[7/13, 6:13 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _24-27_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*
_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
K'ukan da najlat tak'eyi ne ya tsaya ita tarasa ma me zataci masa,Wane murmushi tayi wanda k'ana ganin sa k'asan tana cikin damuwa...
" Uncle jabeer ne yace Najlat bazan tursasa miki ba Amma inson ki jarrabani kiga ko ina sonki...
" Najlat ce tace ita soyayya ta kasance kamar kunama ce gata karama, bak'a tunanin zafin harbe ta sai ka taba ta...to haka soyayya tak'e duk k'an kantar ta, tana shiga zuciyar ka zaka fara jin radadi, ba zata rabu da k'aiba sai kayi jinya....
" Tabbas wanda ya shiga soyayya shi yasan kalaman nan, hakan ya tabbatar mun kin taba soyayya kuma ya nunamin yaudarar ki akayi...
" Kasan komai Na rayuwa yana bukatar shawara da tunani, to lokacin da nayi soyayya ta babu shawara kuma babu tunani...Na dauke ta kamar zuma zak'inta kawai nakeji daga lokacin dana sanar da me zumar sai kuma ya harbe ne da'ita...
" Najlat kisa aranki cewa zamuyi soyayya ta gaskiya kuma zan kula daki, rufun asiri ina dashi karkiyi tunanin ne ba mai kudi bani kuma ba jinin sarauta bani ba...
" Murmushin dole tayi,sai kuma ta tuna da kalmar yarima khaleel da ya taba gaya mata lokacin da tana karama ...cewa Mai samu shi aka fi kauna, Amma mai hikima da mai ilimi su suka fi amfani...
" Najlat k'aifin kalamanki kadai sun cancanta a soki a kuma kauna ci ki, nutsuwa da tunani su akafiso ajikin 'ya mace...
" Tashi tayi tana kokarin shiga d'aki tace a koda yaushe Namiji mai kudi yana gigita mace amma namiji mai ilimi yana burge ta kuma namiji mai gaskiya yafi dadin kallo, da zarar kuma yasa kamun kai sai kaga yazama sarki, dukiya bakuwa ce wanda batazo masa ba shine baisan ta ba, wanda tazo masa tuntuni yasan da tafiyarta, kamar yadda tsoron Allah ke kara imani,haka tausayin ma rashi ke sa mutane su soka, hannu mai bayarwa kullum shine asaman mai karba...
" Dariya yayi yace najlat komai naki irin na maman ki ne, kasamu mace wacce ta fahimce ka yafi kasamu macen da take sonka dan kudin ka...ki soni ko kadan ne kinji?
" Dak'inta ta shige Alwala tayi ta tada sallah...
Jaaa rak'inka jaaa rak'inka...Sarkin fablita sarki suleimanu yana tafi zuwa fadarsa...
" Fadawa ke fadin Allah yaja kwana, wasu Nafadin Allah yakara girma Har ya zauna akan kujerar sa..
" Waziri ne yace rankashi yadade yau kwana biyu yarima khaleel baizo fada ba....
" Sarki ne yace Kuma an tabbatar yana gari?
" Da zuma mugansa gurin uwar soro da sarauniya fatima...
" Waziri ne ya kara cewa kuma ana saran shine magajin ka...
Yarima adamu tare da mahaifiyar shi suna tafi zuwa fadar sarki..
" ciroma ne yace sarauniya fiddausi lafiya kikazo a wannan lokacin?
" Allah yakara maka lafiya Na zone nasanar da kai magajinka yarima adamu...
Duk 'yan fadar suka jiyo suna kallonta..
" yanaso Zai kara aure...
" Waziri ne yace kyan d'a ai yagaji ubansa aure ai sunna ce...
" Adamu 'yar gidan wa kakeso?
" Najlat nakeso Har nasanar da mai martaba...
"Jikin sarki ne yayi sanyi domin yafison yarima khaleel da najlat, to me yace maka?
" yace indai tana sona ko wata daya auren bazai kai ba...
"To zaku iya tafiya.." suna fita fadawa sukace gimbiya najlat ai ta yarima khaleel ce..
" Sarki dai baice uffan ba...
Wai menene kike ta kirana awaya eh fa'iza?
" Ke gimbiya kinacan hankalin ki a kwanci ana nan anata hada miki bala'I kala kala mai martaba ya badak'e...
" Bangani maganar ki ba? " Sarki salim yabawa yarima adamu ke cikin wata daya za'ayi bikin...
" Saboda me to? Kuka tasa toma wai yarima adamu da ko magana bamayi wannan mai aure sak'en wallahi banason sa gwara Na aure uncle jabeer...
" Ohh meki dai komai kinayi babu shawara yanzu magana kuma ta zaune kuma fushi yak'eyi dak'e kinje kinyi zamanki, su inna da sadiya sai dariya sukeyi miki yanzu haka ma auwal yace kina aure zaa sako ki....
" Batasan lokacin da tace wayoo Allah nah na shiga uku..
" Da gudu mumy ta shigo me yafaru najlat menene?
" mumy me isa aka tsanine me isa ba'a sona, kowa baya tausayi na za'ayi min auren dole...
" mumy ce tace indai nice kakarta babu wanda ya'isa yayi miki auren dole...
" Masarauta babu gaskiya mugunta da asiri kowa sai ya zama dan iska me nayi musu bakiji kalaman da suke jifana dashi ba....
" Kada ki damu najlat inshaa Allahu bazaki tabe ba kuma Allah zai tsarik'i...
" Mumy kinsan wanene adamu kuwa mace agurinsa kamar ruwa ce sai yaji ishi yake tunawa da'ita da zarar kuma ya kare sai ya sallameta ga shaye shaye aurensa 6 acikin shekara 3....
" karki damu ke dai kisa Allah alamarin ki komai zaizo da sauke...
" Najlat ce tafara tari mumy tanayi mata sannu aikuwa sai jini abu kamar wasa...
" Aguje mumy tafita jabeer zokaga kada ta mutu...
" inaaa uncle jabeer ma yana kwanci da a dak'insa idanu wansa sunyi jajir dasu batasan lokacin da ta daka masa tsawa ba aikuwa azaburi ya miki...
" Menene haka kuka da girman ka meke faruwa ne?
" Goge idon sa yayi yace ina najlat din?
" Aikuwa suna karasawa dak'i tana kwanci duk jini ya bata ta...
" innalilahi me zangani haka dak'in sa ya shiga ya dakko wasu allurai da karin ruwa cikin mintina yayi mata allurai tare da karin ruwa bacci ya kwashe ta..
" mumy ce ta gyara gurin shikuwa uncle jabeer zama yayi kusa da ita yarasa mekeyi masa dadi, kaddai saboda shi najlat ta shiga halinnan to in ba saboda shine? Ya zaiyi da soyayyar ta..
" Jabeer kaga wasu magungunan ta..." Ke yajawo mata wannan cutar?
" Wallahi tunani ne yarinya karama aci tanada hawan jini..
" mumy ai ciwon zuciya ne ba hawan jini ba...
" ciwon zuciya garin yaya?
" Mumy ku kula da najlat akwai abunda ke damunta wallahi..
Mumy ce ta bashi labarin komai dake faruwa...
" mumy kenan ai kinga wannan yanzu yake faruwa wannan ciwon Nata ya dade...
" To jabeer yarinyar ce da kafiya baka sanin cikinta bakuma ka sanin bakinta....
Wayarta ce tafara ringim jabeer ne ya dauka yace hello...
" yarima khaleel ne yace ina najlat?..
" Batanan ya kashe wayar...
Yarima khaleel ne ya shiga cikin dak'in gimbiya bilkisu shaye shayenta takeyi tayi Nak...
" Baisan lokacin da ya kifa mata mari ba, menene haka shayeshaye a gidana? Bilkisu dama haka kike?
" To sai me nayi shaye shayen sai mai aimu a masarautar mu giya kamar abinci ce sai kuma ta zubi akan gado...
" Dora hannun sa yayi aka yana salati yanzu yaya zaiyi ya gyarara..maganar sumayya ta wado masa ai yarima ka aure kamilar mace yafi ka aure mai sonka saboda wani abun...Mikewa yayi ya huce dak'in ummi sun dade suna hira sannan tace masa zata kwanta sai ya tafi...
Najlat tunda taji sauk'i ta rage hayaniya yau ta shirya zata koma gida mumy dakyar ta barta tatafi tana Bude mota taji uncle yana fadin So garwashe ne...
" Shiyasa nace dan Allah kayi hakuri da soyayyata kada ta konaka kada kuma ka shiga halin dana shiga abaya.....
" Shiru yayi yana kallon ta... har tabar harabar gidan..
Yarima khaleel yana kwance akan kujera tunanin kawai najlat da halin da take ciki domin mai martaba ya sanar dashi anbawa adamu, yayi zurfi cikin tunani sai kuwa bakin bilkisu yaji anasa...
"Meke damunka ne? Kwana biyu kullum tunani kakeyi...
" Sauri yayi yace tunda bakyason abunda banaso ta yaya bazan shiga damuwa ba?
" Uhm Amma ne banji ance babu kyau shan giya ba tunda dai iyayena ma suna sha...
" A uzubillahi ke kuwa kinje islamiyya?
" Mu agida ake koyamana ai har muka gama...
" No wonder cuz karatun gida dana makaranta da bambanci, bilkisu this is the time da zaki nutsu..u know i love you and i care for you! U better stop all this kind of things kidinga abu like i wise women both boka da addini understand?
" Yes my love! But menene illar giyar?
" I feel happy dakika tambayi ne, Allah ya hana shan giya babu kyau kuma tana lallata hanta...
" Shiyasa babar mumcy akace hantar ta ta rube kenan?
" tana shan giya ne?
" sosaima daga karshe sai mutuwa tayi, yanzu dai bazan kara shan giya ba inshaa Allahu kuma naji dadi da ka gyaramin cikin salama da kuma fahimta...
" Ai zagin mutum da tozarta shi cikin mutane ba gyara bani ba, komai kayi shi cikin salama shine d'a'a...
" Rungume shi tayi tace you're my sweet bae so much love for you...take this tafara kissing dinsa daganan salo ya chanja....
Lok'acin da Najlat ta'isa masarautar fablita jikinta duk ya mutu tana kashe motar ta hadu da wane jak'ade yanata wallahi sai na rama tunda ka wulakanta ne...
" Cikin hikima tace baba waya taba ka?
" Yarima bashida kirki 'yata marina yayi...
" To baba ai ai kai kagama ramawa tunda kace masa mara kirki ai afadawa mutum kalma mai dadi ma ai sadaka ce...
" kwarai kuwa gimbiya...Amma kuma na rantse da Allah Sai Na rama ai..
" Ai baba Abu mafi sauki wajen tunkude cuta shi ne ka manta da an cuce ka, kaga yawan rantsuwa babu kyau kwata kwata yanzu sai kaje ka yi azumi...
" To 'yata nagode Allah yayi miki Albarka...
" Sadiya ce tayi dariya tace ohhh mutane sai aikin riya wai dan ashe miki albarka kike abubuwan nan ko?
" Najlay ce tayi dariya tace Komai k'arancin sa-albarka yafi Allah wadai...
" Ohh miki dai yarima khaleel kuma ya zama haramiyar ki sai dai kiyi sorry kije ki aure yarima adamu wata daya k'infito...
" Har cikin zuciyar ta sai dataji babu dadi, Amma sai tace ai Duniya mai juyawa ce, Abin da yake naka ne a cikin ta lalle ne za ka same shi komai rashin karfinka,Abin da kuwa ba naka ba ne a cikinta, ba za ka same shi ba, komai karfinka....Ta shige cikin gida..
" Kafin ta shiga daki sarauniya hafsa tace fara zuwa gurin ubanki yana nemanki gantalalliya kin gama bin maza shine zaki dawo fasika kawai...
" inna kenan kinsan Ko kadan, k'an (Sa) baiyi kyau da linzami ba, kamar yadda kan Doki ya yi kyau da shi......
" jakadiya ce tace Allah yakara miki lafiya tabbas tagayamiki magana...
" Jakadiya me tace kinsan ne wannan karin maganar bana fahimtar su..
" Tana nufin ita batayi kama da karuwa ba Amma 'yayanki sune karuwan...
" Kutmar uba bari nabita gurin uban Nata, tsinanneyar...
" Najlat tana shiga fada mai martaba ya kifa mata mari ina kike zuwa ina kike zuwa???
" yarima Auwal ne yace Allah yakara maka lafiya ai bin maza takeyi...
" Yarima salim ne yace sai nasa akashi ki kowa ya huta kuma ki shirya watan gobe bikin ki...
" Wane dadi makiyan nata sukaji..
" Najlat kuwa cikin kuma tace indai auwalu ne zai gajika to kujerar sarauta tayi asara, mutumin dake ganin girman mutane shine ya cancanta abashi mulki ba kazamin mutum ba munafuki kuma makiri, Iyaye na kuyi hakuri nafadi irin kalaman nan da basu dace ba, wallahi indai wannan mutumin ne ya cancanta ace masa fiye da haka domin duk'kanin ku kunsan halinsa kujerar mulki mahaifinsa kukijin kunya da baku sanar da shi ba...
" Sarauniya hafsa ce tace to shaharar riyar karuwa agaban sarkin kike fadin haka ta kifa mata mari...
" sarki mai adalci ne 'kada soyayya tasa masarautar ka ta lallace..Babbar alamar girman kai ita ce ka raina mutane ko ka ki karbar gaskiya,"Mutakabbari ba ya shiga aljanna....ka yafeni ya mahaifina sannan ta fita bangaren su fa'iza ta shiga tana kuka fa'iza ce tace kiyi hakuri kawata kiyi hakuri danAllah kada ciwonki ya tashi....
" Gwarama ya tashi fa'iza na mutu kowa ya huta abu ya isheni nagaji sai kace nikadai ce 'yar sarkin?...
" Najlat Kada ki cuci wanda ya cuce ki. Sharri kare ne, ko ya yi nisa sai ya dawo ma mai-shi...wannan kalmar itace maganar da mahaifiyar ki tagayawa mahaifiyata lokacin da aka zane ta aka kalamata sharri tayi sata...yanzu datayi hakuri kinga ita tayi gaba...
" tohm Nagode kawata tagare zan tafi masarautar fablita gurin ummi domin ita daya zata iya gayawa sarki salim yaji Amma masarautar nan zugashi sukeyi...
" hakane kam kinyi hikima...
" Kada ki sanar da kowa tafiyata please...
Khalifa kullum tunanin najlat fa nakeyi nakasa mantata wallahi...
" yarima kenan tuntuni shiru nayi maka kawai amma kanason najlat fiye da kankama domin duk soyayyar da aka sak tausayi itace soyayya...
" Hmm bawani so wallahi...kai ina zuwa kaganta ta shiga bangaren ummi da gudu...
" Tana shiga ta rungume ummi tanata kuka...
" sarauniya maryama ce tace menene najlat me akayi miki...
" Kuka kawai takeyi...Yarima khaleel kuwa duk jikinsa yayi sanyi kamar ya rungumetq ya lallashita haka yakeji...
Sarki ya bada oda aduba ko'ina gimbiya najlat ta bata...
Kowa hankalin sa ya tashi a ma auwal da mahaifiyarsa sai fadin ai dama nagaya maka karuwanci takeyi to kagani da idonka auwal yace wane namiji ne yazo ya gudu daita ....
" sarki salim ne yace yaisa yaisa...
Ummi ce tace najlat mintin ki 20 kina kuka kinki ki gayamin abunda ke damunki ti dagani naji gurin sarki nadawo...
"Tana fita khaleel ya zauna a kan gadon zata kwanta kenan ya riko hannunta idonsa yayi ja yace meke damunki najlat...
" Muryar sa taji kamar asama ta jiyo tana kallonsa...
♡ *KOWA YAYI DA KYAU ZAI GA DAKYAU*♡
_KOMAI YAYI TSANANE YANA TARE DA SAUKI_
*(❤ina godiya masoya na❤....ina tare daku.. sak'on ku Na taddani... Addu'a ta gareku itace Allah ubangiji yasaka muku da alheri bukatun ku Allah ya biya muku na Alheri..ya tsareku sharrin duk halittu...taku ce Nana diso❤ ...onelurv)*
{Masu complain bana posting akan lokaci kuyi hakuri Dan Allah ina Dan uzuri ne innayi normal kullum zaku jini inshaa Allahu}..❤
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[7/17, 9:16 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _27-30_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*
_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Meke damunk'i Najlat? Tun dazu fa kike kuka karkisawa kank'i wane ciwon..
" Hannunta ta zare daga Nashi A hank'ali ta mik'i tsaye tana kokarin faduwa idanuwanta sunyi jajir...
" Cikin hanzari yarima khaleel ya rik'i hannun ta...
" Batasan lok'acin data fuzge hannun taba ta shiga cikin dak'i...
" Cikin sanyin jiki yarima khaleel yace wallahi Najlat dina ba haka tak'e ba tanason ya khaleel tana kuma jin maganar sa Amma yanzu ko kallona bakyason kiyi, Najlat karki manta Yana da kyau ka damu da damuwar dan uwan ka,Abin da ya fi wannan shi ne ka taimaka ma sa domin ya fita damuwa....
" Duk maganganun da yak'eyi a kunnen ta yakeyi Amma uffan batace ba, in banda radadin da tak'eji acikin kanta...
" Sarauniya maryama ce tashigo kai baka rarrasheta ba katsaya kana kallonta, wannan sarauta wacce irin sarauta ce indai bazakayi adalci ba kada Allah ya baka...
" ummi me kuma akayi?
" Tun dazu sarauniya fiddausi ke faman surutu a fadar sarki a lallai adamu zai gaji sarauta, wai ke wazai baka sarauta auren fari ma sai yanzu kayi yafika sanin rayuwa...
" Ummi k'i daina damuwa dasu komai Nufin Allah ne, In akaban sarauta Nagode in ba'abani ba ko ajikina, karki damu ummita 'danki ma bayason sarautar nan..
" Toh hak'a nakeson ji domin babu abunda yakai hakkin mutane kakula ka lura...
" Inshaa Allahu, ummi kije ki lallashi 'yar gidan tak'i...
" Ai dole tunda kai ka kasa, Najlat sai da lallabawa...
" Fita yarima khaleel yayi Najlat kuma tana zaune ak'an gado jikinta gaba daya ya dau zafi...
Haba Najlat da hankalin ki kiyita kuka? Ko angaya miki kuka yana maganin matsala?
" ummi dole Nayi kuka, kowa bayasona wai Mai martaba ne zai hadani aure da yarima adamu...sai ta saka kuka kuma kuma...
" karki karasa yarima lafiya ai bazai yihuba, ina.. ki kwantar da hankalin ki babu mai yimiki auren dole, wazai baki adamu kina yarinyar ki dake? To matar daya auro ko wata daya batayi ba ya saketa...
" Ummi please kiyiwa sarki magana ke daya zaiji maganar ki, Allah bantaba jin son yarima adamu araina ba...
" Ina tare dake Najlat sai wanda kikeso zaki aura makiya kuwa sai dai suji kunya ba dai kije ba...
" Yauwa ummi Nagode Allah yasa ya yarda..
" Ameen bari naje Nayi sallah..
♡♡♡♡
Gimbiya bilkisu ke faman jin wak'a sai rawar ta takeyi babu abunda ke damunta, alamun shigowa taje tana daga k'anta taga wata 'yar tsohowa ta kusa awa biyu a zaune sannan tace lafiya???
" Gimbiya nazo miki da labari ne?
" Labarin me kuma?
" wato ana nan Ana alguz akan ahana yarima khaleel mulki kuma babu wanda mulki ya dace dashi in bashi ba, kuma Naga bai damu da mulkin ba..
" Yanzu kina nufin mijin Nafisa keson zama sarki? Tayi wane murmushi ne kuma bazan zama sarauniya ba kenan?
" K'warai kuwa! Dan haka nace kutashi tsaye...
" Hahaha Karbe dubu 5 kyasiya goro duk halin da ake ciki kya sanar dani...
" godiya nakeyi sarauniyar fablita nan gaba...
" murmushi tayi sannan ta shiga dak'i wanka tace cikin gown pink ta daura dankwali yarima khaleel yana shigowa ta manna masa kiss, my dear banason koyarwar wannan da kakeyi, lecturing bai dace dakai ba sarauta ce ta dace dak'ai...
" Murmushi yayi yace to ilimin nawa ai sai yazama Na banza idan bana koyarwa, kuma sarauta ai wahala ce....
" Bakaso kazama shugaba kazama jarumi kamar iyayen mu? Rigarsa take kokarin ciremasa...
" My princess kenan, mubar maganar nan bari Nayi wanka tukunna...
" Shiru tayi tana takaicin yadda yarima khaleel yake Nuna rashin son mulkin sa...
" Yana fitowa daga toilet yace oya a shafamin mai...
" mikewa tayi sannan tace ai dole tunda aikina ne...
" Cikin wane salo take shafa masa mai hakan yasa jikinsa duk ya mutu..Duk kinsa jikina ya mutu kuma inason fita yanzu...
" Yanzu kuma ai lokacina ne takara kashe murya daga nan suka shiga wata duniyar....
♡♡♡♡
Sarauniya fatima ke zaune afadarta, cikin baccin rai ta kalle uwar soro tace wai yarinyar nan dole sai ta aure jinin sarauta ne???
" Wakenan ranke yadade?
" Wacece in banda Najlat yanzu kuma adamu ke santa..duk ya gigice saboda ita..
" Kuma mai martaba sarkin bingim ya bashi ita hakan ya nuna nan gaba zatafiku mukami domin zata zama matar sarkin fablita...
" ina ai bazaiyihu ba ina ina ina bazai yihuba bazata aure shi ba wulakanta shine abunda ya dace daita...
" Ranki shi dade meisa baza'ayi mata turon aljani ba ta haukace gaba dayanta...
" hahaha dadina dake kaifin baseera, daman ance jirawa da tsofaffi ba ta yaro bani..
" sai ki kawo kudi domin aji ayi aiki mai zafi..." kije ki dau jaka dubu a kau darmun da'ita..
" Jakadiya babu inda ta nufa sai dokar dajin banban ta shiga tasa ihu da ihu ta shiga ciki...
" bokan ne yace weee tur tur angaya min nasan dalilin zuwanki...yarinyar sarki itama sarauniya ce hahaha kuma sarki zata aura hahah...
" To boka tayaya za'a haukatar da'ita kowa ma ya tsaneta..
" Tana da addini bazamu iya da'ita ba kuma yanzu ma tana tare da mai Addini kitafi bazamuyi ba kitafi...
" Kome kakeso boka zan baka nidai a haukatar da yarinyar kawai...
" wata irin ihu yayi sannan yace murzuzu angama zakije kishiga dak'in nan sannan zanyi miki...
" boka dak'i kuma me za'ayi adak'in??
" Zanyi lalata dake ne tukunna ina bazakiyi ba kitafi kitafi kuma sai na haukata ke heeee heeee...
" Nayarda boka indai bukata ta zata biya... *( wa'iyazubillahi wannan shine babbar asara da tabewa da kazanta da Mata sukeyi Don kawai wata bukata ta duniya kije ki dakko kanjamau, hakan ba karamar shirka bace ba,babu wanda ya'isa yayi Maka abunda Allah baiyi maka ba wallahi, duk wanda ya dogara da Allah to ya'isar masa duniya da lahira, Allah yatsaremu da bin bokayi da 'yan tsubbu ya tsaremu da tozarta dan Adam, kawai dan rayuwar wane ta wulakanta? garin ka tozarta shi sai Allah ya daga darajar sa kaga kayi asara kai baka biya bukatar ka ba ga kuma fushin Allah da azabar sa..)* bayan ya gama lalatar daita sannan ya bata wane kulli...
" Ke zuba acikin abuncin ta daga ranar sai ku tsaya kusha kallo...
" Godiya muke boka gidiya muke...
Lok'acin data karasa ma sarautar tatarar da Najlat tafita daga fadar sarki suna fitowa sukayi karo..
" Subhnlhi ya hakori baba ban kula dake ba...
" Cikin gigicewa tajiyo tace babu komai najlat..
" Har tayi gaba najlat tace baba uwar soro ga maganin ki ya wade..
" Cikin hanzari ta karba najlat har tayi nisa uwar soro tace kitsaya nayi miki godiya Najlat..
" Najlat ce cikin sauri tace Idan ka taimaki wani saboda Allah kada ka jira ya yi maka godiya, Yardar Allah ta fi yardar mutane...
" To ai shikenan cike da tsoro tashiga fadar sarauniya fatima tabata labarin komai..
" Karki damu uwar soro wannan sirine tsakani na dake...
" Angama sarauniya ne zanyi ciki nayi wanka...
♡♡♡♡♡
Sarauniya fiddausi ce tace inbanda inason musgunawa sarauniya maryam da bazanso najlat tazama sarauniya ba...
" gimbiya Mero ce tace hajiya nifa ina mutukar son Najlat babu ruwanta wallahi duk inda gaskiya take sai ta fadeta...
" sarauniya fiddausi ce tace ku ku rufemin baki dama ke mero sai kace bani na haifi ki ba...
" Mero ce tace Ne kinga tafiyata, haka kurum nasa bak'in hali agabana nakeyin gaba komai fa Allah yakeyi...
" hassana da husaina ne sukace mum kyaleta dama ita sister tafison su yarima khaleel...
" Nafiso d'in kinga yanzu ma gidansa zan karasa...
♡♡♡♡♡
Sarauniya maryam tana zaune tana tauna kayan marmari Amal tashigo da gudu ummi dagaske gimbiya najlat tazo??
" Tana dak'inta ma da gudu ta shiga dak'in suk'a rungume juna sunata ihu amal ce tace yaushe rabon dana ganki??
" Nima haka gimbiya Amal kinga yadda kika dawo?
" humm ai dan uwana yayi rashi dubi yadda kikaye bulbul dubi halitta...
" Hegia kina nan da iskancin ki dama?
" Me za'afasa??? Kinganne kullum inafama da makaranta...
" Ai lokacine kamar yau zakiga kungama...
" ina samari kuma?
" ke kyale samarin nan duk 'yan yaudara ina rukayya??
" Rukayya tana makaranta wallahi kinsan Abbanta bayason tana yawo...
" Ai gwara..
" Amal ce tace ko dai gyarota za'ayi da ya khaleel...
" Ina ai yayanku yafi karfina ooo inada mijina dallah sunansa dr jabeer...
" Kai gimbiya please wallahi yarima nasonki...
" kinji banza aine bana sonsa ai,gwara ma yarima adamu..
" Amal ce tasa dariya kinji yar iska adamu ai ya farkaki...
" hahaha Banson iskanci tashi ki fita malama...
" Ai gaskiya nafada.." oho miki kinga matsa ummi na kirana...
" Amal ce tabiyota tana kin koma 'yar gidan ummi kenan?
" ya son ranki...
" K'inga Najlat kyaketa kaiwa gimbiya bilkisu kayan nan inji mai martaba naga baki taba shiga ba sai ku gaisa....
" Shiru tayi Na dan lok'aci sannan tace tohm kawo..Amal zata bita ummi tace kyaleta taje ita daya....
Cikin takaici Najlat ke tafiya domin ko sunan khaleel ballanta na matarsa bataso, har ta kai gate din shiga gidan taga yafito sanyi da malin malin yayi masifar kyau sajin nan ya kwanta murmushi ya sakar mata haka ya bayyana hakorin makansa sai walwali yakeyi...
" Watasan lokacin dataja wane tsake ba tayi gaba tana tafiya ta tarar da wata jakadiya cikin girmamawa tace sannu danAllah kebawa gimbiya kice inji sarauniya maryama daga sarki...
" To..
" Au a aike ki ki aiki wata ko? Gaba dayan ki kin canja wannan dabi'ar Najlat Dina bace ba....
" ko kallonsa batayi ba ballanta na ta tanka masa tana shiga palour ta zauna kusa da sarauniya maryama tace ummita Na dawo...
" Sannu yar albarka harkin ji...
" Amal ce tace karbe wayarki sai kiranki akeyi...
" Yarima khaleel ne yace ita karya bata dace da kowa ba..
" ummi ce tace dawa kake kaikuma?
" Wacce nake da'ita tasan kanta ai...
" Wayar najlat ce tafara ringing cikin kidan I love you i hate you..cikin lausassar muryarta ta dauka hello uncle?
" akafadar ummi tasa kanta dafatan kana cikin koshin lafiya, tayi kamar zata saka kuka tun jiya baka kirani ba...
" Amal ce ta washe baki tana kallon ikon Allah..." shikuwa Yarima bak'in ciki ne ya turnuki shi sai yaji wani iri...
" Uncle jabeer ne yace kina raina wallahi kinsam bana mantawa dake domin soyyarki kullum konani takeyi...
" Murmushi tayi tace kadaici abinci?
" dafatan ke kinci kuma kinsha maganin ki...
" Yanxu dai zansha maganin..
" haba najlat ki daina wasa da maganin ki ko bakyaso kisamu sauki?
" inaso, nagode da kulawarka kakular min da kanka banda kula mata please...
" Uncle jabeer ne yaji dadi yace yadda kikace haka za'ayi gimbiya inma kince kada na kallesu to sai nak'i....
" ga ummi ta kugaisa tasa mata wayar akunne...
" Lallai ma Amal ummi na daure miki gindi waya akafadar ta...
" Cikin bacin rai Yarima khaleel yace ai batada kamun kai Namiji takeyiwa wannan shashancin?
" Najlat ce tace kinga amal Ba kamar mutum uku a duniya: Na farko wanda ya so ka, sa'ar da kowa ya ki ka. Na biyu, wanda ya ba ka sa'ar da kowa ya hana ka. Na uku, wanda ya zo maka, sa'ar da kowa ya guje ka....
" Jikin yarima ne yayi sanyi sannan yace Allah shaidata ne sannan yafita...
... _Assalamu Alaikum ina godiya da sakon nin ku..da adduar ku ina kuma Adduar Allah yabiya muku bukatun ku Na alheri_ ta kuce NanaDiso...
*akwai hadisi da ke cewa:*
*Ni'imõmi guda biyu mutãne da yawa na tõzartar da su/wulãqantar da su/qin amfãnuwa da su: Lãfiya da kuma sãmun iko/dãmã*
Bukhary.
*Wato bãwa ya sani duniya gida ne na gina lãhira, amma shaid'an yayi alqawari sai ya rud'emu ta hanyar yawan burace-burace!!!*
*Gudun duniya na nufi yin aikin da Allah yake so da gujewa abin da baya so, don haka dai mu taqaita burinmu don duk abin da Allah yayi namu ne bãbu wanda ya isa ya tsaremu/hanãmu samunsa hakama akasin sa*....
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[7/18, 11:33 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _30-32_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*
_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Amal ce tace gaskiya bakya kyautawa gimbiya...
" ummi ce tace kudai kunfiye complain wallahi to ne nayi masarautar binjim Sai nadawo..
" To ummi agaidasu inji Amal..
" zasuji sannan tafita..
" Amal ce tace Nifa yanzu zan tafi inada girki agida...
" please ki kwana kinga ummi sai gobe zata dawo please..
" ke bazam kwana ba, haka kurin da mijina kuma kinsan shi bayacin abincin 'Yan aiki...
" Dariya Najlat tasaka tace kaji dan gayu mai mata...
" wasu ma suyi aure ai sunki.." najlat ce tace Ai lok'aci ne...
Khalifa wai me najlat take daukar kanta ne? Ko kallona batayi fa...
" khalifa ne yasaka dariya yace to kai me ruwanka da kallon ka, ka dameni da zancen najlat, tun abaya sai danace kabita a hankali, yanzu gashinan sonta zai k'onaka...
" please kaje kabata hakuri sonakeyi mudawo kamar da...
" kana nufin Auranta kakeso kayi?
" Aure kuma? Nifa ba sonta nakeyi ba...
" Kai dadina da kai musu ai sai kayi tayi wallahi babu inda zanje..
" haba khaleefa abota batace haka ba...
" kanka akeji kaga tafiyata...
♡♡♡♡
Yarima adamu yana zaune yana tunani daya daga cikin fadawa yazo yace sannu mai jiran gado Nazo maka da labari...
" Cikin gadara yace me yafaru?
" Gimbiya Najlat tana nan agidan nan kusan kwana5 kenan.....
" A zabure ya tashi yace Amma baa sanar dani ba?
" kayimun afuwa sai yau Na sani..
" Dak'insa ya shiga ya chanja kaya yafesa turaruka straight bangaran ummi ya Nufa Najlat na zaune a kan kujerar varanda...
" Yarima adamu ne yace sarauniya ta ashe kina gida? Ni banma saniba ayimun afuwa...
" kallonsa tayi wane takaici ya turnikita tace eh ina gidan lafiya..
" haba Najlat bakisan irin soyayyar danake yimiki ba?..
" gutun tsaki taja tace banda kauna sona kawai kake?.
" wallahi najlat ina sonki ina kaunarki zan kuma rikeki amana....
" Nafarko dai inaso kaje ayimaka karatu kasan darajar mata! Nabiyu kuma inaso kasan illar shayeshaye...
" Alokacin yarima ya shigo ashe najlat ta ganshi...
" yarima adamu ne yace indai nasan wayannan zaki soni...
" Kwarai kuwa cikin bakin cikin dan yarima khaleel yaji tace yarima adamu ai namiji ne da kowacce mace zatace tana so, ka kalli shigarka mashaa Allah kafayimun kyau...
" Wane dadi yaji yace godiya Nakeyi sarauniyar nan gaba...
" Dariya tasaka tace zaka iya tafiya yanzu...
" An gama ranke yadade...
" har yayi gaba tace auuu anjima da night ina bukatar ice cream...
" To Angama..
" ita kanta haushin kanta takeji yadda takeyi masa Amma dan ta kuntatawa yarima khaleel tayi haka..
" yariman ne yazo ya zauna kusa da ita meke damunki najlat...
" cikin masifa tace wai me ruwanka dani ne? Sai na soshi mai ruwanka? Please ka kyaleni nayi rayuwata kada kasani cikin wane halin...
" Yi hakuri gimbiya kokadan banida niyyar takura miki wallahi, kuma wayakoya miki soyayyar...
" Daga kanta tayi tana kallon sa batasan lokacin da hawaye ya wanke fuskarta ba...
" Nasan amsarki itace yarima khaleel ne ya yaudari ne ko? Ki tsaya ki nutsu najlat inasonki ina kuma kaunar ki....
A hanzarci tatashi tace dakata dakata bana sonka bana kaunarka natsaneka yarima na tsaneka tasa kuka ta shiga cikin gida....
" Idanuwansa ne sukayi jajir Nan da nan ya miki ya bar gidan..
Tana shiga cikin dak'i tace kaine zabina bazan taba mantawa dakai ba, zaka kasance azuciyata koda yaushe, Amma kuma lokaci yakuri bazamu taba zama tare ba...
" Anty sumayya ce tashigo menene haka najlat sai surutu kikeyi ke kadai?
" cikin hanzari ta goge hawayen ta babu komai babu komai...
" To Allah yasa ashe kinzo ko kishigo gidana...
" Ai ina tafi sai gashi Allah ya kawoki yanzu Amal tafita ma...
" Toh ya makaranta??
" kafin takarasa sukaji sallamar Gimbiya bilkisu cikin faraa ta shigo tace aa yayarmu kice agidan...
" Nice gimbiya yanzu ai nazo...
" Ayyah ashe kuma ummi batanan, daman nafitone mu gaisa waccan kuma wacece ko gaisuwa?
" cikin hanzari Najlat ta kalleta hakan ya tabbatar mata itace matar yarima khaleel ita dai ba baqa baciba kuma tanada tsayi sai dai kuma batada kiba..
" Anty summaya ce tace Najlat kenan 'yar sarkin binjim ce..
" Ayyah Ko itace kanwar tamu da yarima na yake bamu labari??
" cikin faraa tace eh itace, Najlat ga gimbiya baku gaisa ba...
" Cikin gadara tace sannufa sannan tayi waje directly cikin gidan sarauniya fatima ta nufa...
" Wata dariyar mugunta sarauniya fatima tayi lallaima yau nazama 'yar gata matar sarkin fablita da kanta...
" Najlat ce tasaka dariya Kai hajiya ina yazama sarkin?
" Aikam adamu yakusa zama sarki kinga kuwa zaki dace da mulki...
" whatever bashi yakawoni ba, zuwa nayi mugaisa...
" aikam nagode k'inci abinci ne??
" Yanzu naga 'yan aiki suna kaiwa fada..
" Aikam bari nazubo miki farfesu akayi da macroni sai lemoka da kayan marmari...
" murmushi najlat tasaka tace gaskiya hajiya naji dadi sosai, kamar kinsan ina sha'awa...
" Sarauniya fatima ce tayi dariya tashiga kitchen da kanta ta zuba mata ta barbad'a mata magani aciki ta jujjuya....
" Hajiya da k'inkirani ai nazuba...
" Babu komai najlat ai kema 'yatace...
" cikin zumudi najlat ta karbe plate ko bismillah batayi ba tafara ci... *(gareku 'yan uwa wannan babban asarace aci muna mantawa dayin bismillah kafin muci abu, kuma yakamata muna taka tsantsan gurin cin abincin mutane domin yau tayi wuya idan kai zuciya daya kake zaune da mutum sai kaga shi bayason ka baya kaunarka, burinsa kawai yaga ka wulakanta, kuma komai san mu da abu muna kula da wanda zamu ci da kuma Na wanda za karba, Allah yatsare mu daga sharrin dukkanin halitta)*
" Aa najlat harkin cinye ne?
" Ai abincin yayi dadi bari nakoma cikin fada nagode ada nayi tunanin bakyasona sai yanzu naga kina sona... *('YAN Uwa mu sani soyayyar mutane ba soyayya baci ba, soyayyar ubangijin mu itace gaba idan Allah ya soka tofa kowa zaiso ka, kai dai ka zauna da mutane lafiya karka cucesu dasu soka da kar su soka duk daya ne kai dai kasa Allah Aranka domin kuwa wata soyayyar duk munafurci ce kokuma ba dan Allah ake makaba dan wane abun ne..kusa Allah a lamurukan ka sai kaga ka daukaka..)*
" Ah haba gimbiya, najlat nafita tasaka dariya yau kwanan ki yakare yanzu aka fara wasan mulki dai bazaki hau ba...
" wane irin yanayi najlat ta shiga kafin ta karasa cikin fadar tana shiga ta zauna anty sumayya tace ina kikaje...
" cikin gyatsene tace ku kunfiya tambaya wallahi..
" Najlat kenan, kinga anyi sallah bari nayi Alwala....
" To sai kiyi tayi mana waya hanaki, tasaka earpiece akunnen ta tasaka waka tanataji har gurin karfi hudu, sumayya ce tace najlat ko azahar bakiyi bafa...
" Kyaleni please sai magriba zan hada..
" wannan dabi'ar bataki baciba wallahi wasa da sallah ai baya cikin halinki...
" Banza tayi nata tacigaba dajin wakarta..
♡♡♡♡
Lok'acin da sarauniya maryama tashiga cikin masarautar akallah fadawa 7 ke binta har takusa karasawa cikin fada daga bisani taga auwal yanata kifawa bayi mari...
" sannu da zuwa sarauniya kingansu nan bayi ne 'yan iska marasa mutunci dan iskanci aikinsu nayi nabasu minti daya shine sukayi minti biyu...
" Shine kake dukansu haka haba auwalu haka kaga mahaifinka yanayi?
" dole a hukunta su domin bazan hau mulki anayimun abunda banaso ba..
" yanzu ka tambayesu abunda yasa suka dade?
" Ai basu isa na tambayi su ba su suwaye ina yarima mai jiran mulki...
" Babu shakkah abunda nake ji yau nagane wannan ai zalunci ne, yaushe zaka nutsune yaushe zakayi hankali? Wulakanta dan Adam babu kyau bakasan matsayinsu gurin Allah ba kuma kaima baka huce kazama kamar su ba...
" Allah ya kiyaye nazama kamar zu wannan sai dai danki khaleel yaja tsaki wasu fadawa suka bishi abaya...
" Allah ya wadaran mugun halinka da zalunci abunsoni da kuwa mahaifin ka baisamu mulki ba...
" cikin masifa ta shiga masaurautar da kanshi sarki ya miki ya nufi ta..A hankali tace dakata kukuma ta nuna fadawa bakomai ake bari akuya tagani ba zaku iya fita...
" cikin girmama sarki salim yace wanene yatabamin kanwata...
" sarauniya maryama ce tace Duniya fa mai karewa ce, ita gaskiya kamar daddawa take inkaso kacita inkaso ka kyaleta amma fa kamshin ta sai ka shaka, kana ina fadarka ta lallace abunda auwalu yakeyi akasar nan...
" Auwalu yazama abunda yazama kuma ina iya kokarina mahaifiyar sa ke dauri masa gindi...
" Ai indai uwa bata gyara danta ba to duniya ta gyaramasa kuma indai auwalu da baisan mutuncin manya ba baisan kimarsu ba baisan darajar su ba shine zai hau mulki to kujerar mulki tayi asara gwara adauki jaki yayi mulkin...
" tabbas hakane to amm..
" Karka biye ta mace akoda yaushe mahaifiyar muntana gayamana Abu daya ne kyakkyawa wanda ko makaho yana iya ganin sa,Shi ne kyawon hali,Ka zama mai kyawon hali ba sai ka fadi ba mutane da kansu za su yabe ka...
" Wannan haka yake shiyasa nasanar najlat itama zanyi mata aure.....
" Najlat 'yar kace mahaifiyar ta ta mutu ya kamata kajata ajiki kana ina najlat ta hadu da ciwon zuciya?
" ciwon zuciya kuma garin yaya?
" Kowa ya dakko shirgen sa sai yadora akan najlat dan ka tsaneta, wand ya cancanta zaka bawa yaranka bama ita daya ba dan haka maganar adamu ta ruguje...
" cikin nuna rashin jindadi da tausayin yartasa yace to tana zuwa asubuti ganin likita...
" Tana zuwa sosai shiyasa nasanar dakai ka kula kasan maganar da zaka dauka kakuma gyara fadarka...
" inshaa Allahu nadau gyaranki yaushe zata dawo?
" sai nan da watanne tukunna..
" To nagode da kulawarki...
" Nima nagode da sauraron da kayi..
" Mujema da yawa sannan tayo hanyar gida...
♡♡♡♡
Tun daga ranar najlat ta shiga cikin wane yanayi ita kanta ummi ta kula da wasu abubuwa datakeyi wanda ba halinta bani ba...
" yarima khaleel ne ya shigo yace ummi yajikin najlat din?
" Anya ba haukaciwa tayi ba khaleel sannan ta fashe da kuka ko asubuti zamu tafi...
" ummi anya ba iya shigenta bani ba?
" najlat bata wasa da sallah bata yawo babu dankwali yanzu fa sai kulleta nayi acikin daki zabura fa takeyi tace sai tafita...
" Subhnllahi, bari naje nafito da mota sai mu tafi...
" ina driver kasa ya kaimu..
Sirri kamar dafi yake Yana da kyau ka san inda za ka boye asirinka!...Bana son kowa yasani shiyasa...
To bari naje na dakko hijjabi aikuwa najlat data balle kofa sai gudu tadinga zagaye gidan sarauta tana surutai, sarauniya fiddausi ce tafara ganinta nan tasa aka sanar najlat ta haukaci ta haukaci sai dariya akeyi...
" Najlat tayi hanyar fada kenan yarima khaleel yarikota yasata amota...
" Sarauniya fatima da uwar soro sai murna sukeyi dan sarauniya har da rawa...
" Sarki suleiman kuwa hankalinsa duk ya tashi..
" ita kuwa sarauniya fiddausi tasa adamu agaba kaje asubutin katabbatar kaga yadda ta haukaci kaga yadda tazama wallahi bazaka auromin sirika mahaukaciya ba...
" Aikuwa directly asubutin ya nufa yana shiga yaga nurse sun rirrikita dariya yasaks yace wa zai aure mahaukaciya haha aikam bani aurenta yasaka dariya, najanyi zancen aurenmu kije kisamu irin ki kiaura...
" ummi ce tasaka kuka tace adamu wacce irin zuciya kake da'ita tana cikin wannan halin?
" adamu ne yace kaje ummi ai gaskiya nafada wa zaai aure haukaciya sannan yayi fitarsa...
" Yarima khaleel kuwa malaminsa yayi waya yasanar dashi yace yana binjim sai dai in yadawo..
" lokacin da mumy ta iso cikin kuka tace wannan sharrin gidan sarauta ne Dangina basu taba hauka ba, wannan jifanta akayi....
" Dariyar hauka najlat tasaki tace su jifa manya hahah jifa ke aka jifa....har sai da likitoci sukazo sukayi mata allurar bacci...
Yarima khaleel ne yace 'Yan uwan Annabi Yusuf sun yi niyyar kashe shi, Allah bai kashe shi ba,Sun so su kaskanta shi, Allah ya daukaka shi. Su ka batar da shi don mahaifinsu ya manta da shi, ya daina son sa, amma sai Allah ya kara masa son sa. Aka sayar da shi a matsayin bawa amma ya zama Sarki,Kada ka damu da sharrin dan AdamnAllah gatan Bawa...
Hakane yarima Allah yabata lafiya tasa kuka..
*********
*....Wanda ya fi kowa wahala a duniya shi ne mai bakin ciki a kan ni'imar da Allah ya yi ma wani bawansa*....
_Kusane cewa Babban mabudin alheri shi ne Istigfari. Idan ka yawaita shi matsalolinka za su kau, damuwarka za ta gushe, sauki daga ubangiji zai zo maka_....
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[7/21, 11:33 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _32-37_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*
_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Duk fad'in masarautar fablita ko ina ya dauk'a Cewa gimbiya Najlat ta haukace..wasu Na dariya wasu kuwa Na jajen abun, mafi akasari ma suna cewa ai asiri akayi mata..
" Sarauniya fiddausi ce tace ina fata kaje kaci mata mutunci, wazai bawa mahaukaciya 'Yarsa? Sam bazaiyihu ba mahaukaciya??
" Ki kwantar da hank'alin ki cewar yarima adamu Ni kaina ba don Allah nakeson ta ba, hahaha k'insan halina da zarar ta kwana biyu zan sallama mata...
" Dariya ta kwashe dashi haka mukeson ji ai, tsinanniyar yarinya gwara kada ta warke ai...
Sarauniya fatima ke faman dariya irin tasu ta sarakai cikin gadara tace Mai ja dani sai ya shirya kwanan nan ma zamu aika yarima khaleel din...
" uwar soro tace kinga aikin boka yaci ko? Bukata ta biya sai kikawo wane abun akara kaimasa..
" wannan Ai dole ne...
♡♡♡♡
Sarauniya hafsa ce tayi hanyar masarautar binjim cikin fada takarasa cike da girmama wa tace Allah yaja ran sarki inada babban labari...
" ciroma ne yace wanne irin labari kike dashi...
" labari ne mai cike da takaici da bakin ciki Acikin masarautar ka anyi gamo da mahaukaciya....
" waziri ne yace wannan kwana kwana ce kiyi maganar ki yadda zaa fahimta...
" Najlat ce ta haukace tana can masarautar fablita tanata iskokai, yakamata a dakkota akaita gidan mahauka ta...
" yarima auwalu ne ya kyalkyala dariya cikin muryar mai ban dariya yace hauka shine daidai da'Ita..
" Ba fade ne yace kai yarima ka'iya bakin ka agaban sarki kake...
" Yarima auwalu ne yace a gafarce ne....
" sarki salim yana sauraron duk abunda suke cewa cikin isa yace ita cuta bata wuce kan kowa ba, in bazakayi adduar sauki ba to kama bakin ka...
" waziri ne yace gaskiyar sarki, duk inda gimbiya take Allah yana tare da'ita wannan abun da akayi mata ba sharrin komai bani ba sharrin sarauta ce...
" Sarki ne ya radawa ba fade maganar...
" Malam inusa da ciroma su suka dauke hanyar masarautar fablita...
♡♡♡♡
Mumy ce tace Duk wanda yayiwa Najlat wannan abun kada Allah yabashi kwanciyar hankali...
" Ummi ce tace yarinya babu ruwanta tsakanin ta dakowa mutunci, irin munafurci munafurcin nan na mata wallahi bata iya shiba, kwanaki har kuka nayi mata babu samarin babu mai kiranta ga wannan larurar...
" mumy ce tace ai sara da sassaka basa hana gamji turo...
" ummi ce tace tabbas jakaran da Allah ya nufa da cara ko ana shawo ko ana muzuru sai yayi...
" Yarima khaleel dake faman kallon fuskar najlat yarinya yar fara ga hanci ga gashi mashaa Allah, bakin nan yayi sirit ya bushe, tunani kawai yakeyi yanzu wa zai aureta shikenan an bata mata suna...
" mumy ce tace yakamat ka koma gida ga dare yanayi yarima...
" Tohm mumy Allah yabata lafiya ne natafi sai da safe....
" fitar sa ke da wuya ko bene bai hauba aikuwa najlat ta miki ta ciccire Alluran da karin ruwa, su mumy sukayi kanta suna irrikita amma ina duk ta fusge musu tayi hanyar bine, yarima Na jiyowa yaga sunyi bai san lokacin da ya cafkota ba nurse duk sunyo kanta da Allurai cikin tsawa yace karku yimata wata allura awa shida kenan Ana abu daya???
" Daki sukayi da'ita najlat sai muzurai taketayi cikin zafin nama ta kara yun kurawa zata fita ya cafkoya...sai zare masa ido takeyi...
"Nurse ce tace kaine mijinta??
" sai Alokacin ya kalle najlat yadda ta kwanta ajikin shi tanata nishi...
" mumy ce tace aa ai bata da aure...
" Ayya ranki ya dade Amma dai tana sonsa shima yana sonta dubi yadda yake damuwa akan lamarinta....
" Mumy ce tace ai yayanta ne shiyasa..
" Au Allah sarki to kubari ayi mata allurar domin asamu sauki...
" Yarima ne yace wai ke bakya gajiya da tsikara allura?
" ummi ce tayi murmushi tace kabari ayimata yarima...
" Dauke kansa yayi ai kuwa sai ta tsikara mata cikin muntina ta sulale sai bacci....
Dr abbas ne ya shigo yace sannunku?? Ya bawa khaleel hannu suka gaisa..
" wato awanmu 5 muna bincike akan kwakwalwar ta amma babu abunda muka gani hakkan ya bayyana mana lafiyar ta kalou, Matsalar zuciyar tane kuma shima tana samun sauki amma binciken mu ba muga komai ba...
" mumy ce tace Ni 'yasu to yanzu likita yaya zamuyi???
" Hajiya duk fad'in kunne bai rufe ido, duk tsananin ciwon ai akwai maganin sa, Yadda na fahimta kukoma da ita gida agwada Na islamic ko zaa dace...
" Tohm mungode likita...
" Yarima ne yace duk wanda yayiwa najlat wannan abun wallahi...
" Ummi ce tace dakata khaleel Kada katasar ma abokan gabar ka, sai kaga za ka iya musu...
" Likita ne yace kwarai kuwa domin yanzu babu abunda ake bukata sai lafiyar ta ga wannan itace takardar sallamar taku...
" Daga nan akayo gida da'ita masarauta shiru babu kowa sai yan aiki dake zagaye suna shiga dakin ummi suka kwantar da'ita bayan sunyi sallah yan jajjera musu abinci sai ga sarki suleimanu shi kadai ya shigo...
" Yaya jikin nata??
" ummi ce tace jikinta babu sauki shikenan sun cuci yarinya...
" Matsawa yayi kusa da najlat ya gyara mata gashin ta cikin iya magana yace sauki na Allah ne kuma shi zai bata.. kuma Maryama Ba kowace faduwa ce matsala ba,Da yawa wanda zai fadi amma idan ya tashi ya sheka ba ka iya cim masa...
" Hakane kuma yanzu zan kwanta...
" sarki suleimanu ne yace Amma ina bukatar ki...
" To wa zai kula da najlat din??
" kakarta ai tanan zuwa anjima kya dawo...
" cikin girmama wa tace tohm shikenan..
Fadawan dake biye da yarima khaleel ne suka bisa..cikin mutunci yace ya kamata kuma ku huta yanzu kusan 11 amma bana tunanin kunci Abinci...
" Wannan aikin mu ne kuma biyan mu akeyi....
" Komai yanason kyautatawa ne wallahi inbanda dole babu abunda zaisa kutake mun baya please kutafi na hutashi ku...
" Yana shiga cikin dakunan sa duk baiga bilkisu ba, yana bude wane daki ya tarar tanata kuka cikin kidemewa ya shiga meke damunki me yafaru my love...
" Banza tayi masa tace gaba da kuka..
" Janta yayi ya rungumeta yana bata hakuri cikin kissa tace awa goma yau ban saka a idona ba ko kirana bakaiba...
" Kiyimin hakuri gimbiyata wallahi banajin dadi ne kuma munji asubuti tare da ummi...
" Amma dai hakkina ne ka sanar dani ko?
" kwarai kuwa my love kikwantar da hankalin ki mijinki Na tare da ke ako ina kike kuma ina sonki...
" Dan Allah kayimun alkawari bazaka taba yimun kishiya ba indai kana sona...
" Kirjinsa ne ya buga dufduf...
" ya kayi shiru??
" My love i can't take this promise yayi min tsauri da yawa ina sonki but kishiya bansani ba ko zan kara....
" juyawa tayi zata fita nan da nan ya rikota ta fada jikinsa daga nan salo ya canja...
Misalin karfe uku yarima yana kwance shi dai yarasa abunda yake damunsa kuma duk lokacin da ya kwanta mafarkin najlat yakeyi duk zazzabe ajikinsa, kallon gimbiya bilkisu yayi yadda take baccin ta cikin kwanciyar hankali yadda take nuna masa soyayya hakan yakan burgesa, wayarsa ce tafara ringing mamakin kiran yayi cikin sallama ya dauka...
" Malam idress ne yace yarima yanzu mai martaba sarki suleiman ya kirani yayi min bayanin yarinyar da batada lafiya yanzu katashi kaje kasaka mata suratul bakara kokuma ka karanta mata, kasamu ruwa akofi ya tofa mata falaki da nasi katabbatar tasha kakuma shafi mata jikinta...
" Mikewa yayi ya nufi bangaren ummi stright dak'in da najlat take ya nufa, mumy tana kwance akusa da'ita,zama yayi ya bude kur ani cikin murya mai dadi yafara karanta suratul bakara mumy ce ta tashi zaune yadda taga yana karatun tace muna godiya khaleel Allah yasaka da Alheri yadda k'akeson najlat baa magana...
" Sai da yakarasa karatun sannan ya tofa falaki da nasi yace duk yadda zaayi ta bata tasha...
" Tohm zan kokarta sannan yayi hanyar gidansa...
Da sassafe jakadiya ta shigo Nan ta zauna kusa da Najlat tana sannu 'yar Nan wanga abu baiyi kyau ba...
" Mumy ce tace komai yayi farko zaiyi karshe..
" To muje ma da yawa ni nayi gaba...
" Yarima khaleel ne ya shigo sanyi da wata hadaddiyar alkyabba Amma kayi kyau yarima sai kace sarki...
" Tsigunnawa yayi yace ina kwanan ku kuntashi lafiya???
" lafiya lou kaga najlat ko magana batayi sai dai tayi ta kallon mutane...
" malam yazo shida ciroma yanzu zasu shigo sai kusa mata hijjabi...
" Malam idress ne ya shigo yace wata ta zauna kusa da'ita..kuma tun yaushe abun yafara??
" ummi ce tace kusan sati daya kenan abu sai gaba yakeyi anrasa dalili...
" Watsa mata man zaitun yayi sannan yafara karatun ayoyin ruqya wata kara tayi sannan tace wai menene kabi kadami mu da karatu???
" Karatun ya ciga dayi har sai da sukace kadaina kona mu mugu azzalumi mai ruwanka da ita ko yar uwar kace???
" au zaluntar ku ma nakeyi kenan? Bakusan wannan abun da kukeyi babu kyau ba??
" Kai kasan babu kyau mu agurin mu da kyau tunda an bamu jini kafin mukayi alkawarin haukatar da ita...
" Karatu yaciga dayi har sai da suka fara zamu fada maka komai kadaina konamu kaciremun kafa cikina duk ya fashi...
" waya turo ku? Ku musulmai ne?
" mu arna ne anturo mu mushiga jikinta don mu haukata ta daga bisani kuma mu batar daita...
" Wanene ya turo ku?
" bazamu fadi sunanta ba kuma mun riga munyi mata ajiye acikin mahaifa..
" cikin ladabi malam idress yacigaba da karatu sai ihu sukiyi, to kugayamin dalilin dayasa aka turoku...
" Zamu fadamaka amma kadaina karatun wata mata ce bataso tazama matar sarki nan gaba kuma dama yawanci duk antsane ta, Amma kadaina konamu zamu fita...
" Mu addinin mu ya hanamu zalinci kuma babu kyau zalinci, yanzu kucere ajiyar da kukayi mata...
" mun cire kuma zamu tafi bazamu dawo ba dalilin dayasa ma muka fara samun nasarar shiga jikinta taci abinci mai dauke da asiri kuma babu bismillah, daga nan mukafara sata wasa da sallah sai jin kide kide, Amma kuma akwai masu karatu kusa daita shiyasa duk lokacin da suka fara mukan yunkurata ta miki..
" Karatu yadinga yimusu har sai da suka kone sannan yace najlat...
" Cikin sanyin murya tace Naam..
" Ina ne kemiki ciwo?
" cikina ne kadai yake yimin ciwo...
" yabata zaitun yaci tasha daga nan yafarayi mata fada game da sallah azkar da kuma zama da Alwala...
" bayan angama komai akayiwa Malam godiya sannan akayi masa alheri...
" mikewa najlat tayi tana kallon yadda yarima ke kallonta can kuma taga mumy tana sallah tace mumy me kikazo yi?
" bakyajin dadi ne shiyasa nazo dubaki...
" ummi rannan ne nashiga bangaren yama yama sai kuma ta rikice..
" ummi ce tace bangaren wa kika shiga?
" Namanta ummi nasan dai anbani abinci naci daga nan kaina yafara ciwo...
" To kina kula dai kinji, Allah yatsare gaba...
Wanka tace sannan ta nufi bangaren mai martaba cikin faraa yace sannu najlat yajiki?
" Jiki naji sauki fa, yarima adamu ne yace mahaukaciya ashe kinsamu sauki...
" Har cikin kanta sai dataje zancen ba shiri ta bar fadar sarki ne yace duk wanda yakara kiranta mahaukaciya to sai yakwana gidan yari...
Tana zaune tana karatun kur'ani sallamar yarima khaleel taje zama yayi kusa da'ita yace ya jikin naki?
" Batare da ta kallesa tace da sauki..
" ko kina bukatar wane abunne?
" a'a, " Najlat wannan fushin dakikeyi dani yayi yawa yanzu zamu tafi yaki banda tabbacin zan dawo...
" Cikin hanzari tace yaki kuma..
" Kwarai zamu tafi yaki Allah yasan wanda zai dawo da rai acikin mu dan haka nake niman yafiyar ki...
" idonta ne ya ciko da kwallah tace banu komai ai yahuce...
" Cikin murna yace to zamu koma kamar da??
" Dan Allah kakyaleni yarima kaje kayi rayuwar ka kabarni kada kasa zuciyata ta fashe....
" Najlat Amma ya kamata...
" Ya'Isa please kabar dak'ina...
Khalifa inason Na aure Najlat domin na tausaya mata halin datake ciki???
" kacemin dai kana sonta...
" nifa bana sonta inason dai Na taimaka mata yadda ake mata bori a cikin masarauta...
" To basai ta yadda ba...
" Kaifa kafiya mugun baki...
UMMI ke zaune taba tana lazumi cikin girmama yarima yazo ya gaidata ashe mumy tatafi...
" Tun jiyama tatafi inson inyi magana da kai khaleel...
" Tohm ummi inajinki..
" Ni mahaifiyar kace bazan Nema maka abunda zau cutar dakai ba inaso ka nemi auren Najlat...
" Baisan lokacin da cikinsa ya kada ba domin abubuwa biyu ya tuno gimbiya bilkisu batason kishiya da kuma lokacin da Najlat tace Ya aureta yace baison ta...
" Ko baka sonta ne???
" ummi Akwai Matsala najlat bata sona!!!
" Kai zaka koya mata yadda zata soka domin Na fuskanci kuna tausayin juna nan ku...
" Yarima khaleel ne yace tausayin nema zaisa na aureta...
" Amma naji dadin goyan bayan dakayi min ubangiji Allah yayi muku Albarka ya tabbatar muku da Alheri...
" Amen ummi, sannan ya fita kansa gaba daya ya kulle ta yaya zai tunkari najlat da zancen ballantana ma bilkisun sa...
" Najlat tana zaune tana tauna tufa kamar daga sama yarima khaleel yace Najlat insonki kuma zan aureki...
" Batasan lokacin datayi waje da tufar data fara taunawa ba, Aure? Aure?? Ni zaka aura baka isa ba bana sonka baka isa ba sai tayi dak'in ummi...
WANE HALI NAJLAT ZATA SHIGA?? ZATA AMINCI DA YARIMA KHALEEL KOKUMA UNCLE JABER..
" WANE YANAYI YARIMA KHALEEL ZAI SHIGA...
" GIMBIYA BILKISU ZATA AMINCI DA KISHIYA???
" DA GASKE YARIMA KHALEEL YANA SON GIMBIYA NAJLAT...
*GODIYA DA FATAN ALKHAIRI GAREKU MASOYANA💜 ADDU'ARKU TANA RISKATA ALLAH YABIYA BUKATU NA ALKHAIRI...#TEAM SGN..#ONELOVE..#TAKU CE NANA DISO...*
_ya zo a hadisi cewa: Bãbu wata rãna da bãyi zãsu wãyi gari a cikinta; fãce sai Malã'iku biyu sun sauko -daga sama- d'aya daga cikinsu yana cewa: " Ya Ubangiji ka mayarwa wanda ke ciyarwa abin da ya ciyar" d'ayan kuma yana cewa: " Ya Ubangiji ka sanyãwa mai 'bõyewa/riqewa asãra/tafiyar da dukiyar_
Bukhary & Muslim
*Wato ana son bãwa ya dinga yawan kyautatãwa 'yan uwa musulmi, don haka ya janyõ masa wani alherin, kuma kyautatãwa ga 'yan uwa na jini lãda biyu gare ta, kada mu d'auki ra'ayin cewa sai munyi kud'i sannan zãmu taimaka! Don ice tun yana d'anye ake tanqwarã shi !!!*
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[7/24, 3:26 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _37-40_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*
_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Lok'acin da najlat tashiga dak'in ummi da gudu tana kuka..
" lafiya najlat me a kayi mata? Nifa banason cin mutunci shima tsokanar ki yakeyi??
" Najlat ce tayi wane tunani duk yadda uwar wani take son ka, tafi son nata d'an..
" Ummi babu abunda nayi mata fa, Allah ki tambayi ta daga...
" Najlat ce ta katse sa Ummi kishiga tsakani na da yarima Yadamine,Kuma...
" Ba sai k'in karasa ba kikwantar da hankalin ki, khaleel baruwanka da najlat nagaya maka...
" To ummi Amm..
" kawai k'a amsamin da toh kafita...
" Toh ummi bazan sake ba kiyi hakuri gimbiya...
" wane kallo tayi masa da sai da ya murmusa mata..
" yana fita ya dafi kansa ya'ilahi yaya zanyi da Najlat da bilkisu zaman su bazai taba zuwa daya ba domin kowacce da irin nata halin, inason najlat Amma Nafison gimbiyata uwargidata sannan ya murmusa....
Ke kuma komai kidinga kuka sai ya rainaki...
" zunburo baki tayi tace toh ai ba saurayi na bani ba da zai raina ni naji haushi....
" Shiru ummi tayi batace k'ala ba...
Ummi zanje fada yanzu zandawo...
Tohm sai k'in dawo..!!!
♡♡♡♡♡♡
Sarauniya hafsa ke zauni tana tauna inibi sadiya ta kallah tace saura wata Nawa bikin naki??
" Sadiya ce tace bikin mu dai nida waccan ballagazar yarinyar ai saura sati1...
" Hahaha ai in baki labari anfasa bikin yace bazai aure mahaukaciya ba, yafasa hahaha daman nifa Nafison tashiga duniya...
" toh yanzu tana ina ne?
" Tana can masarautar fablita tana yawon duniyar ta....
" Ayyah yanzu babu mai sonta sai dai talakawan kauye dan sune daidai da ita...
" Ina zuwa bari naje ta zuga mai martaba...
Sarauniya hafsa matar sarkin binjim tana shigowa zuwa fadar sarki salim ayi hattara...
Allah yakara maka lafiya inason muyi magana...
" Nan ya daga hannu kowa yafita zama tayi tace mai martaba yakamata ahada bikin sadiya da najlat kada duniya suce ana nuna mata bambanci....
" kinyi magana mai kyau Amma kuma ai batada tsayaye najlat...
" To kayi shila agari mana ko da mai kwasar ta tunda kowa yak'ita...
" zaki iya tafiya zanyi tunani akai..
" Tana tafi tana murmushin takaici har ta karasa cikin gidanta Nan ta hadu da Auwalu yayi shayeshaye ya koshi sai tumbile yakeyi.. aikin banza kiba a kunne, kai dai baka taba janjawa...
" idan nazama sarki sai nafi haka tambili...
Tsaki tayi ta bashi wuri..
♡♡♡♡
Yayin da najlat taisa cikin fadar sarki Suleiman cikin girmamawa ta gaidashi Nan yasamata albarka tare dayi mata tambaya babu abunda ke damunki yanzu ko?
" Eh babu abunda ke damuna inaso Na koma gida yau shine nazo Na sanar dakai...
" Tom zansa amaidake zuwa bayan laasar Sai ki shirya...
" Tohm Nagode Allah yakara girma..
" Yarima adamu ke faman sauri domin ya isa fada ayayin da yaga najlat tafito sai ya canja tafiyar tashi ta koma bangaren ta sai da ta tsaya domin su gaisa da jakadiya sai gashi agabanta...
" Mahaukaciya ashe kin warke yanzu sai soyayyar mu ta dora...
" Cikin zafin rai tace kasan mahaukata basu dace da mai hankali ba dan haka zaka iya neman wacce ba mahaukaciya ba sai kuyi soyayya...
" Najlat karki manta indai Ne nayi nasara ayaki tofa ne zan zama sarki...
" Dariya tayi tace sarauta?? Bakasan nema na gajeta ba?? Ta bangare har biyu???
" Amma zaifi kyau ki amince min domin ina sonki...
Najlata ce tace Ba kowace magana ce ake ba da amsar ta ba,Ko shiru magana ce... sannan tatafi..
Shikuma ya dafi k'ansa sannan yayi cikin gida...
Wallahi baka isa ba wallahi baka isa ba yadda kakeji da mulki haka nakeji dashi masarauta mu tafi taku komai da komai baka isa kayimin kishiya ba wallahi kayi kadan...
" Haba gimbiya bilkisu kitsaya ki saurari ne mana...
" Na saurari me cin amana ko zalunci kokuma tozartane kakeso kayi...
" yarima khaleel ne yace Iyakar dan Adam ya yi kokari bisa sha'anin duniyarsa, amma ba tilas ne duk sha'aninsa ya zo masa yadda yake so ba, dakata gimbiya ne mijinki ne kuma inada damar auran sama da daya...
" Aikin banza aikin wofi ai kasan baa hada gudu da susar duwawu, bazan zauna da kowacce macce ba sai dai mu rabu....
" baisan lokacin da ya kifa mata mari ba which kind of nonsences is this ko angaya miki raayin kainane?? Ko ance miki sonta nake? Ki bude kunnen ki kiji zan aureta ne dan na tausaya mata dan kuma umar nin iyayena amma kina kiso....
" Kaga khaleel riki kalmar son ka bana so ko me kakeso kaje kayi kanka kayiwa nikuma bani zama da Amarya dan haka kazaba ko ni ko ita...
" Kansa ne gaba daya ya kulle direct dakinsa ya nufa wata irin zufa yakeyi yarasa abunda ke damunsa gashi gobe zasu fita yaki....
Najlat Na zaune tana hada wasu kaya ummi ta shigo tace Najlat kije ana jiranki awaje...
" rungume ummi tayi tace i so much love you my ummi you're so much to me, zanyi missing dinki...
" nima haka najlat ki kula ki kiyaye kizauna da kowa lafiya, Allah kima zai baki miji nagari, kuma kisani Kada ki yi farin ciki da samun al'amrin da ba zai wuce ki ba Kada ka yi bakin cikin wucewar al'amarin da, tun fil'azal ba za ka same shi ba....
" tohm ummi nagode, sannan tayo waje tana fita yarima adamu ya sha gabanta please najlat ki saurari ne...
" Ka girmama kanka don mutane su girmama ka. Idan kai ka wulakanta kanka faufu, babu mai girmama ka...sannan tayi gaba tana isa taga yarima khaleel a cikin motar bude gidan baya tayi ta shiga cikin masifa yace Ko angaya miki ne driver dinki ne? Indai baki dawo gidan gaba ba to babu inda zan kaiki...
" Ta kusa minti 5 sannan tafito tashiga tunda suka fara magana babu wanda yayiwa wane magana..
Wayarsa ce tafara ringing cikin masifa gimbiya bilkisu ke magana...
" speaker yasa yace haba my gimbiya nace ki kwantar da hankalin ki please wannan auren da zanyi badan inasonta zanyi ba dan na taimaka mata ne, ko 'Yan aiki sai sunfi ta daraja .....
" katse wayar tayi batare da tace komai ba...
" najlat ce tace cikin masifa kowacce asarariyar ce zata aureka ai da sai kaje can ku cinye kanku kai da matar taka...
" Dariya yasaka yace kwana nawa ne maye yayi Amarya zai cinye ta?
" Suna isa masarautar najlat tace a dade anayi....wataran gaskiya zata bayyana....
Cikin gida ta isa tana ganin faiza ta rungumeta i miss you abokiya...
" kawas kinkara kyau ya jikin naki?
" Jikina ai yadade da samun sauki kinsan lafiyar Allah ke bayarwa...
Tabbas kuwa...
Bari Nashiga ciki tana isa sadiya tace au ashe zakizo bikin nawa???
" najlat ce tace me zai hana bikin yaya guda...
" Sarauniya hafsa tace sai kace gaske bakin ciki ya cika miki zuciya shine zakiyi mana karuwanci...
" Abun ai Na Allah ne bana mutum ba tashige daki...
Gaisawa sukeyi da sarki salim nan ya sanar da sarkin cewa yana son najlat kuma yanaso ahada bikin da sadiya...
" kai amma naji dadi sosai da sosai inshaa Allahu daman kayan dakin tare nayi musu komai...
" Amma mai martaba inaso please kada asanar da angon anjima zaa kawo kudin sarana nan da kwana uku zaa kawo lefe...
" Babu matsala Allah ya taimaka..
" Najlat tayo fada kenan shikuma ya nufi gurin faiza...
" Aa yarima ashe kai ka kawota?
" Dole na kawo gimbiyata Ai, ki bakisan ankai kudi ba???
" Wai da kai da najlat???
" eh mana kinsan tana fushi dani please and please ki tayani bata hakuri ga dubu dari kibata kinji....
" Toh Allah ubangiji ya tabbatar muku da Alheri...
" Ameen sai anjima...
" Najlat tana isa fada bayan sun gaisa da sarki yace ki rubuto min duk wane abunda kike bukata na Amarya...
" Mai martaba wazai kara aure???
" Kece zakiyi aure...
" Cikin wane yanayi tafara zare ido daganan tafara tare sai jini kafin ta miki ta wadi kasa...
" ku dakko mot...
Barakallahu fiykum💜 ina godiya da addu'inku Allah yasaka muku da alheri..
*Wato ana son yawaita sulhu tsakãnin mutãne, don shaid'an yana burin yaga ya 'bãta tsakãnin Musulmai, wanda hakan ke haifar da gãbã mai wahalar sha'ani, don haka duk mai son lãda to ya yi qõqarin sulhu tsakãnin mutãne, sannan Malamai sunce a madadin mutum ya yi qarya gwanda ace ya yi (Tauriya) ya fad'i magana mai ma'anõni da yawa..*
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[7/25, 11:17 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _40-43_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*
_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Sarki salim da k'anshi yasa Najlat a mota Nan waziri ya nufi asubuti dasu, Suna isa nurse sukayi dak'in duba lafiya da'ita, likitoci uku ne Akanta suna duba lafiyar ta....
" waziri Ne ya kalli sarki suleiman yace in banyi kuskure ba, da anbar maganar auren Najlat yanzu...
" Sarki salim ne yace Duk masifar da ta samu dan Adam yana jin ciwon ta,Amma ya fi jin ciwon dariyar da abokan gaba suke yi masa...
" Wannan haka yake ranka yadade Allah ya bawa gimbiya lafiya...
" Dr hassan ne yafito cikin girmama wa ya gaida sarki, Allah yakara maka lafiya da kabarta agida sai Nazo...
" A'a inason ayi mata check up sosai ne ....
" To duk da haka jikin gimbiya da sauki kuma tana shan magani akan lokacin hakan zai taimaka gurin warkar da ciwon Nata...
" Waziri ne yace likita yanzu wane hali take ciki?
" Ta warware dama damuwa ce tasata cikin matsala nayi mata allura ga wasu magungunan sai kujera minti 30 sai kutafi da'ita...
" Sarki ne ya shiga dak'in datake kwance tarar da'ita yayi hawaye Na wanke mata ido..cikin sanyi murya sarki salim yace najlat Nasan ban kyauta ba nazabar miki miji ba tare da niman sanin ki ba Amma kisani ne mahaifin ki ne bazan taba zabar miki abunda zai cuceki ba....
" Rike hannun sarki tace mai martaba bai wai ina damuwa da zabin ka bani? Abunda Nake damuwa dashi wane irin namiji ne???
" Najlat acikin zuria ta kin bambanta kin kasance yarinya mai hankali mijin da Nazabar miki Nasan yanada addini duk tsiya bazai wulakanta ki ba, Najlat banaso naganki cikin damuwa tuntuni nayi kuskure yanzu inaso nagyara kuskurena gurin faranta miki...
" Share hawayenta tayi tace zanmaka biyayya ya mahaifina Nasan bazaka zaban abunda zai cutar dani...
" Karki damu najlat kodaina damuwa ina tare dake...
" Murmushi tayi daganan sukayi gida suna shiga akafara sanarwa sarki ya dawo Najlat bata tsaya ko'ina ba sai gurin su fa'iza...
Fa'iza ce tace congrats kawas Allah yabaku zaman lafiya..
" Cikin mamaki najlat ta jiyo yaushe kikasan maganar nan?
" Ai nasan cikin hukuncin Allah sai haka ya faru gashi wannan kudin inji angon ki...
" cikin mamaki najlat tace are serious? Wane angon nawa kuma ke if not mai martaba yayimin magana kowane mijin zan zauna ne dashi a matsayin *KADDARA TA*
" Any way yakamata ki iya mouth dinki kinaganin yadda makiya sukayi miki caaa aka....
" Kinsan Allah kawas yadda Natsene Yarima khaleel haka Natsane mijin da zan Aura! So zanje kawai Nayi biyayya....
" Mamaki ne yakama fa'Iza tabbas najlat don't know wanda zata aura, should ai tell her???
" Kinga bari Natafi Na lurah bakya bakin ciki da Abunda Nake bakin ciki da shi...
" Ba haka bani ba kawata sai yanzu Na dabbatar *SO GARWASHE NE* Allah kadai kisawa baya daga karshe ya cire mai....
" you won't believe me when i said i hate love, i really hate love sorry, am not interested in any relationship i just want my life cool ans simple at this age i don't like any tension, so zan zauna agidan mijina ne has kaddara...
" yakamata kiyi tunani najlat kada fushi ya rufe miki ido ita rayuwa babu inda bata sauyawa yanzu wane zaisoka anjima ya kika..Nasan all this hate akan soyayyar ki da yarima ne, wannan ne time din daya kamata ki yafemasa last time when he said baya sonki he mean baida interest din aure ki so stop judging...
" Stop it fa'iza.. I don't have that time da zan tsaya sauraron maganar sa so bye...
" Oh ne faiza mutum da bai iya fushi ba in aka bata masa yafi kowa...Allah ya daidaita ku...
♡♡♡♡
Mum kinji abunda yake cewa wai Aure when mukayi aure bana tunanin anyi 2years, ina 'yar sarki..
" Malama yimun shiru before Nafasa miki baki ta waya, sai kace ba 'yata ba mata nawa mahaifinki ya auro still ina gidan ina kissar ki ko a cikin tamu ma sarautar kinfi kowa daukaka yanzu zaki fara taki rayuwar kigama da yarima khaleel kuma kina tunanin za'abawa mijinki sarauta bayan kinsan you're the only wife...
" mumy tawa my momcy advice tayi Nagode sai Nazo...
" That's my daughter much love..
♡♡♡♡
Sarauniya fiddausi ce tace wai adamu yana ganka kayi shiru ina mazan takar taka???
" yarima adamu ne yace ke yafimin idan nayi miki wane abun duk jikina babu dadi Anjima zamu tafi yaki....
" Adamu kai zakayi nasara nabawa bokayi kudi ayi maka aiki kai zakayi nasara daga Nan yafita gurin matarsa ya nufa Nafisa Nafisa...
" Allah yajaran mijina sarkin fablita...
" Wai me isa kuke nuna son zuciya akan sarauta ne, bani ne wanda ya dace da sarauta ba yarima khaleel ne...
" Allah ya kiyaye kai ne magajin masarauta nice kuma matarka...
" Bani mintuna zan dan huta...
Yarima khaleel ne ya shiga yace cikin dak'in Gimbiya bilkisu tashi tayi ta rungume shi inasonka ina sonka mijina you're my happiness...
" sumbatar ta yayi I’m not perfect, I’ll annoy you, make fun of you, say stupid things, but you’ll never find someone who loves you as much as I do, kiyimin addua Allah yasa nayi nasara...
" U are always in my heart i can't stop praying for you..
" fita yayi straight yayi mota...
" Dariyar mugunta tayi ne gimbiya bilkisu yanzu muka fara...
♡♡♡♡
Najlat tana zaune tana karatun Alkur'ani acikin barandar cikin gidan bayan ta gama tafara danna waya kamar daga sama taje anyi sallama...
" Amsawa tayi batare da ta daga kanta ba...
" Amincin Allah ya tabbata agareki matata...
" A zabure tajiyo tana kallonsa matarka kuma ta ina na zama matarka?
" I don’t understand how can I care so much when you don’t care at all...yarima yace najlat kinsan ankawo kudin mu...
" she raise her head high,Dakata dakata dama kaine mijin Kuka tasaka tace Natsaneka bana sonka..
" He just feel bad, bakomai najlat say what ever you want am with you..kuma inaso in sanar daki zan tafi yak'i kiyimin addua Allah ya bamu nasara...
" Tsaki tayi tace Nasara??? Do i look like i care???Bana fata dawo tare da kai...Allah yasa kada kayi Nasarar...Anyar fita tayi..
" Rikota yayi.. in this one month, in every passing moment i felt you near to my to my heart,I felt you every moment around me,your eyes make me strong and at the same time weak, and today i didn't what to become weak in front of you,the pain you gave to me today was in my eyes..kuma bana son in nunamiki, i didn't ask you to love me but expect you to gave me respect..but respect of being your husband...
" Tureshi tayi tace that's your own problem rubish tafita..
Sarauniya hafsace tace eyyah najlat ashe ansamu mai kwasa Allah yasa ki dade agidansa...
" Sadiya ce tace uhm dadin abun dai ne dubu dari da Hamsin aka kawomin...
" Sarauniya hafsa tace ai daman kudi kadan sunfi Albarka ke kuwa karya ce zata kasheki...
" Najlat dai uffan batace ba sai sanarwa datakeji sai bayan yaki za'a yi bikin anjima zaa daura musu aure...
♡♡♡♡♡
murna gurin ummi baa cewa komai cikin faraa tace Amal an daura auren yayanku...
" Tsalle Amal tayi tace kar dai da gimbiya??
" eh da'ita... " kai dadi nayi murna kinga sai yaji da gwazonsa??
" Murmushi yayi yanada kayan yaki irin wannan murna Amal?
" Ai bakaga murna ba ai sai tashigo masarauta...
" Tsugunnawa yayi yace kisaka min Albarka ummita zanyi nisa Allah kadai yasan ko zan dawo...
" Allah ya baka Nasara dana Allah yadawo daku lafiya...
" Nan Sarki suleiman yayi sallama da mutane yarima adamu kuma ya dafa kafadar Khaleel yace Nasan kai ne sarkin wannan masarauta dan Allah ka kula da 'yayana..
" Haba adamu wannan wacce irin magana kakeyi???
" inaji ajikina balallai in dawo ba...
Bayan kwana hudu ko'ina an shirya dawowar sarki suleiman da rundunarsa cikin tashin hankali Akazo masarautar fablita aka sanar cewa sarki suleiman ya mutu da daya da cikin yarima...
Sarauniya bilkisu dake kuka Kamar ranta zai mutu tace shikenan yarimana na shiga uku
" Kai bak'aso kaga yadda ake kuka ake kururuwa ba ummi da sarauniya hafsa da fatima duk sun fito idanun su dauke da hawaye sunata tambaya wanne yariman? ....
Najlat Na zaune tana cin tufa faiza ta shigo da gudu tace sarkin fablita ya mutu...
" Najlat ce tafara kuka tana innalillahi wainna illahir rajiun...
" Fa'iza ce takara cewa wane daga cikin yarima ya mutu...
" Shiru najlat tayi tare da murmushi..
" Najlat murmushi kike fa?...
" Sai kuma wane sabon hawayen ya wanke mata fuskarta tace Allah yayi musu rahama...
WANENE YA MUTU YARIMA KHALEEL KO YARIMA ADAMU?
YAYA MASARAUTA ZATA KASANCE?
" YA GIMBIYA NAJLAT ZATAYI IDAN TAJI YARIMA KHALEEL NE...
" WANE IRIN TUGGU SARAUNIYA HAFSA ZATAYI YAYIN DATAJE YARIMA KE SON NAJLAT???
SHIN SOYAYYA TAKAN ZAMA KIYAYYA KOKUMA KARYA NE???
Mashaa Allah...
_I read all your comments Wanda ke sani cikin farin ciki your love for this book is very important and precious to me.._
*Ina godiya ga makaranta da duk masu son littafina ga kuma masu like and comment akan littafina...*
_I request you to please avoid all the grammatical and spelling errors_
*Ina son jin opinion dinku akan wannan shafin...*
_Rayuwar Masarauta zata fara yanzu kukasance da Ne.._
*Allah yasaka muku da alheri yabiya bukatu...Amen*
_Please do vote and comment your comment and vote give more courage to continue writing my story..And your comments help me to write better...#TEAM ...SGN ....#SGN LOVERS..taku ce Nana diso..👌🏻_
( *Wato ana son bãwa ya kasance mai tausayi ga kowa da kowa, don in mun bibiyi tarihin Manzon Allah SAW zamu sãmu cewa tausayinsa ya mãmaye kõ'ina har dabbobi, don haka abin da ya kamata mu dinga tausayãwa na qasa damu don muma Allah ya tausayã mana, sannan kuma mu girmama na sama da mu ta hanyar yi musu biyayya matuqar basu nemi da mu sã'bãwa Allah ba...*)
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[7/28, 10:11 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _43-46_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*
_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Sarauniya fiddausi ce tafita tana ihu kugayamin ko adamu ne ya mutu tana kuka hakan yakara tayar da hankalin ummi cikin tausayi tace ki kwantar da hankalinki....
" Cikin kururuwa tace Narasa miji Narasa adamu heheheee heee takara fashewa da kuka....
" Yarima khaleel ne aka shigo dashi gaba daya jikinsa jini sai nishi yakeyi haka ya tabbatar wa da kowa adamu ne ya mutu, cikin magagin azaba khaleel ke kiran ummi ummi zuwa tayi ta rungumeshi tana sannu khaleel, Nan ta bada umarni atafi dashi gidan sa kuma a kirawo masu maganin gargajiya...
" Gimbiya bilkisu ce ta rungumeshi tana kuka sannu yarima sannu yanzu da kai ka mutu yaya zanyi wane hali zan shiga, ina sonka mijina ina mutukar kaunar ka please kada katafi ka barni...
" Hannun sa dake dauke da duk jini ya shafa gefen fuskarta yace Am with you my gimbiya, yanzu adamu ya mutu shi da mai martaba...
" kadaina damun kanka yarima Kwanan su ne ya kari...
" Murmushi yayi sannan ya rufe idanun sa cike da radadin da yakeji ya tuna da maganganun gimbiya da take cewa ka mutu acan ka mutu acan..baisan lokacin da baccin wahala ya kwashe sa ba....
Masarautar fablita ta cika da mutane da sarakai da gamnoni dukkanin su sunzo ta'aziyar sarki suleiman, shikuwa yarima khaleel yana kwanci ta dalilin jikinsa da bai gama warkewa ba...
" sarauniya fiddausi kuwa bak'in ciki da bala'i tasaka a gabanta, gaisuwar ma da kyar take amsawa, Hankalin ta bai tashi ba sai da aka gaya mata cewa saura kwana uku a nada sarki tare da yin bikinsa....
" jakadiya ce tace hajiya yakamata ki daina kuka d'a Na kowa ne kuma yarima khaleel zaiji maganarki kuma zai girmama ki...
" Dakata dakata indai jinin sarauniya maryama ne zaiyi mulki bazan taba sonsa ba bazan taba kaunar sa ma, inaso kije kiyi masa mugun asirin da zai haukaci....
" Jakadiya da tsoron Allah yagame jikinta sai cewa tayi to sannan ta fito daga dak'in...
" Bata dira ko'ina ba sai gidan sarauniya maryama Nan tatarar da gimbiya sumayya da farouk dake zaune suna jajanta mutuwar mai martba cikin ladabi ta gaishe su sannan tace Allah yaja ranki nazo da labari ne...
" Farouk ne yace ku har yanzu baku daina munafurci ba???
" sumayya ce tace kayi shiru ka kyaleta tafada mana...
" To dai hausa sunce gyara kayanka bazai zamo sauke mu raba ba, yarima khaleel yana cikin hatsari domin Yanzu sarauniya fiddausi tace aje gidan boka domin a haukatar dashi kada ya samu sarautar nan dan haka kema ki tashi tsayi....
" Sarauniya maryama ce tace Hmm hukuncin Allah ai bana mutum ba kuma idan Yazama sarki ai amfanin kowane bamu kadaiba...
Tabbas hakane mu jima lafiya ne natafi..
" Farouk ne yace ummi yaushe zaa fara bikin Sarkin namu...
" Ina tunanin gobene har tarewar ta...
" Ohhh Allah yayi najlat da Yarima...
" Farouk ne yace nima datana da kanwa ita zan aura...
Sarauniya Fatima ce tayi dariya tace yarima khaleel yanzu zanfara mulkin karya zan nuna nafi kowa sonka zan yaudarika da kalamai zan kuma nuna maka soyayyar karya dan nasamu matsayi a mulkin ka sannan ta shiga cikin dak'insa tare da sallama cikin gigicewa ta zauna kusa dashi kayi hakuri ranka yadade tun dazu banzo na duba lafiyar jikin ka ba...
" Riki hannun ta yayi yace ina sonki hajiya ina kaunar ki kina nuna kulawa Akaina ina kuma tare da ke...
" Cikin kissa tace kada kadamu sarkin mu yaushe ne wacece Amaryar tamu...
" kafin yayi magana tashigo tace mai martaba yanzu zaa nadaka matsayin ka, Sunata jiranka...
" Cikin tsaki yace banason sarautar nan Amma wasiyyin da mahaifina yayimin yazama dole Na karba...
" Sarauniya fatima ce tace Sau da yawa kakkan ki wani abu, amma ya same ka. Samuwarsa kuwa ta zama alheri ce gare ka,Sau da yawa kakan so samuwar wani abu, amma ka rasa shi,Kuma rashin nasa ya zama shi ne alheri gare ka, Ka tashi katafi kai ka dace da wannan sarautar...
" Murmushi yayi yace ina godiya hajiyata sannan yafita zuwa fada...
" sarauniya fatima ce tayi murmushin kissa tace ina fatan kinsan gobe wata sarauniyar zata shigo??
" Sani na da rashin sanina bai dameki ba!.. shishige cikin Abunda babu ruwanki? So what? Idan nasani? Please kikama girman ki and this king mijinmu ne not you so please maintain...
" mtseww Ni ta hannun daman khaleel ce kuma zan nunamiki sunana na asali fatuwa zakisan makircina....
" Gimbiya bilkisu ce taja tsaki sannan ta huce fada...
Manyan matan dake tattare a fada sunkai su dare Bayan 'yan gari tare da Na fada Nan aka yimasa nadin sarautar sai kabbara sukeyi aka saka masa crown sannan aka saka masa riga sannan ya zauna akan kujerar mulki, Cikin girmama wa yace Ni sarki khaleel nayi alkawarin Amana da yin mulki tsakani na da Allah mutanen fablita ina tare daku...
" Nan Akasa Allahu akbar Allah yaja kwanan ka sarkin fablita sarki khaleel...
" Tasowa yayi yazo ya gaida ummi hajiya da fatuwa sannan ya matsa gurin manya daga nan ya huce gurin matarsa...
♡♡♡♡♡
Najlat dake zaune cikin laffaya Nan su mumy suka shiryata cikin alkyabba sannan aka hada Mata kayanta...
Sarauniya hafsa kuwa tana cikin rikici tunda taji cewa sarki khaleel zata aura, daga ita Har 'ya'yan sai mugun fata sukeyiwa najlat...
" Mumy ce tare da kaninta sukace Najlat kinutsu domin munga kanki narawa gidan dazaki shiga gidane mai tsada Mata dayawa suna fatan samun gidan Amma babu dama ki iya kissa zama da mutane kuma kiso mijinki ki zauna dashi lafiya..
" Yamutsa fuskarta tayi sannan tashiga dakin sarauniya hafsatu Nan tace Allah yarabaki da mijinki...
" Najlat ce ta dago kanta da sauri...
" Kalleni dakyau Allah yasa adaran yau ya sakeki...
" Ko bakiyi addua ba kobaki ce Komai ba natsane sarki khaleel bana sonsa Kuma kijerayi dawowata...
" Yauwa 'yar duniya gwara kikashe auren..
" Cikin bakin ciki tashiga dakin sarki salim fada yafara yimata da saida tayi kuka yace najlat kinzama matar sarki kuma nasan auren nan bakyason sa inaso kiyimin biyayya kizauna da mijinki lafiya...Najlat duk yadda kika kai da tsanar sarki khaleel in ba kaddara ba kada ki rabu dashi, zanbaki bayi guda10 zan hadaki da jakadiya daya sunanta ruma...
" Rungumesa tayi tana baba zanyi maka biyayya sun kusan minti biyu sannan aka saka amota sai masarautar fablita...
Tun kafin su karasu ko'ina sarki yasa an kawatasa komai nafada ansaki na zamani queen bilkisu bakaramin kyau tayi ba cikin Alkyabbar ta dukkanin su suna jiran zuwan amarya...
" Mota 30 akayi ta 'yan kawo najlat tun daga hanya ake sanarwa queen najlat sarauniyar fablita tana karasowa cikin masarauta...
" Su fatuwa, sarauniya fiddausi duk sun gigice yayin da sukaji cewa najlat ce....
Suna isa amarya na mota sannan suka tsaya acan baya sarki khaleel yazo ya bude mota ya riko hannun ta cikin masifa ta fizge hannunta tace kada kakara riki ne domin rashin taba juna yana daya da cikin dokar auran mu dana kafa...
" Sarki khaleel a hanzarci yajiyo yana kallon ta...
Oooh yup yup Najlat ta zama amaryar sarki Khaleel.. Abun Na Allah ne shi keyi kuma ya bayar komai nufin Allah ne...
_(Ayimin afuwa za'ajine da sauran zuwa gobe )_
_Love you all thanks for reading..._
_God bless..._
_Do vote, like, And comment..._
_Menene ra'ayin ku game da shafin nan?_
( *Wato abu ne mai kyau mu dinga sõwa 'yan uwanmu musulmai irin abin da muke sõwa kanmu na alheri, hakan kuma shi ke qãra had'in kai tsakãnin al'ummar musulmai, in muka san wasu na cikin wani tsanani to sai mu taimaka musu iya yadda zamu iya ko ta hanyar addu'a ne !!!* )
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[7/29, 11:51 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _46-48_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*
_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Tsak'i tayi sannan ta fito a hank'ali daga motar jerawa su k'ayi fadawa suna biye dasu har suk'a karasa cikin fadar sarki sannan suk'a tsaya, ummi ce tafara zuwa tayi musu kyauta sannan sarauniya fiddausi dak'e faman kallon najlat itama ta bada kyautar ta, fatuwa itama ta bayar, a hankali gimbiya bilkisu ce ta karaso fuskar ta cike da murmushi itama ta basu kyauta tare da fadin Allah yakawo 'yan biyu...
" Najlat kuwa tsabar takaici batasan lokacin da tace Allah yatsare ba...
" Shikuma sarki khaleel yaji amma sai yayi shiru haka sukayi abubuwan Al'adun su sannan aka tafi da queen najlat zuwa sashenta..
" Ruma ce tace queen najlat ki duba kawataccen ginin da Akayi miki gaskiya yayi kyau..Allah yabarku...
" Is okay please basai kin karasa ba, dukiya sarauta mulki duk baya gabana tayadda zanyi nabar gidan nan zanfarayi yanzu...
" Ruma ce tace Allah yaja kwanan ki yana dakyau muna godiya ga Allah , nasan ada kinata rokan Allah don yabaki miji kuma nasan Nagare to yau Allah ya baki sarki fablita kuma...
" Queen najlat ce tace yanada kyau kina iya bakin ki, domin zaki iya haifar wa kanki matsala...
" Allah yahuce zuciyar ki sai da safe....
Haba jakadiya me isa boka yabar najlat ta aure sarki nashiga uku shikenan zata rugurguje plan d'ina..cewar fatuwa
" jakadiya ce tace ai yanzu babu zancen boka sharri zaki fara kulla mata har sai ta bar cikin gidan sarautan...
" Koma me zaayi inaso ahada da asiro kuma inaso muyi takunnu ahankali...
" Allah yaja ranki..
Sarki khaleel ke zaune suna shirya yadda zaa gabatar da tsare da kuma tsananin dokar da'akasa da kuma cikin masarauta...
" Queen najlat tana zaune tana kallon waya sai jitayi ana fadin sarkin fablita sarki khaleel yana kan hanyar shigowa cikin dak'in queen najlat...sauri tayi ta juyar da bayanta sannan ta rufe fuskar ta...
" Assalamu alaikum queen najlat...
" wa'alaikas salam, in banda lada zan samu acikin Amsa sallamar da bazan amsa ba...
" Najlat ya kamata komai kitsaya ki...
" Yana daga cikin dokar auren mu banda magana mai tsaho...
" Au... ne mantawa nakeyi sannan ya nufi kan gado yana kokarin cire rigarsa..
" Cikin murya mara kara tace yanada kyau mutum yana cika alkawari, yana daga cikin dokar mu banda zama ko kwanciya adak'ina...
" Amma najlat...
" Hannunta ta daga masa hakan yasa ya juya ya nufi bangaren queen bilkisu..
" cikin murmushi queen bilkisu tace subhnalhi me zangani mai martaba...
" Murmushin karfin hali yayi yana kokarin cire rigarsa, nan da nan ta cire masa , hakan ya tabbatar mun da cewa baka sonta, kuma dole akayi yimaka...
" Murmushi yayi ya kwanta yace ko?
" kwanciya tayi akirjensa tace ai basai na tambayi ka amsarka,Ai da ganin fuskarka Naga amsarka...
" insonki my queen....
" Kara rungumesa tayi tace ina tare dakai zakayi alfahari dani..
" Murmushi yayi yace nagode sannan suka kwanta...
" Najlat dai datayi baccin ta cikin kwanciyar hankali bayan tayi sallar asuba tayi wanka nan aka sanar da'ita sarki yayi kira zuwa fadarsa...
" cikin gyatsene tace bazataje ba...
" Ruma ce tace queen najlat wannan ba karamin hukunci zaki jawowa kanki ba acikin fada kuma ke matarsa ce...
" Mikewa tayi sannan ..bayi 4 suka bita abaya har ta isa cikin ma sarautar cikin irin gaisuwar sarakai tayi sannan ta huce ta zauna..
" Sarki khaleel ne yayi magana cikin girmama wa yace Wannan masarauta ta tsananta akan shayeshaye da kuma fyade da girman kai kamar yadda aka samu wannan bawa.. ya sawa sarki dan tsame a lemo wanda hakan babbar kuskure ne tunda mai martaba baya son abu mai tsame...
" waziri ne yace anason kowa ya bada shawarar abunda zaayi masa..
" Ciroma ne yace asare masa kai domin yayi kokarin kashi sarki...
" fatuwa ce hukuncin kissa shiya dace dashi...
" sarauniya fiddausi ma haka tace hakama dukkan yan fada sukace...
" Sarki khaleel yana kokarin yarda da maganar queen najlat tayi magana...
" Abu uku ba a wasa da su: Addininka, da kasarka, da mutucin ka, Abu uku ba a fadar su: Arzikinka da Iliminka da yawan shekarunka, wannan hukuncin zalunci ne kuma babu kyaum.. inada tabbacin baisan sarki bayason abu mai tsame ba..Dan haka hukuncin da zaayi masa shine ajamasa kunne...
" Sarki khaleel ne yace ku sakeshi akuma yimasa kashide...
" Hakan bakaramin bata ran queen bilkisu yayi ba har ma su fatuwa ita kuwa najlat bata tsaya ko'ina ba sai cikin fadarta Nan ta zauna tana kada kafa...
" Ruma ce tace meke damunki ranke ya dade???
" Nifa nagaji da zama acikin fadar nan haba ki duba wane zalunci ace azzaluman mutane su zasu dinga bada shawara kwata-kwata ilimin da suke dashi basa amfani dashi..kuma sarki suleiman baiyi irin zaluncin nan ba....
" Ranki ya dade yakamata kina iya bakin ki domin magana zata iya sakaki acikin halaka, kuma duk abunda sukayi hukuncin masarautar ne...
" bazan iya zama inda ake zaluncin dan adam ba bazan zauna dasu ba...
Sarkin fablita sarki khaleel yana tafi zuwa fadar sarauniya najlat...ruma ce tayi saurin fita...
" Yana shigowa yayi gyaran murya yace ina fatan hukuncin dana yanki yayi daidai...
" cikin murya kasa kasa tace kwarai kuwa...
" Yakamata ki fuskan ci ne kuma ki nunamin kulawa...
" tsaki tayi sannan tayi banza dashi sai da kansa ya fita bayan fitarsa aka sanar da'ita yarima farouk zai shigo...
" Gaisuwa agareki queen najlat..
" tare dakai zan iya sanin me ke tafi dakai???
" Nazo ne neman Alfarma danAllah ki saka baki sarki khaleel yabani shugaban mayak'a..
" Ince kayi karatu kanada sana'a?
" A'a..
" lallai ma Amma kake son abaka shugaban mayaka yak'in ne zai ciyar da iyalan ka nan gaba?
Sana'arka arzikin ka,Annabi Dawuda makeri ne,Annabi Zakariyya kafinta ne, Annabi Idris madunki ne,Annabin mu makiyayi ne,Nemi na kanka, Zaman banza babbar cuta ce, Arziki kuma zomo ne, Zomo ba ya kumuwa da kwance!
" Tabbas hakane sarauniya kuma nagode da shawarar ki...
" Zama tayi tana tauna kayan marmari sannan ya fita...
Queen bilkisu ce a zaune tanata dariya jakadiya ta kallah tace kullum sarki khaleel gurina yake kwana?
" Saboda me?
" saboda baya sonta baya kaunar ta kuma..
Anya sarauniya kyace baya sonta? Ita dai ce bata sonsa...
Hahaha jakadiya kenan nice kalbin zuciyar sa, bana tunanin zaiso kowacce mace bayan ne...
" Ranke ya dade hakan yayi daidai ai sai kikara tashi tsaye domin mallakar sa...
Kwarai kuwa...
Yau ya kasance Ana taron masarauta kowanne yana cikin Nishadi kowanne yana wasanni queen bilkisu tana kokarin tafiya gurin sarki khaleel tana kokarin riki masa hannu sunata dariya..
" Queen najlat ce tajiyo tana dariya hannun ta riki da ruwa jiyowar da zatayi mayafin ta ya harde zata juyo kenan ruwan hannun ta ya watsu afuskar fatuwa (sarauniya fatima) aikam sai ta wadi...
Mutane sukayi kanta sarki khaleel yace ayi ciki da'ita...
" Queen najlat ta juya zata bashi hakuri yaja mayafin ta ta wado jikinsa...
" ke jaka ce ke dabba ce fatuwan hajiyar tawa idiot ya hankada ta....
" Kuka ta saka tashiga cikin bangarin ta...
" Queen bilkisu ce tace Na fahimce wannan matar taka batada mutunci..
" Dakatar da'ita yayi yace is okay...
" Gurin fatuwa yaje yace hajiya sannu...
" Matarka bata sona bata kaunata ta tsaneni please kaje kanuna mata matsayina...
" straight ya huce part dinta kuka taketa kamar ranta zai fita...
Najlat Najlat Najlat???
" Mikewa tayi tace wannan ya tabbatar mun bakasona ko aka gayamata da gangan nayi???
" Amma najlat baka kyautawa bakya bin ka'idar masarautar nan...
" ka sauwaki min ka saketa ko auren dole ne???
" bazani barki ba zaman auren mu ba makawa zan iya rasa raina in bakya kusa dani....ki yarda dani, murmushin soyayya zakiyi min, sanda nazo nabaki labarin zuciya yakamata ki yarda dani, kiyi hakuri halin masoya ne juriya, kina da kyau tamkar zinariya, Na saka sonki tuntuni nazamto jinin ki dan haka babu shariya...durkusawa yayi agabanta hawaye na zuba a idonsa..
" juya bayanta tayi tana kuka tace nace maka doguwar magana tana daga cikin sharudan mu...
" Kada kiyimin wannan horon, mulkina yana bukatar ki please najlat...
" Tsaki tayi tace idan kagama ta tsuniyar taka zaka iya fita...
Mikewa yayi ya fita straight fadarsa ya nufa sukayi wane dan gyare gyare queen bilkisu tasa aka sanar da najlat cewa yaune watan da kowa ama sarauta zasuyiwa sarki abinci...
" Tana cikin kitchen tana hada nata tafita yin sallah kenan fatuwa taxo ta juye mata 'dan tsame acikin miyar tata tana dawowa takama bayinta da fada ina kuka shiga bayan nafita??
" ruma ce tace fatuwa ce ta shigo cikin madafar...
" Fatuwa kuma me tazoyi??
" Duk sukace basu sani ba haka aka jerawa sarki dukkan abunda aka dafa zuna zaune afada yana cin kowannen bayan yaci na najlat sai Amai Amai....
" Ummi ce tace meke faruwa nan queen bilkisu tamatsa kusa dashi ya goge bakinsa...
" Fatuwa ce tace fadawa afito da abincin da yakeda tsame a nemi kuma kwanon wanene...
" sarki khaleel sai zare manyan idanunsa yakeyi yayi shiru kafin yadago yaga kwanon najlat ne...
" Fatuwa tace kowacece mai kwanon nan tayi niyyar ta kashe sarki dan haka tanada hukuncin shiga gidan yari na kwana daya...
" Queen najlat ce taga kwanon ta nan da nan hankalin ta ya tashi...
" Nan sarki ya sallame kowa dacewa za'a bi wacce taso aikata muguntar nan...
" wane kawataccen murmushi fatuwa tayi tace najlat bazan barki kiji dadi ko da Na sau daya ne hahaha...
" Queen Najlat ce kifaman kuka Ruma wallahi sakamin akayi ta yaya zan kashe mutum? Tayaya zanyiwa mutum abunda bayaso..Duk tsanar danakeyi masa bazan iya cutar dashi ba...
" Sarki khaleel yadade adak'in yana bayanta tana juyowa ya rungumeta na yarda dake nakuma San halinki...
" kokarin turesa takeyi yakara matsowa kusa da'ita..
" Wai menene hakane??
" Kinason Na kubutar dake?
" shiru tayi hawaye Na bin fuskarta..
" hakan ya tabbatar mun kinaso, inaso kicere duk wata doka dakika doramana kafin aure inaso kuma ki yarda zaki zama abokiyata me ban shawara...
" Afurgeci ta dago kanta tana kokarin magana yasaka bakinsa anata...
" Tureshi tayi tace kada kakara taba ne kada kakara tabani tasaka kuka...
" Ko anan narage wane radadin son dana keyi miki..ya rage naki yanzu sai kiyi shawara in kin yarda doka ta sauka akanki in baki yarda ba kuma sai kiyi ready din shiga kurkukun...
" Tsaki tayi sannan ta zauna ta rasa yadda zatayi kuka ke bin fuskar ta....
♡♡♡♡♡
Gimbiya sadiya diyar sarauniya hafsa ce ta shigo tana kuka ya sakeni saki uku....
Sarauniya hafsa ce tace me kikaye masa???
" wallahi ban masa komai ba...
" To wallahi ba zai yihuba sai najlat itama ta fito daga gidan mijinta tsinanniya ita tayi miki asiri asakeki ai....
" gimbiya ce tace shayeshaye yakeyi sannan ya zanine...
" Auwalu ne yayi dariya yace kada ki damu zan kai sunan najlat gurin boka gobe dukkan wane jindadi zaa dauke mata...
" Sadiya ce tayi dariyar murna sannan tace yauwa yarima asa itama ya saketa...
" Angama ai hahaha...
DA GASKE SARKI KHALEEL YA KAMU DA SON QUEEN NAJLAT??
QUEEN NAJLAT ZATA YARDA DA SHARADIN SARKIN??
" WANE MAKIRCI FATUWA TAKE HADAWA YAYIN DA AKA GANE ITA TA ZUBA???
" WANE HALI QUEEN BILKISU TAKE SHIGA YAYIN DATA GANE SARKI KHALEEL YANASON NAJLA???
" ASIRIN SU YARIMA AUWALU ZAICI NAJLAT???
_To All the amazing people who are reading...voting..like.. andcommenting..subhanallah i don't know how to thank you oll....._
_You people made my day and also make me smile when ever i read your comment's.._
_Allah yayi muku albarka yabiya bukatu Na alkhairi..._
_Ina jiran ra'ayinku game da wannan shafin...._
_Sorry for the all spelling and grammar error..as I couldn't get enough time to reread some page and make correction...#team SGN..#KHALEEL#NAJLAT#BILKISU#KINGDOM_
( *Manzon ALLAH (S.a.w) yace: kowace gab'a ta mutum a kwai sadaka a kanta a duk sanda rana ta b'ullo ka sasanta tsakanin mutum biyu sadaka ce, ka taimaki mutum ya hau kan dabbarsa koya dora mata kaysnsa sadaka ce, kalma mai dadi sadaka ce, ko wane taku kayi zuwa Sallah sadaka ce haka kuma kawar da duk abinda zai cutar da wani akan hanya sadaka ce.....Imam Bukhary da Muslim suka Ruwaito*)
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[8/2, 2:14 AM] Kubrieh Cie Bervier✨: _48-54_
*SO*
*GARWASHI*
*NE*
_NA NANA DISO_
http://nanadisoo.blogspot.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Queen Najlat k'e zaune ga dare yayi masarauta tayi tsit, hank'alin ta yana k'an maganganun sarki khaleel, ranta ba k'aramin b'ace yayi ba tana kok'arin cire k'ayanta taje motsin mutum jiyowar da zatayi taja mayafi tace ko wanene ba'akoya masa sallama bani....
" Shiru yayi yana Kallon ta, Nata salon yana mutukar burgesa...cik'in murya raunanan niya yace Alheri bashida sakamako sai Alheri..
" Me kake nufi? Kana nufin cewa taimakata kayi ka aurene kokuma kana tunanin banida masoya???...let me tell you Auren ka kaddara ce, kuma Har yanzu bana fidda ran rabuwa da kai ehee....
" Najlat kinfi k'owa sanin soyayyar danake miki, ina Tunanin idan wane yace mik'i bana sonki bazaki yarda ba...
" Excuse please ko kana tunanin zan manta da tozarta ne da k'ayi akam soyayya kai ne Namiji Nafarko dana faraso ko amakaranta kai ka hanani soyayya Amma daga k'arshe da ka koyamin soyayyar taka sai ka yaudare ne ka kuma ko nata ta koma garwashi..ko kana tunanin zuciyar mutum guda biyu ce? To zuciya daya ce tak sai kuma ta fashi da kuka, A yanzu indai kanason farin ciki na to ka sakeni....
" Kansa yaji kamar yana sara masa sannan yace idan sakina kike bukata to ki tabbatar kin haifa mini 'ya'ya tukun...
" 'Yaya lallai kanada ragaggin tunani kana tunanin zan haihu da wanda natsana? Kokuma kana tunanin zan zauna da makiyi na....Kuma hukuncin da'aka yanki akaina na shiga gidan yare na aminci da dai na janye sharadin mu...
" Mamaki ne yakama sarki khaleel shi dai yasan halin najlat ba haka yake ba Amma kuma kwatakwata ta chanja masa.. bazai iya jurar ganin ta cikin gidan prison ba akan hukuncin da yasan sharri akayi mata...
" Dariyar yak'i tayi tace kana mamakin nayarda ko, To wannan kadai ma ya'isa kagane natsaneka bana kaunar ka bakuma Na son zama dakai...
" Wata dabara ce ta wado masa yace lallai kam Na tabbatar dan haka sai kishirya da Asuba zaki tafi, zasu baki uniform kisa kuma aikinki aciki shine gyara dokuna da kwashe musu kaya, kuma in kin fito za'a taru afada asanarwa da duniya kinason kashe sarki...
" Kirjenta ne ya buga a tsorace ta dago idanta da hawaye ke wankewa tace tabbas kiyayyata a cikin zuciyar ka tananan tunda gashi kayarda da zalunci bayan kasan bani Na zuba maka a abinci ba...
" Gyara tsayuwar sa yayi yace ta'ina zan sani bayan kwanon ki aka gani,kuma nasan bakya kaunata komai ma zaki iya yimin...
" Ko koyashi ban iya kashewa ballantana dan uwana musulmi nacewa Allah me???
" In kinason ajanyi sai kin cire sharudan dakika sakamin, Na Barki lafiya...
" Allah yayimin tsare da sharrin ku banyi abu ba aci nayi...
Ruma ce ta shigo haba queen najlat kalaman ki suna tsauri fa...
" Ruma shugaba in mugune ne gareni bazanyi biyayya ba,Kuma kinsan inada tunani da hankali bazan shiga tarko ba...
" Tabbas hakane queen Amma kuma ina tunanin cewa Fatuwa ce ta zuba miki acikin abincin...
" Tabbas itace domin naga tafita daga kitchen din...munafurci dodo maiyi bazayaci riba ba..Amma kuma sarki yasan bazan zuba masa ba...
" Haba queen najlat shigark'i gidan prison tarajar k'i da k'imarki zata ragu kuma zaa daukeki mara amana gashi har mijinki kin cuceshi mijinki...ko kina tunanin mutane zasu san gaskiya bayan kin shiga?? Yana da kyau kiyi tunani...
" Kina nufin ruma nacere dukkan sharadin dana saka kafin auren mu???
" queen Najlat kenan kina bani mamaki ahaka kamar wayayyiya mai ilimi Amma bakisan yadda zakici ribar zama da mutane ba, idan zaki duba masarautar nan bayan ummi babu wanda sarki khaleel yakeso sama da fatuwa gashi dai bata sonsa Amma kiga yadda take nuna damuwa akansa...
" Meyasa wai duniya samsam bazatai tabbas ba?
" Mutanen cikinta sai Ahankali shiyasa...
" Najlat ce tace yanzu to ina zanganshi? Gashi gurin karfe biyu...
" Mai martaba yana fita masallaci tun karfe 4 na asuba baya shigowa cikin masarauta sai karfe 5:30 wannan lokacin zaki bi domin sanar dashi.....Ka siyawa kanka 'yanci yafi Ace ka siyawa kanka tsiya...Na barki lafiya Sai da safe...
" Allah yakaimu sannan tayi Alwala ta kwanta...
Queen bilkisu ke faman shafa gashin kirjin sarki khaleel cikin Nuna kulawa tace yau dai kamar kana cikin wane yanayi???
" Murmushin dole yayi yace duk yanayin danaki ciki tunda ina tare dake ai yagushi...
" Nagode da irin soyayyar da kake nunamin tabbas kayimin mutunci kakuma tabbatar da cewa najlat 'yan aiki sunfita daraja agurin ka tunda tazo baka taba kwana gadonta ba...
" Hmmm Ko du k'anku *MATANAH* ne kuma kowacce da matsayinta...
" Koma meye Nasan nafita matsayi ta kara rungumesa, basai lokacin da suka shiga wata duniyar ba...
Sarauniya fiddausi ke faman tsaki tana jujjuya kudin hannunta,can kuma tace wallahi indai inason mulkin khaleel to banason kudin nan...
" Husaina ce tace haba ku kullum bakwa son mutum tsana dai tsana dai..Naga yana yimiki biyayya kuma komai sai ya nemi shawarar ki...
Dallah yimun shiru shasha shai wanda basuda lafazi, khaleel din zanso? Ai bank'iba ace yanzu akashe shi...
" ke dai mahaifiya tace kuma bazan daina gayamiki abunda Babu kyau ba, kuma mugun nufi bazai taba cutar kowa ba sai mai shi, kuma rabo in yarantse hassada bazatai aiki ba...
" Tashi kibani guri kafin nakarya ke...
" Allah baki hakuri, Amma gaskiya ce sai Nafada wallahi gaskiya dok'in kowa ya hau bazaiyi Nadama ba...
" Ke dai kinfita a 'ya'yana wallahi dan uba kikeso???
" Mulki dai Na Allah ne bana mutum bani wanda yaso zaibawa abunda Allah kadai ke bayarwa ina ne ina kishi bayan nasan kowa rabonsa zaici acikin duniyar nan...
" Dan ubanki kifita kafin Na kifa miki mari, wawiya sha sha sha...
" gimbiya mero ce tashigo tace Abun Alfahari ne aciki 'yar ki tana sanar dake gaskiya, ke mahaifiyar mu ce kullum fatan mu kika sance uwa tagari kuma dukkan mu kiwo ne Allah zai tambayi ki akan tarbiyar mu, kuma ke yakamata kina sakamu ahanyar gaskiya.....
" Sarauniya fiddausi ce tace dama ke ai kinsaba sai kiyi tayi...
" yakamata ke lura kikuma duba yadda ake mutuwa bakin ciki da hassada bazai sa mutum yaki samun abunda Allah ya rubuta zaisamu...Kuma mun bi sarki khaleel domin kullum fadansa mubi Allah muji tsoron Allah...Dan Allah kiyi tunani Akan maganar mu kidaina tunanin cutar da kowanne dan adam ko dabba d'a kuma nakowa ne...
" Gimbiya mairo ce tace tabbas naji dadin fadin kalmomin nan daga bakin ki husaina...
" Gimbiya mero kwanaki nazo hucewa ina tsaye sai naji queen najlat tana gayawa jakadiyar ta cewa..Ba kowa ne ke gane cewa komi na duniya akan yarda da ikon Allah yake guda ba, Wasu kullum cikin faman yi da mutane da wahalar da zuciyar su da gabobin su kan bata sha'anin wasu suke, Maganin wadannan ka riki tawakkali da juriya da addu'a, Wallahi komi sai Allah ya yarda... Dana zauna nayi tunani sai naga maganarta fa gaskiya ce duk abubuwan danayi sai na nemi yafiyar Allah domin akwai gaba bansan irin rayuwar da zanyi ba...
" Tabbas k'inbi hanya mai kyau kuma Wanda yasan Gaskiya yaki aiki da ita, yake bin son zuciya shi wannan batacce ne in ka bishi zai halakar da kai....
" Ita dai sarauniya fiddausi tunda suke magana bata kara tankamu su ba sai ma tashiga wane tunanin...
Queen najlat tana Tashi da asuba tayi wanka sannan ta gabatar da Sallar ta daga nan tahuce tana azkar har dadai filin da sarki khaleel yake hucewa Anan taga wane d'an gidan marigayi yarima adamu haneef yanata karatun alkur'anin abun bakaramin burgeta yayi ba cikin murmushi tace sannu haneef Amma naji dadin ganinka kana karatu...
" cikin girmama yaron da baifi shekara 13 yace ina kwana sarauniya..
" Lafiya lou haneef ta samu kusa dashi ta zauna batasan sarki khaleel yana bayansu ba sai kallonta yakeyi wane sabon sonta ne ke shigarshi da yaga yadda take maganarta...
" Amma haneef bakazuwa gidana kaga sai mudinga karatun tare, inaso ina ganin yara akusa dani kaji please kadinga zuwa hakan zai eh bimin kewata kaji nema mamanka ce kaji...
" Tohm sarauniya zandinga zuwa Amma karatu da wahala so nake nadawo kamar sarki...
" Karka damu zama kafishi haneef kai dai ka dage domin Karatu akwai wuya, ilimi akwai dadi, Nema akwai wuya, arziki akwai dadi, Zama da jahilci ba wuya, rashin ilimi akwai takaici,Haka duniya take, yaro bata hankalin dare ka yi suna!...
" Kai Amma sarauniya k'inyi bari naje nakarasa karatuna ga sarki yana jiranki Abayana...
" daure fuskarta tayi sannan ta mik'i ahankali tace ankwana lafiya??
" Tayaya zan kwana kalou bayan kinaso kisaka ne acikin damuwa kinason fasamin zuciyata ko kina tunanin zan juri zamanki acikin prison???
" Cikin rashin damuwa tace Na janye sharudan...
" Baisan lokacin da ya rungumeta ta ahankali taja jikinta tafara tafiya..
" sarki khaleel ne yace Nadamu dake, inasonki, Na baki kaina, ki yarda dani Nasaki aruhina, kece kikasa nakamu da ciwon kauna Na baki jiki zuciya ta, fata nagare zantayi akanki Allah yakawo lokacin da zaki ce kina sona...
" Juyowa tayi afusace sannan taja alkyabbarta...
Bayan sarki khaleel ya shiga ya gaida iyayensa can sai ya huce zuwa gurin fatuwa suka gaisa..
" Mai martaba ina fatan anyi prison da wacce tayi kokarin hallaka ka? Domin jiya kasa bacci nayi saboda ana kokarin kashemin d'ana...
" Karki damu hajiya wacce ta aikata ai zata kara aikatawa ankuma samu akasin kanon yazo iri daya dana mutane to ankasa tantance kona wanene...
" Diriss tayi cike da bakin ciki tace to ai shikenan Allah yayi maka albarka...
" Ameen yace sannan ya huce d'ak'in queen bilkisu tana zaune tana cin tufa, cikin kalar tausayi tace Allah yaja zamanin mijina, wallahi ina cikin damuwa Aina bala'in son 'ya'ya Amma tunda nayi bari sau biyu shikenan ko cikin bana tunanin nakara dauka...
" Shiru yayi yace komai lokacine sarauniyata nima ina cikin damuwar inason naga an haifa min..
" To Allah yakawo mana akusa.. " Ameen sannan ya nufi fadar Najlat kafin yashigo aka sanar da'ita yana tafi zuwa tagyara zamanta ta juya fuskarta...
" ina fatan kin karya kinci abinci??
" cikin yatsene tace eh naci..
" Zama yayi abakin gadonta yace in babu damu yanka min fruit..
" Batare dataci komai ba ta yanka ta ajiye masa akusa dashi...
" Nagode to..Jujjuyasu ya dinga yi har nakusan minti 10 sannan tace ko baka yarda dani bani???
" Kina daga cikin mutanen dana yarda dasu...
" To sai kaci ai,..." Murmushi yayi yace k'insan ne d'an gatane Komai matata kiyimin...
" shiru tayi tace ban tambayi ka ba ai, in kuma zancen matarka zakayi min zaka iya komawa gurinta...
" Kema Ai matata ce yakamata abotar mu tafara tun yanzu mana, ki bani kula 1 zan baki goma..
" Itace damuwarka?.... " kwarai kuwa, yanzu inaso kibani Apple abaki...
" Acikin zuciyarta tace lallai mutumin nan yafara huce gona da'iri...
" Ya kikayI shiru bayan kuma mun janyi sharadin mu, yakamata kikasance mai cika Alkawari...
" tashi tayi ta dauki tufar tafara bashi abaki, kallon hannun ta yadinga yi da yadda bak'in ta tasa janbaki sha ba k'aramin kyau yayi masa ba, can yace kina masifar kyau da jan jambaki...
" Bataci masa kala ba tamiki zanje gurin ummi...
" ban baki izini ba, dawowa tayi ta zauna ta juya masa baya...in kinaso ki fita to kizo kiyimin shaving din gashin kirjina...
" Afirgice tajiyo what?? are you okay?
" Au daga nace matata ta tayani shaving shine nayi laifi??
" Abun dai ko tsari.. cewar queen Najlat...
" To wazai mun in ba queen dita ba? Kece farin cikina kuma sanyin idaniyata...
" Cikin yaudarar riyar magana tace zanje gurin ummi Nadawo sai nayi maka...
" Au yaudarata zakiyi ko?
" Ai itace ta dace da kai na tafi...
" Mikewa yayi shima zai tafi fada duk irin maganganun da Najlat ke yaba musa bayajin zafin su yarasa dalili...
Babban abunda ke tayarwa da najlat hankali bai huce kullum tazo hucewa ta kofar dak'in ruma sai taji kuka ba, yau dai ta yanki shawarar tambayarta...
" Lokacin da queen najlat ta shiga dakin sauri tayi ta goge hawayen ta tace banda kisa akirani ranki ya dade???
" A kwai abunda ke damunki Ruma kullum na tambayi ki sai kicemin bakomai??? Dan Allah ki sanar dani...
" Ruma ce tasaka kuka ta kusa minti biyar tace kinsa ne fadar abunda bazan..sai ta kara fashewa da kuka, tabbas ranar wanka baza adinga boyan cibi ba...
" Queen najlat ce idanuwanta suka cicciko tace mutuncin 'ya mace na 'ya mace ne....
" Ruma ce ta share hawayenta tace damisa d'akinta daban yak'e kowa yashiga yagama...to haka samarin zamani suke yaudarar su takan mai da so garwashe...
" Queen najlat ce ta miki tsaye tace so garwashe ne?
" Tabbas SO GARWASHI NE... Tun ina shekara goma sha shida nake soyayya da aliyu yaro ne mai hazaka ako da yaushe yana Nunamin cewa ai bashida wata 'ya mace sama dani, in takaita miki ma agarin mu kowa yasan tsakanin mu, yadda naki son sa ko kanina banso... Kullum kalmar sa mun kusa aure, Duk samari na idan sukazo sai na koresu ne sai Aliyu sau da dama aminiyata deeja takan sanar dani cewa ta ganshi tare da mata Amma sai Na karyata ta hakan yajawo har muyi fada...wata ranar sai Allah yasa yatafi sana'a birni nayi kewarsa haka yasa ya aikomin da waya, Ako da yaushe Aminiyata tana yimin fada cewa nabi duniya a hankali domin da aliyu yana sona tsakani da Allah da tuni ya aurene..Nakan nuna mata bacin raina akan maganar sa, watarana ya aikomin da dubu hamsin mahaifiyata tace bazan karba ba Amma nak'i jin maganar ta sai da Na karba Na boye, Wataran yazo kenan mahaifina yayi masa zancen turowa sai yace gini yaki yana karasawa zai turo...Mahaifiya ta ce Na hakura dashi amma nak'i..wataran ina wanki kawata deejah ta tawo aguje tana fadin ruma ankama Aliyu yayiwa wata yarinya fyade bansan lokacin dana kwara mata ruwa aka jikinta ba muka hau danbe har mahaifina yafito yana rabamu yatambayi me ya hadamu nagaya masa...Mahaifina yace deejah ai wannan munafurci ne..ai mahaifiyata tana fitowa tace deejah kawa tagare ce kuma wallahi bazatayi wa aliyu karya ba ke kuma ruma kije da halinki ba soyayya ba??? To sai ta konaki kin zama toka daga karshe kiyi nadama, kuma indai soyayya ce munga india wa duk sunyi sungama ballantana ku da ko cikakken ilimi bakuda shi...Ai kuwa daga ranar nadaina kula kowa sai Aliyu...Queen najlat abun dayake dan duniya ne Aliyu sai ya siyomij atamfa da shadda yazo yatsarane har dacewa zakiji ana gulma agare bakin ciki akeyimana anaso arabamu... Nace masa tabbas kuwa...Hmmmmm Sai ruma ta fashe da hawaye...
" Queen najlat ce tace kada ki katsemin Ki karasamin danAllah gaba daya jikina ya mutu...
" Ai in gayamiki watarana nafito ina gona ina kokarin cirar barkono sai kuwa Aliyu yazo yace min innarsa tana son ganina... Nace masa bari naje gida domin in sanar Amma yahanani nan ya yaudarine har muka shiga cikin wane gida naga wata tsohuwa wacce ki kama basayi nan tacemin nagyara mata wane dakinta ina shiga naji ana kokarin rufe kofa banyi tunanin komai ba.... kukan da ruma tafarayi shine ya tsayar da labarin...
" Queen Najlat ce tace subhnlhi karkice yaudarar ki yayi...???
" Kuka takara fashewa dashi tace gaba daya sai daya konani kurumis ashe yana cikin dakin sai naga mutum fuskarsa arufe yana kokarin danne ni inata aliyu aliyu ashe shine sai dana na bude fuskarsa nace kada kayimun haka soyayyar mu batace haka ba kada ka wulakanta ne kabari muyi aure...Tsake yayi yace aiyau sai na kita miki haddu ke saina nanuna miki cewa kudina bakici na banza ba kuma yarda badakowa akeyi ba...ina ihu ina dukansa ya tsikaramin allura ban kara ganin kaina ba sai acikin jini da yayi sanadiyar hawan jini gareni jinin danake ganin laifin nawa ne...
" queen najlat ce ta goge hawayen ta tacce tabbas so bashida Amana kuma Aliyu bai kyautaba...
" wane sabon kukan ne yazowa ruw acikin halin tausayi tace kuma sai Alokacin nagane gaskiyar da kawata deejah take fadamin ban zame ko'ina ba sai gurinta ta taimaka min nayi wanka, kuka nakeyi ina bawa deejah hakurin kin daukar gaskiyar ta Amma dayake kawarkir ki ce sai cimin tayi haka Allah ya kaddara ruma Amma komai sai kayi hakuri kuma ka jajir ce zakafi karfinsa tabbas soyayya tanada radadi Amma saboda wane kada ta sakaka ka kafirciwa ubangijinka dukkan tsananin soyayya in kina addua Allah zai cire miki, kuma duk babban dayabaki shawara kuma kinsan tagari ce kitsaya kiyi nazari domin zata amfani ki, iyaye sun huce gaban komai ruma in kika bisu kin tsira...San abun duniya kuwa babu abunda yake haifar wa da mutum sai danasani...haka nakoma gidan batare dana sanar da kowa ba nadinga kuka ko kwana biyu banyi ba naji labarin ai ya mutu...mutuwar sa ta girgiza ne hakan yasa nace tabbas wannan wane waazini garemu masu mugun hali haka na dage nadinga neman yafiyar Allah nakuma daina kula kowa har wasu na tunanin mutuwar aliyu ce nan deejah kadai tasan halin danake ciki kinga abunda son abun duniya rashin ilimi babu ma ace na addini rashin jin magana kuruciya ta jawomin sai da suka konani maras yanzu gani nakeyi babu mai sona...
" Queen najlat tace kidaina kuka ruma tabbas kin tafka babban kuskure kuma da Allah yasoki da rahama sai yasa kika koma gareshi gurin neman yafiya da ibada kuma shi Allah mai yafeyani komai kaddara ce Amma kaima sai ka karekan ka....bin maza biye musu tsananta soyayyar su in ba tsananta son Allah da annabinka ba to akwai matsala komai zamuyi muna istikhara neman zabin Allah tub farkon lamuran mu sai kiga Allah ya taimaki mu....
" Nagoge queen najlat...
" Allah ya hadaki da wanda sai soki tsakani da Allah sai anjima...
Queen najlat tana shiga d'akinta taga gimbiya amal...
" Ohhh queen ina kika shiga kodai anata harka da ogah ne???
" banson iskance yaushe kikazo???
" yanzu nazo please tambaya nakeso ki tambayar min mijinki please???
" kije da kanki mana?
" Wallahi ko naji balallai ya saurari ne ba please matar sarki wallahi ina bukatar amsarsu...
" To menene tambayar taki???
" yauwa please ayar datayi magana dangani damasu hakuri... bayani dan gani dashi hakurin ga bawa sai hadisi please...
" Toh kamar yadda naji tambayar taki nasan amsar...
" Daman nasan kinsani ai to ina bukatar bayani...
" Allah SWT yana fad'a cikin suratul Baqara (155-157) cewa:(...Kuma ka yi bishãra ga mãsu haquri..
Wad'anda suke idan wata masifa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mu ga Allah muke, kuma lalle ne mu, zuwa gare Shi, mãsu kõmãwa ne"..
Wad'annan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma wad'annan su ne shiryayyu )..
" Yauwa nagode sai kuma hadisi queen..
" Kuma yazo a hadisi cewa Abdullah 'Dan Mas'ud yace: Na shiga wajen Manzon Allah SAW a lõkacin yana zazza'bi, zazza'bi mai tsanani, sai nace da shi:
"Lalle kana zazza'bi, zazza'bin mutum biyu". Sai yace: Haka ne, ina yin zazza'bi kamar yadda mutun biyu cikinku ke yi Yace ...sai nace: "Hakan na nufin kana da lãda biyu kenan? Sai yace:( Haka ne, kuma bãbu wani musulmi da cuta zãta sãme shi, tun daga rashin lãfiya da wanda ba shi ba; fãce sai Allah ya kankare/zubar masa da munãnan ayyukansa kamar yadda bishiya take zubar da ganyenta...Bukhary & Muslim
" yauwa Allah yakawo 'yan biyu..sai dan bayani please..
" Wato Allah ya riga da ya tsãra duk abin da zai fãru ga bãwa, wannan abun kuwa d'ayan biyu ne; ko abin da rai ke so, to, sai muyi gõdiya, ko kuma abin qi, to, sai muyi haquri ! Kuma mu sani cewa Allah yana jarrabar bãwa ne gwar-gwadon Imãnin bãwan...!!!
" To ne zanyi gaba sai zuwa gobe inshaa Allahu...
" Ba fadi ne yace Allah yaja kwanan ki sarki yana kiranki acikin Dak'in sa..
" To tace sai datayi kusan minti 20 taje tace lafiya...
" Inason shawararki dangani da yak'in da zamuyi inaso dukka rundunar mu su huce...
" Tabe baki tayi tace me ruwana da zancen yaki kuma???
" Haba my love kinfa janye sharadanki kuma mun zama abokai kinga sai kibani shawara...
" Atawa fahimtar zaifi kuraba mayakan biyu runduna daya suyi gaba tun asuba sai kuma su boya abayan duwatsu runduna na biyu sai su tafi da safe...
" Menene hikimar hakan to??
" Ayayin da inda zaku yaka zasu kasance cikin shirya shiryan su da asuba zasu kuma sakan kamce tunsun san sai safiya zaku fito Amma in runda ta farko ta afka musu da asuba hakan zaisa suyi saranda kuma bazasu samu karfin yakin ba daganan zasu bada gaskiya in sukaga runduna ta biyu...
" Tsayawa yayi yana kallonta such a nice wife friend...Allah yayi miki albarka i love you...
" Albarkar dai amin amma soyayyar ka is not my business...
" Har tayi kofa ya tsayar daita yakaraso yace queen najlat khaleel...yarinya yar kwalisa gata da shiga irin ta alfarma, ga lafazi irin gidan girma..kamar tayi magana ya matso batasan lokacin da ya shammaci ta ba ya fara kissing dinta..dakyar ta tureshi idonta duk yayi ja...
" queen bilkisu ce ta shigo tagansu ahaka queen najlat tayi waje suka bangaji junan su....
Assalamu alaikum...
( *Ku jira sauran zuwa gobe)*
*KOYA ZATA KAYA???*
_INAJIRAN RA'AYINKU DANGANE DA SHAFIN NAN..AND TODAY I WANT MY ALL SILENT READERS TO PLEASE COMMENT AND VOTE...LIKE_
*INA MUTUKAR GODIYA DA KUMA FATAN ALKHAIRI GA DUKKAN MASOYAN LITTAFIN NAN ALLAH YASAKA MUKU DA ALHERI*
_....i thank you all for being such a wonderful readers.._
*Sorry for all the spelling and grammar error...#TEAM SGN*
_Wanda ka yiwa alheri wato ka taimake shi a rayuwar sa, ka tsaya akan hidimar sa, Amma ya dawo yana rama maka da zagi, ko yana aibata ka, ko ya nuna maka rashin godiya. To ka da ka damu, kayi hakuri ka zuba masa ido, kuma kada kayi masa gori, hakika mafi yawan masu butulci rayuwar su cikin nadama take karewa, Kuma tabbas zai samu wanda zai yi masa fiye da abinda yayi maka, Kai kuma Allah zai saka maka_
*'Yan uwa mu sani duk abinda kowa ya shuka shi zai girba a duniya da lahira,Nakan ji tsoro in na tuna cewa: Wanda ya aikata alheri ko da baifi kwayar zarra ba zai gani, Haka nan wanda ya aikata sharri shima ko da bai fi kwayar zarra ba zai gamu da sakamakon abin da yayi a duniya da lahira*
_Masu magana kance alhaki kui-kuyo ne mai Shi yake bi.._
*Allah ya tsare mana imanin mu da mutumcin mu....amin*
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
No comments:
Post a Comment