce irin magana ce...

     " Husna ina sonki zaki Aure ne???

      " Ji tayi tun daga k'anta yana sarawa, wane abu taje kamar a mafarki zan aure ka? Innalilahi wainna illahir raji'una...

     " Kuka ta sak'a tafita gurin su, inna abba abba?

     " menene husna kika fito afirgece?

      " Wai ne yak'eso wai zan aure shi, shikenan abbana ya samu matsala?

     " Inna ce tace ai ba sa'id ne ya haife ki ba, hameed ne ya haifeki....

    " Cikin zare ido tace kema inna kema bakyasona kenan ku...

    " su mama jamila ne sukace anaso ana kaiwa kasuwa ai ubanki ya mutu tun k'ina ciki 'yar nan...

   " husna ce ta matsa k'usa da mama tana fadin mamata bazakiyi min karya ba Ki gayamin gaskiya please ta fashi da kuka....

     " Asma'u sa'id d'an k'awunki ne ba shine ya haife ki ba, sa'id yaya yak'e agurin ki...

     " Mik'ewa tayi tana fadin No No No *A UBA NA DAUKE SHI* No impossible...

     " Mik'ewa sukayi suk'a nufota tana k'okarin waduwa kafin su karasa itama ta wad'i Nan da nan akayi cikin asubuti da'ita....

    " Maryam ce kuma ta shigo tana wallahi sai Nace ubanki, maciya amana daman ba 'yarsa bace ba, wallahi bazaki aureshi ba, tsinannu wallahi sai nasa akasheki.....

     " Dr Aisha ce tace k'e dak'ata! Ba'a auren aka aure k'i, kuma husna sai ta aure sa'id tunda d'anane....

    " inna ce tace Aa aisha kibarta ta aure wanda takeso kada ku kashe yarinya...

     " Maryam ce tace Naga ta inda zata shigo dan uwarta, mugaye matsafa antsafeshi ansaka masa son yarinya acik'in zuciya..

    " Mama jamila ce tace k'ada kiyarda maryam wannan mutane basu da imani...

    " ke maryam fita fita anan nace ki fita , kice kuma babbar mahauk'aciya domin bak'i isa hana abunda Allah ya nufa ba.....

    " Tana daga ido taga kawunta na ta masifa ba shiri tafita . ...

   " kuyi hakuri Yarinya...

      " inna ce tace babu komai...

     " Dr Aisha kuwa lok'aci daya tashiga tunani, ita bawai batason sa'id ya aure husna bani aa tana tsoron da fargabar da matarsa zata sak'a husna...

MUJE ZUWA.....

*WANNAN SHAFIN NAKUNE SAK'ON KU YANA RISK'ATA 'YAN GROUP DINA (NANA DISO NOVELLAH) ALLAH UBANGIJI YA SAKA MUKU DA ALHERI, YA TSAREKU SHARRI MASU SHARRI.*

    😍😘😍  _Barakallahu fiykum❤❤❤ Am so grateful for your loves /cares and comments.. May the blessings of Allah fill your life with happiness and open all the doors of success now and always...😘 Nana Diso love u oll....Daku Nak'e 'Yan group d'in NANA DISO NOVELLAH_💙

*Urs Nana diso*

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[6/26, 10:05 AM] ‪+234 803 885 2783‬: _70-80_

        *A*
              *UBA*
     
*NA DAUKE KA*

  

_NA_
      _NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

Tunda husna ta suma hank'alin sa'id ya tashi hak'a yasa, yaji k'amar shine Sanadi, 'yar kwanciyar da yayi inna ta shigo ranta A bace tana zanbada masifa....

    " Inna Dan Allah kiyi hakuri in ban sanar da husuna cewa ina sonta ba zan yaudari k'aina, kuma kina ganin yadda Dr aminina yak'e kokarin tusa soyayyar sa...

    " Dak'ata kafin Na bata mak'a, kafin raina ya bace wallahi wallahi kacere son husna, kamaji Na rantse maka ko? Domin sai wanda tak'eso za'a aura mata to k'aje kaga halin da tak'e ciki ita ba mahaukaciya ba ita ba mai hank'ali ba dame zataje da wannan fitinanniyar 'yar tak'a kokuma da matarka wacce batasan darajar mu ba ballanta na mijinta.....

      " Shiru yayi yana sauraron inna idanu wansa duk sun canja k'ala cikin ladabi yace Tohm inna k'insan ni daya ne dank'i to ina tabbatar miki ajali na ya matso indai bak....

     " To idan anjalin nakane yazo ai ka huta, Amma ne bak'a isa kayimin dabara ba bak'aisa ba...

     " Inna Indai ba husna ce tace batason Na ba bazan rabu da'ita ba...

       " So? Aikuwa bata sonk'a da ace tana sonk'a da bata suma ba lok'acin da k'asanar da'ita kaje ka nema wata husna ta dr Ammar ce...

    " shiru yayi bai kara firta komai ba sai numfashi da yak'e jaaa...

    
   Cik'in budewar ido ta riko hannun Dr Aisha tace mamana mafarki Nakeyi kokuma gaske ne...

      " Husna so kikeyi Na rasa ki? Husna bazaki kwantar min da hank'ali ba?

     " To mama yaya zakuce abbana bashi ya haifeni ba, kuma wai wai zai aure ne?

       " k'i daina kuka ki kwantar da hank'alin ki wanda kikeso shi zan bak'i yar lelen mama...

    " kuka takara sak'awa ne bazan aure abbana ba Dr Nakeson Na aura banason...

    " inna ce ta shigo jikinta babu kwari tace husna ki kwantar da hankalin ki shima sa'id din baisan me sonsa ba shiyasa....

     " Dr Aisha ce tace ai inna abun bana zafi bani ba fahimta fuska, Allah shi yak'eyin komai sai mutsaya mugani....

    " To ba dole naji wane iri ba yarinya ta sume ak'an ance ana sonta!...

    " Cik'in k'inkina tace nifa ina son Abbana Amma *A uba Na dauke shi*...

      " Nena ce tace to husna saunawa ana irin auran nan? Tunda dai aure bai haramta ba to k'i Amince mana ki duba halin da yashiga saboda ke!..

    " ummi ce tace gaskiya Nena karkuyi haka, ku dubi soyayyar dak'e tsakanin ta da Dr Ammar mana? Shekara hudu yana jiranta...

    " Hmm shikuma sa'id d'in haka akace miki baya sonta to tun tana cik'in mahaifiyar ta yace abashi ita sai ki lissafa iya adadin shekarun ....

     " Husna ita dai kuka tak'eyi mai ratsa jiki...

    " Ummi ce ta dafata k'i kwantar da hank'alinki sai wanda kikeso zaki aura ....

    " K'allon ta dai kawai tayi sannan ta shiga toilet alwala tayi sannan tafito tayi sallar ta tare da Addu'oin Ya Allah kafitar dani daga matsalar dana k'e ciki ya Allah k'azaba min abunda yafi alheri....

    " cikin murya kasa kasa mama tace husna?

    " Na'am ina suleiman kuwa?

    " hmm ai kwanaki ya kirawo ne har yayi aure da 'ya'ya biyu, wallahi mama bansan bason ya suleiman nake ba sai daga baya nagani shakuwa kawai mukai....

   " Allah yabada zaman lafiya, Abunda Nak'eso dak'e yanzu kiyita Addu'a husna, ina sonki wanda kikeso shi zan aura miki....

    " murmushi tayi da baikai baka ba...

●●●●●

   Ummi ince dai k'ince ubansu?

     " Fati husna ta tsafe mahaifin ki son da yak'eyi mata baza'ace komai ba, naso ci mata mutunci sai naga ashe bata san ma ba mahaifin ta bani ba, kuma bata sonsa hak'am zaisa nasamu nasara A k'anta....

     " Hmm Ai ne nafison ma tazo domin mu dakata muyi mata murus...

   " Namiji baiyi ba yanzu sa'ar 'yata zai auromin!..

   " Ke dai kibarni da 'ita zanyi maganinta...

   " yauwa fati haka nakeso dak'e, bari naje gida Nadawo dakko min katan din taliya da lemo kisan amota...

    " Naga abba yabar kusan dubu dari biyu a bed dinsa na dakko miki?

     " Yauwa 'yar zan baki kema ka sonki sai Na dawo tukunna, oya bye bye....

    " bye...

●●●●●

   Hajiya hajiya hajiya ta fashe da kuka...

      " Maryam lafiya kikazo menene ?.
  
     " Wai sa'id ne zaiyi aure kuma...

    " Aure kuma? Aure?

     " kuma husna zau aura!...

    " Laaah cin amanar har tak'ai nan..

     " Baffa ne yafito yace k'in ga yanzu kika gama cewa k'in tuba, kuma Wannan yarinyar 'yarki ce idan kika bata tarbiya me kyau to fa babu shakkah rahamar Allah zata tabbata agareki Amma idan kikace zaki lallata ta to kisani kiwo ce agareki..
   
    " Haba kawu Amma ace yarinya ta girma agidan ta yaci amanar ta?

       " Amana? Lallai bakisan mecece Amanar ba?

     " k'insan kuwa shakuwa da gatan da mahaifiyar husna tayiwa sa'id? To baro kije kafin Alhaji hameed ya mutu sai daya bada umarnin aurawa sa'id husna...

     " maryam ce tace ta yaya zata shigo gidana sa'id nawa ne ni k'adai....

      " Yimun shiru sha sha sha, bayan ki yanada damar auren uku, maryam kada shedan ya rudeki kiyi hank'ali da duniya, Dama abaya nace kiyi ahank'ali...

    " Gaskiya baffa ne...

   " yimun shiru ke tara kudi a gidan duniya kisha sha'anin ki Amma kisani alheri lahira zai biki, idan bak'iyi hakuri ba to babu inda zak'ije, majaifiyar husna bakisan wahalar datasha ba k'insan cewa har kosai ke babu wahalar da batasha ba, Amma daga karshe wane result kikagani nata....

     " hajiya tace tabbas hak'ane kam Ai dama rayuwa sai Ana hakuri da juna....

     " Dama ai ne bakwaso na, Kuma bazan barta ta shigo ba...

    " To sai kije kiyi abunda kikaga zaiyi miki daidai...

    Fita tayi bata k'arasa ko'ina ba sai gidan Aminiyar ta tana shiga tafara bata labari....

   " cikin hanzari aminiya tace kishi ? Ai yanzu an daina wanga abu...To mekikazo nayi miki na rak'aki gurin boka afasa auren ki jawomin masifa, Ai yanzu andaina bin malamai malaminki shine ibadarki ki kaiwa Allah kukan ki zakiga cigaba...ke bari ingayamiki maryam kitashi ki kiyiwa mijinki biyayya koda ta shigo sai dai ta bik'i Ne kishiyoyina har guda biyu duk binsu nakeyi azauna lafiya duk wacce ta cuceni kanta tayiwa sak'ayya kuma ai tana gurin Allah...

    " Aik'in banza kawai wazakiyi wa wa'azi kinga fita ta...

    " A dai bi duniya asannu domin ba matabbaciya bace ba...

●●●●●

   Dr ne yashigo cik'in asubutin hannun sa rik'e da leda sai da yafara zuwa dak'in sa'id suka gaisa ya huce dak'in da husna tak'e...

    " cikin murmushi tace sannu da zuwa...

    " tsayawa yayi yace me kuma yak'e damu gimbiyata?

   " Kuka tafashe masa, kana sona dr?

    " husna wannan wacce irin zance ne?
 
    " indai da gaske kakeyi gobe adaura aure ne na yafe komai...

     " Husna wane abun ne yafAru?

    " Abba bayason auren mu!...

    " haba husna kece me cewa aji tausayin mutum kinga halin da yak'e ciki ne kije kigani, kibare ya samu sauki sai ayi maganar da turowa.....

    " Tabbas bakasan auren to ina yimaka albishir da kakusa rabuwa dani...

    " Husna kome fa zak'ice Sa'id sai yaji sauki fa, wai meke damunsa kamar ciwon zuciya...

   " cikin mutuwar jiki tace ciwon zuciya innalilahi....dr garin yaya?

    " ke zan tambaya da ance abun bai kai haka ba Amma yanzu sai tsanane yak'eyi, kome yasaka aransa?

      " Cikin taushin murya tace Nece dr.....

     " Ke kuma?..

" Boye boye banamu bani gwara nasanar maka duk halin da ake ciki nan ta gaya masa komai da komai...

    " Shiru yayi yace addua zamu dage da'ita babu abunda yafe addua, husna in ke matatace zab aure ki ya tashi yabar cik'in asubutin ciki da kunci.....

    "Wane sabon kuka takara fashewa dashi tana ya Allah ka zaba min mafi Alheri...

●●●

    Hello Ammar tun dazu nak'e jirank'a a asubuti but k'aki kafito...

     " zakri k'a tausaya min mana k'asan halin dana k'e ciki ne?

   " me kuma yafaru dr?

    " sa'id yace amanata yasan inson husna amma ya...

    " Dakata dr kai kace Amanar kanka, ka mata lokacin da nake cimaka kabi a hankali? Amma gaba daya ka ki saurara ta, to husna itace Asma'u da sa'id yake yawan zancin ta, kai kafi sanin ta da husna ce...

    " Wallahi bansani ba zakri, yanzu yaya zanyi da soyayyar ta...

    " ka cigaba da Addua Allah yakawo mafita...

    " haba zakri nasan inason husna amma bazan iya jure halin da sa'id yake ciki ba tun muna kanana yake cimana asma'u amma yanzu na butulci masa...

   " Matar mutum Ai k'abarinsa...

   ●●●●●

   Sa'id ne ya dafa bango ya karasa dankin da aka kwantar da husna tana zaune Amma tayi tagumi ya kusan minti 5 atsayi sai kuma cikinsa yafara zafi cikin karfin hali ya koma cikin room dinsa...

    Bayan ankwana biyu husna tana tare da mama dasu nena tana cik'in palour taji sallamar Rabi'a da gudu ta rungumeta bestie kwana dari?

     " Lafiya kalou sis ina mama mugaisa gaisawa sukayi sannan tayi cikin dak'i da'ita...

    " ke zance naji daga sama wai sa'id ke sonki....
   
   " Wai yaya za'ayi haso wanda na dauke a matsayin uba?

   " to ina dr d'in naki?

        " shima yau kusan sati daya ko waya nakirawo baya dauka...

    " Husna Ne kawarki ce bazan baki muguwar shawara ba ki aure ya sa'id Dan Allah ko dan cetoshi daga halin da yak'e ciki ki duba yadda dukiyarsa take rawa domin baya kusa da'ita duk kuma saboda ke, kuma nasan kina istikhara...

    " ina yi wallahi da idan dr bai kirawo ne ba bana samun suk'uni...Amma yanzu dubine sak'ayau, Nidai Nagaya miki....

    " Tohm bestie ya nagank'i da tak'ardu lafiya?

   " Nazo ne ki danyi min bayanin wasu abubuwa....

    " tohm Allah yasa nasani rabi...

    please bayani k'an Neman, ilimi yada ilimi da azumi da zakkah da itikafi da aikin hajji....

     " Wai bari dai nayi miki bayani kadan kadan..

   " yauwa nagode..

    Neman ilimi

_Wato neman ilimi na addini wajibi ne don haka ya zamanto farkon abin da aka saukarwa Manzon Allah SAW shi ne: (Yi karatu) !!! Don haka ya wajaba mu nemi ilimi kuma tsaftatacce ingantacce wanda zai amfanemu a duniya da lahira._

         Yada ilimi

   *Wato yad'a ilimi na daga yankin Imãni don haka duk abin da mutum ya sani wanda yake ingantacce to ya sanar musamman a lokacin da yasan hakan zai amfãnar, sannan duk wanda yasan wani ilimi kuma aka tambaye shi akai to ya fad'i abin da yake gaskiya, in kuma bai sani ba to rabin ilimi ne mutum yace: Ban sani ba!!!*

Aikin hajji

  _Wato aikin Hajji ibãda ce mai girman gaske; ga wanda yaje yi dan Allah, kuma ya tafi da kud'in halal sannan yayi aikin irin yadda Manzon Allah SAW yayi; to, anai masa albishir da kankare zunubai ta yadda zai dãwo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifeshi !!!_
  
Ittikafi
   *Wato itikãfi shi ne lizimtar masallaci don bautar Allah, kuma ana yin itikãfi ne a watan azumin Ramadãn a goman qarshe don neman dãcewa da daren laitatul qadri. Kuma ana iya yin na wasu kwanakin ba sai goman ba a'a zã'a iya yin qasa da hakan. Sannan akwai dõkoki da qa'idojin yin itikãfi don haka sai mu nemi saninsu musamman tun da ga azumi na gabãtowa !!!*

Azumi

   _Wato azumi babbar ibãda ce wacce ta qunshi kãmewa daga cin abinci da shan abin sha da sha'awa da fad'a da zãgi da gulma d.s.s. tun daga fitowar alfijir na biyu har izuwa fad'uwar rana da niyyar bautar Allah SWT !!!_

Zakkah

  *Wato zakka wãjiba ce a addini, kuma ana fitar da ita ne cikin jinsin abubuwa uku in har sun kai nisãbi wato: Kud'i da Amfanin gõna sai kuma Tumãkai. Da ace mãsu dukiya cikin musulmai suna yin zakka kamar yadda Allah yace ayi to da musuluncin ya wuce yadda muke ganinsa yanzu !!!*

   Gasunan amma bayanin a kadan ne...

  Me yawan kenan Nagode sosai Allah yasaka da alheri ne zan tafi sai naga card..

    " haha tohm shikenan...

Husna yaya maganar samarin nak'i?

   " Mama Na aminci zan aure abba, Amma kusani biyayya zanyi muku domin naga k'unfi sonsa fiye da samari na kuma Anty maryam batasona...

    " To husna ai rayuwa bakowa ke sonka ba kaidai kazauna da mutane lafiya sai Allah ya taimaki ka kuma naji dadi Allah yayi miki Albarka yasa kizama uwa tagare...

    " mama yaushe zaku koma ne inason na bikune...

     " Yanzu sai after bikin ki zamu koma fa!...

   " cikin mamaki tajiyo bikina kuma?

   " eh manah Ai nan da 2mouth za'a sak'a
..

   " shiru tayi tace Allah yajikan Abbana, da duk musulmai...

     " Ameen!!!...

 
●●●●●●

   Yau sati 3 da k'ai kudin auren husna dubu dare da hamsin sun sak'a biki wata daya, tundaga lokacin fa su husna suk'a kasa samun kullum tunani duk ta wada Amma kuma bata bari agani barri inna dak'e jiran k'ada...

    " Su fati kuwa kullum kara haukaci wa sukeyi jira sukeyi kawai A daura auren...

    "  mama naji kina kirana?

    " eh ki dau motata kije ki duba jik'in sa'id kar asallame shi ba kije ba...

    " Ne mama da k'in...

    " au husna baki isa nagayamiki kiji ba?

    "  yi hakuri mamana bari naje Na shirya, Dak'i ta shiga less d'inta blue tasaka riga da skirt sunyi mata kyau bama irin dukiyar fulanin ta ko ina yayi bul bul, mayafin ta fari ta yafa! Abarka da fara red lipstick tasaka ta huce zuwa asubutin...

    " Husna tana kofar da k'in taje sa'id yana cewa inna husna bazata zo ba husna bata damu dani ba...

     " Ni dai kaci abincin Dan Allah kaci...

    " Allah bakina babu dadi ko da kuwa nace...

    Fadawa tayi tare da sallama inna ina yini?

   " lpya..

      " Cikin kunya tace ina yini abba yajikin naka?

    " murmushi yayi yace lafiya..

    " inna ce tafito ta barsu agurin..

   " husna ce tayi karfin hali ta zuba masa abincin ta kawo masa tas yacinye har da shan lemo yanata janta da hira amma bata kulashi..

    " Husna kina sona?..

    " *A UBA NA DAUKE KA!* Zanyi rayuwa da kaine abisa kaddara...

     " Bakomai naganki kusa dani ya 'isa koda baki soni ba...

    " Fita tayi tahuce gida...

   A Kwana atashe babu wuya agurin Allah yau ne k'amun husna tayi masifaffan kyau dangi sunzo anyi harka sosai, washe gari aka daura Auren sa'id da husna akan kudi dubu dari biyu...

   Mama sai fada takeyi mata wa'azi kuwa babu k'alar da batasha ba ga sai kuka takeyi dakyar aka banbare ta daga jikin mama...

    " Shukrah ce tace amarya yaya?

     " Ke dai bari wai wanda Na dake gani amatsayin uba shine ya zama mijina...

    " kinga shanyi maganin ki ke kikaga zaki iya tunani...

  Dr Ammar kuwa gaba daya yabar garin...

   ●●●●
Karfe tara  Aka kai husna gidan ta kowa sai yabon gidan yakeyi saboda kyau da tsare sai da ya rage babu kowa sai ita kadai...

  ●●●●●

  Maryam kuwa gigicewa tayu hankalin ta yakara tashe dataje gidan sa na sultan road aka kai husna.

    ●●□●

   Abokanan ango suk'a shigo sukayi mata nasiha suma suka fita, Sa'id yana shigowa cikin murna yasa suka gabatar da sallah yayi mata addua sannan taje ta kwanta!..

    " Ganin sa tayi yana tunk'aro ta nan da nan tayi maza ta matsa please abba karka matso Allah bazan...

    " husna Nifa mijin ki ne yanzu ki manta da baya ki fuskance gaba...

   Ni dai kada ka matso please ta fashe da kuka...

    " rungumeta yayi cikin murya mai rauni yace husna kada kice haka yau shekara daya inada bukata please husna....

    " Tureshi tayi tace haba wannan wane abun kunya ne tabar dak'in...

    " Sa'id kuwa hawaye ne ya zubo masa, Shi kadai yasan irin feeling din dayake daga karshe alwala yayi kama sallolin sa....

*Urs Nana diso*

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[6/26, 10:05 AM] ‪+234 803 885 2783‬: _90-100_

        *A*
              *UBA*
     
*NA DAUKE KA*

  

_NA_
      _NANA DISO_

http://nanadisoo.blogspot.com

Da safe Husna ta shiga wank'a sai alokacin ne tak'ara ganin gidan, ita k'anta sai da tace mashaa Allah, Dakuna hudu kowanne da toilet ga kitchen kato, ga palour guda biyu baranda, ko'ina ya tsaru sosai da sosai Amma kuma sai taga wane bangare kafin ka karasa k'amar nata ne but da gate atsakanin su...

    Wane material d'inta tasaka doguwar riga ta k'amata, sannan tayi steps da dankwalin hoda da lipstick ta shafa ta dawo k'an gado ta kwanta ga yunwa da takeji...

    " Sa'id ne yayi sallama yashigo cikin dak'in sannan ya zauna...

     " A hank'ali tace ina kwana?

       " Lafiya lou, k'inci Abinci?

    " Shiru tayi ko k'allon sa batayi ba..

    " Ga sabuwar wayar da nasiya miki sai ki kunnata, ki fito ki karya kuma, zanfita ne yanzu...

     " Cikin wata shagwabab beyar murya tace to ne k'adai zan zauna?

     " bazan dadi ba fa zandawo..

    " Gaskiya tsoro nakeji Abba...

     " To ko zaki bini muje?

      " Daga k'anta tayi Alamar eh..

     " Rik'i hannun ta yayi haba my husy Allah in ba dole ba bazan fita ba, zanbiya gida zan kuma je kasuwa kayan mu sun iso, zan rarraba...

      " Shiru tayi ta k'au da kanta...

     " To shikenan bari Na fasa tunda bakyaso, kuma ko nazauna ni ba kulani kikeyi ba, yanzu gurin maryam zanji na danji dadi ai..

    " Har cikin ranta taji haushin maganar sannan tace ai ban rik'i ka ba, ni babu ruwa na kada ace kasuwan cin ma na haka....

    " husna kenan idan k'in hanani ai ba lefi baniba Ni mijin ki ne...

     " Jiyowa tayi ta kalli sa wane kyau yakarayi hancin nan mashaa Allah duk da dai shi ba wane fari bani ba Amma kyansa yana rudarta uwa uba addinin sa ga tabon sallah yayi shar a goshin sa....

    " hularsa yasaka yace karki karacemin Abba, kike rani da kowanne suna inma sa'id ne kicemin in nakara jin kinci min abba ranki sai ya bace...

     " To idan ba abban ba me zance mak'a kada kamata fa *A UBA NA DAUKE KA* Tayaya kuma zan tsaya ina...

    "Katse ta yayi adaba karki manta _hucaccan abu yana bayan mu fararre kuma yana gaban mu, mu rayu acikin yanzun mu domin shine ke gari mu,_ Dan Allah ko bakya sona ki kula dani please...

   " jikin ta taje yayi sanyi sannan tace ni ai bance bana sonka ba...

   " husna kenan ai aikin mutum shi ke nuna maka inda mutum ya dosa..husna ke kyakyawa ce kina da kyau ga kyan sura, Na zama zabinki yanzu kuma nine angonki...

    " Wata kunya ce ta lullube ta, mikewa ta zata bar gurin riko hannun ta yayi...

     " Husna ta yaya zanyi na fassara kalma so da baki? Ko ko inyi misalin Nakeji ajiki, ido baya iya gani so k'an iya saka tunani me kyau ko ko mune...

     " Tak'e jikinta ya mutu wane yar taji ajik'inta kara riko hannun ta yayi sai ta wado jikin sa, kamshin turaren shi ya dinga duk'an hancinta ....

    " Tare da ke husna babu mai rabamu, ki dubi yadda na dawo saboda soyayyarki, ki tausayamin ki soni ko kadanne please...zani kiraki da mai dak'ina...

    " Dan Allah kasakine abb...

     " kina karasawa zanyi kissing d'inki..

    " Kanta ta shigar saboda kunya...

     " Ni nagani nagani da idona Na firta kalaman kauna, Na sak'i cikin Kalbina kike mulkin ruhina, jini fata da k'ashina k'inyo kamawa...

    " To to , sai ya sassauta mata rikon, a guje ta gudu dak'i tana hakk'i daman Abba ya'iya kalaman nan lallai indai zan cigaba da jin k'alaman nan to fadawa soyayyar sa bazatayi min wuya...

     " Sa'id kuwa jikinsa duk ya mutu directly gidan inna ya isa yana shiga yaga su baba jamila gaidasu yayi...

    " ohhh kaje ka aure 'yar da ka raina anya kuwa sa'idu kana da adalci...

    " baba sumayya ce tace mtseww ke kika tsaya kina asarar bak'in ki matar da ko san sa batayi ai ance dr tak'eso kuma sho yayi aurensa, Ai gangar jik'inta ya aura....

    " sa'id ne yayi murmushi yace koma menene ga k'ayan abincin kunan k'arasowa...

    " mama jamila ce tace gashi k'azama me kudi ko bama sonka ma soka dan abun duniya...

   " part din inna ya shiga, suka gaisa...

     " son ince dai babu wata matsala ko? Tunda yarinyar nan ba sonka tak'e ba kada tayi mak'a wata illar...

     " murmushi yayi yace inna wayace miki batasona yanzu ma dakyar ta barni na fito...

    " To alhamdullilahi haka nakeson ji ai..

   " Daman zancen kayan abinci ne da kayan da nake rabawa da sallah zaki lissafa...

    " Tun yanzu sa'id?

" eh inna ina tunanin zamuje umara ne, ni da k'e da husna da fati...

     " To madallah Allah yakara bude son...

   " Bari naje kasuwa kya turo akawo min...

Directly gidan sa yahuce yana shiga ya tarar da maryam sai kuka takeyi, sallamar sa k'e da wuya ta tashi ta rungume shi yanzu sa'id kayimun adalci gidan dana dadi ina burin shiga wata ta rigani shiga haba sa'id...

     " Da zaki kwantar da hank'alin ki da k'in moreni, ku shirya ga mukullin gidan ku shiga part d'inku...

    " Murmushi tayi tak'arba...

     " K'e kuma fati wallahi kika sake kikayi wa husna wata maganar banzan sai na saba miki yanzu matar ubanki tak'e...

    " Maryam ce tace an daiji kunya anji kunya...

     " dariya yayi yace dan ma ban aure yar shekara 8 ba...

      " Nan tace ai da sai kakara..

   "Guda daya ma kinkasa samun sukuni ballantana guda biyu...

   ●●●●●

    Ina amaryar tak'e ne ga munan mun karaso ....

     "Dariya husna tayi tace sassan nunku to....

    " Lallai gida mashaa Allah..

    " Haba anty ummi sai yanzu inata jiran ki tun dazu...

    " ke miyar kice ba'a karasaba kuma sai da muka biya aka kai gara, ina mai gidan Naki ko k'in boyeshi a d'aki?

     " Uban nawa zan boye? Haba Anty ummi dan Allah wai ku ko kunyar lamarin bakwayi?..
    
    " wallahi husna ki nutsu idan baki farantawa mijin ki ba naga wanda zaki farantawa kuma kishiya ta mallakeshi ke kinanan..

    " Suna zaune kuwa maryam da fati suk'a shigo eh gamunan mun iso miji dai nawane agama abubuwa afita, Fati tace mijin da ba'a sansa ummi, mutum ma yayi aure bai daina son mijin wata ba...

     " Anty ummi ce tace to wallahi idan baki gyara ba wayannan sai sun sakaki kin kusa hauka, Ni bari ma in tafi...

    " Haba anty ummi tafashe da kuka to yaya zanyi please...

    "Allah husna bazan zauna ba wannan abun tak'aice ke dakika zauna dashi kikasan halinsa ace bazaki faranta masa ba sai kiyeta daukar sa Amatsayin uban... *Duniya ce*

    " Kuka tasaka tatashi ta hau sama dak'inta ta kwanta gurin magariba taje karar motarsa mik'ewa tayi ta lika ta window din saman ta...

  " maryam ce tayi hugging din fati kuma tace sannu da zuwa Abba..

    " Yauwa kunyi abinci kuwa?

     " maryam ce tace munyi mana kodan mufaranta wa mijin mu, wannan gida dak'a gina Allah ya biyak'a da Aljanna..

    " Bakomai matata muje Nace abincin...

      " ita dai husna batasan meke damunta ba ta daije wane abu yatsata mata awuya...

    " sallah tayi ta kwanta sallamar sa taji...

   " Kin shiga kun gaisa dasu maryam?

    " Dak'ile tace aa!..

       " To kije ku gaisa k'inje....

   " ina zakaje da daddaren nan?

    " matar ammar aka kwantar a asubuti tayi bari kinga i need to go ko?

     " cikin ranta tace lallai ma dr har ya manta dani suna soyayyar su...

     " ko dai kada naje ne?

       " No sai kadawo ayi mata sannu..

    " Tana shiga tace sannun ku..

       " To muna fika kinshigo kiyi tsaigumin naki ne?

      " kyaleta nace ubanta ummi tsinanne ya mai bin mazan wasu...

     " wannan kalma tayi mata muni har ranta, cikin masifa tace in banda mijina yace nashigo ai da bazan shigo ba ....

     " Maryam ce tace Au mijina dai ina wane mijinki sai kace ya damu dak'e mtseww aikin banza...

     " habaici dai kalakala tana zuwa tafashe da kuka...

    Kullum husna bata samun suk'uni agurin su maryam abu tun baya damunta har yafara damunta gashi sa'id shima yaja baya da'ita wayar da sukayi da mamace yasa taje dadi ma...

Yau Alhamis girkin tane tana cik'in kitchen tana girki sai gashi ya shigo...

    Husna me ya hadak'i da maryam?

    " Ne yaushe rabon dana ganta?

    " To Amma kika zagi iyayenta? Haba husna me isa kullum sai kunyi fadane sai na tambayi ki kice karya akeyi miki? To kije ki bata hakuri...

    " wallahi bazani ba ai dama bakasona komai fati komai maryam husna kuwa ko oho baka damu dani ba...

    " Husna ke nace kibarni nasamu nutsuwa dak'e Amma k'inki, kullum aikin a uba kika dauke ni!!! Haba husna nifa yanzu mijin ki ne wata na hudu kenan da auren nan, maryam ita ta fahimce ni kullum tana tare dani ya kikeso to nayi? Da nak'an jura idan nayi azumin amma yanzu daga Nasha ruwa hankali yak'e tashi...

     " Kayi hakuri nasan nayi lifi Amma in...

     " ya isa kishirya kuje gidansu zasuje suyini...

    " Har yayi nisa tace please my husby i can't go..

     " K'amar daga sama yaji zancen jiyowa yayi tare da murmushi ina sonki husna ina kaunarki rayuwata is in complete with out you....

     " Cikin ranta tace ina sonka nima tuntuni kunya ta hanani nunawa...

   " yau kuwa wasu body hug tasa tayi kyau ko'ina ajikin ta moving yakeyi tana jin karar motarshi kafin su maryam su fito ta fito....

     " Yana fitowa ta rungumeshi kallonta kawai yakeyi hankali ta sumbace shi...

     " husna kice???

" maryam da fati kuwa kasa fito suk'ayi...

      Dariya husna tasaka tace bakina kwai zance mai dadi...mijina ne kai inasonka, zani siyo maka babban doki da dogarai suyi gadinka domin kar aidamun ka...

     " Husna kice yakara kallonta tun daga sama husna?...

   " hannun ta ta dora akan kafadin sa Kaine  likitan zuciya ta dak'e dubata, mai jinyar ta asa'ilin asa'ilin da kaban cuta, yau ta warke babu abunda ke damunta, Na dau alkawari zuciyar ka zani faranta, Abunda kayimin kudi bazasu iya biyanta, banaso murabe kasakani a kirjinka, biyayya zanyi ma kullum in gaishe ka....

    " Murmushi yayi sannan ya rik'i mata hannu suka shiga cikin gida abinci ta kawo masa sannan yace yafita bai dawo ba sai kusan karfe 11 ya kulle ko'ina dak'insa yaje ya kwanta domin gani yakeyi duk da sha'awar da ke dawainiya dashi husna bazata yarda ba dakyar dai ya daure ya huce dak'inta tana k'an sallaya, to tashi muyi sallah...

    " Nazata ma kayi bacci har inacewa babu sallama?

     " Murumushi yayi sannan sukayi sallah kwanciya ita dai tayi tare da addua can dare sai jinsa tayi gaba daya ya fita hayyacin sa Abun har tsoro yak'e bata...

     " A hankali tace please kayimun Hankali...

        " bakaramin jikata tayi ba shikuwa sa'id sai shimata albarka yakeyi...tun daga ranar kuwa kullum yana manne da'ita kullum abun har tsoro yake bata...

     " Maryam kuwa babu yadda batayi ba Amma abu ya faskara, wata rana zazzabi ya faskara ajikin ta babu kowa agidan husna tana shiga ta ganta a galabaice directly asubuti sukayi da'ita, Nan taga likita, tun daga lokacin maryam ta saurara wa husna...

     " Fati kuwa aure kawai takeso ta rasa yadda zatayi ta sanar da abban nata,  dayake yanzu suna shiri da husna tana shiga tace Anty?

   " Naam babbar yaya ya sanyi?

    " lafiyalou dama maganar abba...

    " ko ba maganar nazir ba nasanar dashi yace kice ya turo...

    " wane tsalle fati tayi nagode abunda nayi miki kiyiwa Allah kiyafemin please...

    " bakomai fati daman zaman tare ya gaje haka...

      " Fati tana shiga tace ummy danAllah kidaina tsokanar husna kullum burinki kici mata mutunci amma kullum kice abaya....

    " wallahi Na fahimta kishiya abokiyar zama ce kada ta cuceki kanta tayiwa, kinga sallah da nakeyi akan lokaci sai naji zuciyata kullum dada nutsuwa tak'eyi...

Kwanaki sai ja sukeyi husna kullum son mijin ta take karayi, yau ma tana kwance a kirjinshi yace yanaji jikinki zafi?

     " Husby tunda kwanaki bakina ba dadi kuma nayita jin amai Amma yak'i fito...

     " To ko asubuti zamu tafi...

      " No ni bazani ba yaushe zanje yemein please tafara yimasa shagwaba...

     " kissing d'inta yafarayi...., Ni kagayamin please...

    " gobe zakije... rungumesa tayi tana ta murna i love you husby you're my life...

     Washegari sukaje murna gurin su nena mama kuwa rungume husna tayi data fahimce tana zaune lafiya, mamata ina sonki.. nima ina sonki husna kibi mijinki kiyi masa tarbiya...tohm inshaa Allah kafin sukara zancen sai amai...murmushi dr Aisha tayi ta bata wane maganin tun daga lokacin bata karayin amai ba...

     Nena kuwa magunguna ta hada mata turaren wuta jibge guda...

    " Mama tace mlm saifullahi yazo kwanaki...

    " Cikin hanzari tace dan Allah fa?

    " Sa'id ne yayi saurin kallonta sai kuma tace Allah sarki...

    " yaran sa guda hudu yanzu..

     " Good kawai tace data lura ransa ya bace daga nan sukayi sallama suka huce airport...

     Cikin satin da ya huce akayi bikin fati ankaita gidanta mai kyau sa'id ya kashe mata kudi sosai kuma ya biya umarar har mijinta..

     " Yau husna sunata hira da maryam sa'id ya shigo yace aa *MATA NAH* Ina alfahari daku...

    Maryam ce tace Albishirin ka husna ciki ne da'ita...

    " kunya taji tayi saurin bin part dinta,

   " Sa'id kuwa aguje ya biyota please da gaske ya dauke ta cak sai gado nan ya nuna mata love kala kala....

    Bayan sun dawo daga umara cin husna yafi sosai zaman lafiyq ke guda atsakanin su...

     Bayan watanne uku tana zaune a daki sai nakuda da maryam ce takira sa'id sukayi asubuti nan da nan ta haife danta santalile mai kama da'ita...

    Murna gurin sa'id ba'acewa komai, haka akaci taron suna boy yace sunan baban husna wato hameed dr ammar ma yazo mata barka tare da matarsa da 'yayansa...

      Hmm husna dama kawu yace min *SAI NAYI NADAMA* sa'id ne yace dama *SON ZUCIYA* Yasa kika ki fahimata... husna ce tace bana mantawa da tsaftacecen *MARAICI NAH*Sa'id yace ai Dama in mutum bai bi duniyar a hankali ba yashiga  *KUNCIN RAYUWA* kuma komai *Nufin Allah ne* Sa'id yace gashi yanzu duk munzama *MATA NAH*..Maryam tace tabbas husna *k'e ta dabance*...

    A shekaru sun shuda zaman lafiya sukeyi husna takara haifar wane d'an inda aka saka masa sunan mahaifin sa'id wato lukman.. Sam sa'id yace matarsa bazatayi aiki ba yak'i amincewa hakan yasa mama taje dadi,  su baba jamila kuwa sun tuba sun nime yafeyar mutane...

      Yara duk sun tasa sa'id yana zaune sunata wasa da lukman da hameed husna sai dariya takeyi musu sunata abi abi...

     Sa'id ne yarada mata akunne nifa wane nakeso..

     " Nifa na kammala, miji mai kaunata sirika mai kamar uwa 'yaya masu tarbiya ga kishiya mai kamar yar uwa...

     " Kissing dinta yayi yace ku shirya zamu huce umara next week...

    Cikin murna tayi masa godiya ta shiga daki shima yabita tare da yaransu...

Kokari nakeyi naga nakarasa rubutun Amma ina sai naga littafi ya kare! Abunka da karamin littafi babu wuya ya cika, dubawa nayi ko akwai ragowar page ina wasu sababbin littafai na hanga ajiye littafin nayi tare da bibiyar labarin ina nazari kamar haka!!!!

   _Rayuwar duniya lallai hakuri take bukata abunda hakuri bai bakaba sai kaga rashin sa shima bai baka ba_

   _yanzu kake cikin gata da kudi sai kaga an jarrabe ka da babu.._

_Duk wanda yayi hakuri da kaddara mai kyau da mara kyau sai kuga yace riba agaba_

   _Idan abu yafi karfin ka fara nemon taimakon Allah, zakaci nasara_

  _Wanda kafi tsana sai kaga shi yake taimakon ka_

_kiyayya sai ta dawo soyayya, wanda baka tunanin yasoka sai kaga shi yake sonk'a_

    _Ba lallai wanda kafi so kake aura ba, shi aure da haihuwa da kutuwa nufi ne Na Allah_

  _har gage da ihu da kururuwa da cin mutunci bashi zai hana miji karo aure ba, koma ga Allah yar uwa kiyita Addu'a Allah ya baki mai tsoron Allah ma mashirika ba sai kiga komai yazo miki da sauki..._

Mutum ya tashi acikin Sulusin dare na karshe wato daga karfe uku kenan har zuwa hudowar alfijir.....

(Saboda lokaci ne mai albarka wanda Allah yake amsa addu'a sosai acikinsa)

Yayi nafilfili sannan ya
zauna yayi ma Annabi (saww) salati gwargwadon iko.

(Domin shi salati mabudi ne.).

Sannan ya karanta ayatul kursiyyi (domin ita ce ayah mafi girma acikin Alqur'ani).

Sannan ya karanta addu'ar nan ta Annabi Yunus (as) wacce Manzon Allah (saww) yace duk wanda ya
karanta Allah zai yaye damuwarsa, zai biya masa bukatarsa.
Addu'ar ita ce : "LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZALIMEEN".
Sannan mutum fadi bukatunsa sannan ya Qara yin salati ga Manzon Allah (saww).
In sha Allahu Za'a samu biyan bukatu da yayewar bakin ciki ko damuwa.

Domin wadannan hanyoyin ingantattu ne daga Manzon Allah (saw).......

   May Allah (SWT) shield us from trials, afflictions, poverty, evil thoughts & may HE grant us HIS Rahma at all times fi duniya wal akhira...

    Be yourself. People may or may not like you, but it’s important that you stay true to who you are..

Who are you to judge the life I live? I’m not perfect and I don't have to be! Before you start pointing fingers, make sure your hands are clean...

  ALHAMDULILLAHI ANAN NAKAWO KARSHEN LITTAFINA MAI SUNA  *A UBA NA DAUKE KA*
  

Time:-12:08
Date:-FRIDAY 26 MAY  2017
 
  *Ashirin da tara ga watan sha'aban 1438*

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATA GA MANZON RAHAMA (SAW)

   ABUNDA MU KAYI BA DAIDAI BA ALLAH YA YAFE MANA!

   WANDA MU KAYI DAIDAI ALLAH YABAMU LADA!

  KU DINGA DAUKAR ABUBUWA MASU AMFANI...

   RAMADAN KAREEM!!!

    *'YAN UWA GAFA WATAN LADA GA WATAN RAHAMA GA WATAN DA CEWA ZAMA BAI KAMAMU BA MU DAGE GURIN NEMAN RAHAMAR ALLAH A WANNAN WATAN MAI GIRMA KADA MUYI SAKACE DA IBADA HAKURI KYAUTATAWA BAYIN ALLAH SADAKA DAKUMA KARATUN ALKUR'ANI ALLAH UBANGIJI YASAMU CIKIN 'YAN TATTUN BAYINSA YA HADU MU DA DAREN LAILATUL KADRI YA YAFEMANA KURAKURAN MU..*

   _SAI MUN HADU ASABON LITTAFINA MAI SUNA_
  
     

        *SO*
              *GARWASHI NE*
    

  

    INSHAA Allah Nan ba da bayan sallah!

  Gaisuwa gareku mutanen kirki HASKE WRITER'S ASSOCIATION..Allah ya cigaba da daukaka mu...Allah ya karemu ya kuma kara hada k'anmu..

ﺍﻟﺸﻜﺮ ﻭﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﻟﻠﻨﺎﺱ
ﺑﺎﺭﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ
ﺃﻧﺎ ﺑﺎﻻﻣﺘﻨﺎﻥ ﻟﺬﻟﻚ ﻣﻦ ﺃﺟﻞ ﺣﺒﻚ

♡♡♡masoya na♡♡♡ Allah ya biya muku bukatun ku na alheri, Allah yatsareku daga sharrin mutum da aljan....ina Alfahari daku..

  TAKU HAR KULLUM!!!

     *NANA DISO (MUTAN MADINA)*
*Urs Nana diso*

Deejarh berver

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

No comments:

Post a Comment