Sunday, 13 August 2017

SO GARWASHI NE 54-63

[8/6, 1:04 AM] Kubrieh Cie Bervier✨: _54-57_

    *SO*
        *GARWASHI*
                        *NE*

_NA NANA DISO_

      http://nanadisoo.blogspot.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Queen bilkisu ce tayi Mata wani irin kallo cikin isa ta karasa kusa da khaleel ta dafasa yanaga idonka yayi ja??

    " Shiru yayi kawai Yana kallon ta, can kuma yace tunanin ki nake tayi ....

    " Murmushin kissa tayi tace Namijin mazaje kenan, Allah yabaka iya kalami...

   " my queen mu zamu fita yak'i I need your du'a...

    " Cikin rashin jindadi tace hakan ya nunamin kun tattauna da najlat akan yaqin kenan???

    " Kwarai kuwa domin hakk'inta ne akaina tambayar ta shawara...

    " Wane kuna taji har cikin zuciyarta Amma sai ta nuna bata damu ba tace eh hakane fatan alkhairi agareku baki daya...

   " Nagode sannan ya shiga bandaki...

    Queen bilkisu ke faman zagaye lallai sarki yafara son najlat ya kamata ayi wani abun akai...

    " Tuntuni nake nunamiki hanyar tsira Amma kina tunanin hanyar halaka cewar jakadiya...

    " Yanzu me kikeso ayi? 

    " Tashi zakiyi tsayi kidinga kunsa mata takaici tare da bata mata rai...

    " Tayaya???

" Ta kissa mana kissa...

      " Hahhaha kice nayi mulkin da mukeyi atamu masarautar, zan nuna mata ni daya ce matar gold...

    Yauwa hajiya haka nakeso...

Ruma ce tace Ka nemi girman duniya da aikinka, kada ka nemo shi da asalin babanka..

    " Queen najlat ce tace tabbas Laifin da tufar arziki ta boye, idan iskar tsiya ta zo sai ta bayyana shi, me yafaru ruma?

  " Fa'iza ce tasanar dani cewa sadiya mijinta ya saketa wata daya daya huce....

    " Azaburi queen najlat innalilahi wainna illahir rajiun ita kuwa me tayi masa haka, ta dafi kanta tare da hawaye yana wanke mata fuska....

    " Ruma ce tace kada kiyi kuka queen wannan kaddara ce daga Allah in baki manta ba lokacin daza'a kawoki gidanki mahaifiyar sadiya haka tace Allah yasa asakike sai gashi 'yarta aka saka kuma dama bahaushe nacewa Tuntuben harshe ya fi tuntuben kafa zafi, Na kafa saurin warkewa yake yi, na harshe kuwa illanta mutum yake yi har karshen rayuwarsa...

     " Cikin rashin jindadi najlat tace Amma kuma inason zama agida yanzu ruma...

     " Ai dama darajar 'ya mace to gidan mijinta, kuma makiyanki babu abunda suke fata irin suga kinfita daga wannan kawataccen gidan, kuma sarauniya kada kimanta ba duk abunda kakeso kake samu ba,ya kamata kimanta da baya ki fuskanci gaba kodan makiyanki....

      " Amma ruma tayaya zan'iya zama da wanda bana sonsa?

    " Ai ita soyayya ahankali take shiga lokacin da zaki fara sonsa bana tunanin zaki tuna da kiyayyar da kikayi masa...

    " Anya ruma?

        " Hmm queen najlat kenan kina mutukar bani mamaki wallahi kin manta aure ibada ne mijinki ne fa bakakin maganganu bai kamaci ki ba, duk abunda zakiyi indai zaki faranta masa zaki samu lada fa, Idan ka kyautata ma mutum za ka mallake shi....

     " jikin queen najlat ne yayi sanyi tace Amma kuma inkika lura zakiga baya sona! Yafi son queen bilkisu hatta shawara da'ita yakeyi....

   " kefa marainiya ce shiyasa nace miki ki rufawa kanki asiri ki zauna da mijinki lafiya domin har mahaifiyar sa itama sai ta daina sonki indai ta tabbatar da bakyason danta?

    " ummin kike nufi haba ummi bazata taba cancajamin ba...

     " Tohm kishiga gidan dadi lokacin da queen bilkisu ta shiga zakiga wacce zata fi tararraya...

   Kuma kowanne miji yafison mai kyautata masa mai kuma tararrayar sa, bama kisan wani abu ba queen bilkisu ba haka take ba Amma na tabbatar mijinta yagyara ta...

    " Tayaya kikasani?

  " Tabbas Na manta bansanar dake abu guda daya ba.. Nayi aiki amasarautar su queen bilkisu masarauta ce kazama wacce ko sallah bata damesu ba kuma suna shan giya kamar yadda kuke shan ruwa, bilkisu bakowa bace ba illah 'ya ga hajiyar gidan tana mutukar santa ke ingayamiki ma bilkisu sai datayi shekara 12 akadaina yimata wanka, kuma tanada rashin kunya Amma abin mamaki mijinta yagyara ta tsaf sai kace wane malami....

     " Sarki khaleel Allah ya bashi ilimi both na addini dana boko kuma ya koyar da makarantu da dama har ma da jami'oi...

     " To kinga tabbas sarki yafison queen bilkisu domin tafi damuwa dashi kuma bata ya'bamasa maganganu, ga maganar sa da takeji
....

    " Nagode ruma tabbas maganga nunki sun ratsamin jiki duk da naji zafin wasu Amma mai sonka kadai zai gaya maka gaskiya nagode yaruwa...

    " Babu komai ranki yadade duk abunda nafada bakiji dadinsa ba kiyi hakuri.....

Najlat tana k'wanci hawaye yanata wanke mata fusk'a tunanin irin munanan maganganun da tak'e gayawa sark'i k'uma bai taba tanka mata ba zuwa cikin muryar fadawa taji sunci Sarkin fablita sarki khaleel yana tafi zuwa cikin fadar queen najlat..

    " cikin kasalalliyar murya tagyara kwanciyar ta ta juyar da fuskar ta da hawaye ya wanke mata....

     " Sarki khaleel ne yayi sallama cikin sanyin murya ta amsa masa..lafiya queen najlat??

    " hawayen fuskarta tayi saurin gogewa cikin kuzari ya karaso kusa da'ita ya dagota please meke damunki???

    " Kallonsa tsaya yi nakusan mintina sannan tace babu komai fa...

     " cikin nuna kulawa Sarki khaleel yace konayi miki laifi ne kokuma wata ta batamiki acikin masarauta??

" Tashi zaune tayi tace babu wanda yabatamin fa kawai ina tunanin mamata ne...

    " Najlat kenan har yanzu baki yarda inasonki ba kenan? Nisartar kanki agareni bakaramin illabani ba, masarauta tana bukatar masu ilimi...

    " ilimi kuma? bayan kuma kanada kudi??
   
    " Ilimi ya fi kudi, kuma ya fi mulki, Ke har lafiya ma ya fi ta, Kudi da mulki da lafiya duk suna gushewa, Amma Ilimi yana nan tare da mai shi ba su rabuwa...

    " Murmushin karfin hali tayi tace hakane ba yanzu zaku tafi ba???

     " basu karasa wasu shirye shirye ba....

    " To Allah yabaku nasara ta koma kan gadonta...

    " queen Najlat sannan ya shafa fuskarta tunda so yay gini in k'ingujin to za'aji kanmu..

    " So kuma?? Bayan abota mukeyi?...

    " ke komai nace, kawa,mata,masoyi ya komai ma, sannan ya dago kanta...kullum zuciyarta tana radadi kaunarki cikin raina danAllah ki tausaya min kalaman so gayamin, shi so indai yakama mutum akwai matsala in yafici, idan Na rasaki zan maci, tunani na ma zai baci....

   "Wasu sabon hawayen ne ya wanke mata fuskarta tana kallon sa mamaki ne ya kamata tabbas komai Nufin Allah ne yau ita yarima ke gayawa kalaman nan....

   " ki daina tunani najlat kinsan bakida ishasheyar lafiya kinji...

    " Ba tunani nakeyi ba ranka shi dade..

    " Kamar asama yaji sunan jiyowa yayi cike da jindadi yace Nagode da wannan sunan dakika kirani, please ki kularmin da kanki, in nayimiki kuskure kiyi hakuri...

     " Murmushi tayi tace tohm shikenan yadda kace haka za'ayi...

     " Tohm nagode da amsamin dakikayi Allah yayi miki albarka sannan ya sumbaci bakin ta..

Straight sarki khaleel ya huce gurin ummi gaisawa sukayi sannan tace nikuwa ya zamanku da najlat?

    " Murmushi yayi yace yanzu ma muka rabu da'ita..

     " Tana sonka kuwa naga bata damu dakaiba...

    " Murmushi yayi yace tana sona ummi...

     " To Allah yakawo 'Yan biyu...

      " murmushi sukayi sannan ya huce zuwa gurin fatuwa nan suka gaisa sannan ya huce zuwa filin yaqin yanata Allahu akbar mayaka sunkai 4000 sannan...

    " Queen bilkisu ce tatawo dauke da wata 'yar akwati sannan tayi masa wata gaisuwa sannan ta bashi tare da fadin nasara tana tare dakai ta rungumeshi...

    " queen najlat da jikinta duk yayi sanyi sarki khaleel ne yace ke mizaki bani?

    " wane iri taji tarasa me zata bashi kallonta dayaketa yi yasata cire wani zobinta tasa mai ahannu ta dago kansa tare da nasara tana tare dakai mijina...

Mijinki wane murmushi yayi da ya haifar da hushiryar sa sannan yace duk wanda yanuna bajinta shi zaa yabawa...

    " Juya tayi zata huce fatuwa tace Ai bishiyar datayi rissa batasan tushiba..

    " Wane kallo queen Najlat tayi mata tace ki iya bakinki da matar sarki kike magana...

    " Tsaki fatuwa tayi tace ai kinkusa tafiya dan yakusa sakinki tunda daman ba sonsa kikeyi ba...

     " Queen najlat taji haushin kalmar amma sai cewa tayi aiki kadan mai dorewa yafi yawan surutu mai hucewa...

    Tana karasawa gaba tace ina gaisuwa ummi...

    " banza tayi mata sannan ta kau da kanta...

     " Queen bilkisu ce takaraso cike da faraa ta rungume ummi tare da fadin kin kwana lafiya?

    " Lafiya lou queen dafatan kina lafiya kima...

    " Queen bilkisu ce tace lafiyar dai ragaggiya ce tunda mijina ya tafi jihadi...

     " To Allah yakawo 'yan biyu...

     " Queen najlat datayi saurin barin gurin fuskarta dauke da hawaye tana shiga masarautar ta tarar da haneef tare da qurani a hannunsa zama tayi kusa dashi tana kokarin maida kukanta...

    " kada kiyi kuka sarauniya mai albarka nasan batamiki akai shi mutum sai kayi hakuri dashi kinga nima nayi hakuri da mutuwar babana...

   " Hawayen ta tashare tare da fadin haneef wayake koya maka wannan maganganun??

    " murmushi yayi yace mata masu hikima da tunani irin naki sune makaranta ta, kuma kinsan Idan ka kasa gane wurin da ka yi shuka kada ka samu damuwa, Watarana ruwan sama ne zai nuna ma ka,Haka rayuwa take, Yau da gobe babbar makaranta..

     " To kawo muyi karatun kada time din makaranta yayi...

     " Basu gama ba sai gurin sha biyun rana sannan ta bashi tufa yatafi...

     
♡♡♡♡♡

   Yarima auwalu ne gaban boka shi da kanwarsa gimbiya sadiya boka ne yasa dariya hahhahaa kunaso akashewa najlat aure ko?

    Gimbiya sadiya ce tace kwarai kuwa ....
 
     " To zamu kashe mata Amma da sharadi guda daya yarinyace mai ibada bata wasa da sallah ku ingaya muku koda mun tura mata aljani bazaiyi tasiri ajikin ta ba....

    " Yarima auwalu ne yace saboda me boka???

     " Saboda tanayin azakar bata taba fashin sa...

    " gimbiya sadiya tace to boka atura mata ayayin datake bacci mana...

    " Tana zikirin bacci koda natura aljanu dubu sai sun kone amma gawata dabara wannan hayaki gari ne ku tabbatar kun watsa adak'in ta indai har tashaka ko ta taka to daga ranar zata bace baza akara ganinta ba.....

     " yarima auwalu ne yace godiya mukeyi tsinanne hahahha wannan labari ne mai dadi...

     " Boka ne yace ko kawomin saniya da jaka guda daya shine ladan aikin ku....

      " Toh angama sannan suka isa gida...

     " Gimbiya sadiya ce tace to tayaya zamu iya watsa mata??
   
   " Sarauniya hafsa ce tace ke zaki shirya daniyar kinje gurin ta sai ki watsa acikin dak'inta amma kada ki saki kifi awa 1 acikin masarautar...

     " sadiya ce tace toh...

     " Duk maganar da sukeyi kamar akunnen bah-bah nan tasanar da faiza tace batada kudi awayarta bari ta bayar asiyo mata kati..

♡♡♡♡

    Queen najlat ke saune tana faman karatu kamar daga sama taji sallamar gimbiya sadiya ....

    " Lallai ne sarauniya irin wannan fada haka kalli yadda kikayi kiba...

    " Queen najlat ce ta murmusa tace Allah ko?

    " eh mana yagida ya mutanen gidan? Ina mai martaba...

    " yana kalou yana gaida ki, kinga ne bari na tafi sauri nakeyi fa...

   " Ahh bakwana zakiyi ba???

    " kinga sai anjima..

   " kitsaya ina zuwa tashiga da wayarta cikin dakin zata dakko mata kaya aikuwa sai gimbiya sadiya ta watsa maganin tayi saurin fita ....

   Faiza ce tayi maza kiran najlat cewa kada ta fita palour sun watsa mata magani..

     " Magani kuma faiza? Gaskiya ban yarda ba...

    " Najlat ki tsaya ki saurari ne sun...

    " Aikuwa sai ta katse wayar gaba daya ma har zatafita, sai ta tuna da maganar mamanta masoyinka baya taba zama makiyinka...

    " Ta kusan awa daya adaki sannan tayi bismillah tare da karatun alkurani ta fita zuwa kan kujera...

    " Faiza ce ta kara kira hello queen najlat babu abunda ya sameki ko???

    " Faiza kenan da Allah na dogara shine zai kareni inakuma neman tsarin sa da surari da kuma adduoin da fiyayyen halitta saw yakoyar, wayo na dabarata bazasu hana asiri kamani ba Amma imani na da tsoron Allah zai hana kuma Allah zai kareni....

   " Tabbas kingama magana..kuma daman kinsha fada Kada lamarin duniya ya dame ka,Duk abin da ke cikin ta na Allah ne,Kada sha'anin arziki ya dame ka,Domin daga wurin Allah yake fitowa,Kada ka samu damuwa a kan gobe, domin a hannun Allah take,Abin da ya kamata ya dame ka shi ne, neman ka samu yardar Allah....

     " Tabbas hakane faiza nagode mujima dayawa....

   ♡♡♡♡♡

Hahaha dariyar yarima auwalu nasan yanzu najlat tabata bamai neman labarinta kuma....

    Anya kuwa maganin mai kyau ne cewar sarauniya hafsa yanzu sukayi waya da mahaifin ku...

     " ke sadiya kinzuba kuwa?

     " wallahi koina sai dana watsa...

    Jikin yarima auwalu ne yayi sanyi sannan ya mike....

   ♡♡♡♡♡♡

Yau sarki khaleel suka dawo sunyi nasara a yak'in sun kuma samu bayi dayawa suna isowa akayi cikin dakin sa dashi yana kwance duk ya jigata nan yasanar da bafadin kada yasanar da kowa yana nan yakirawo queen najlat j
Kawai...

     " Tohm yace sannan yasanar da queen najlat sauri tayi ta'isa dakin tana shiga taga jini na zuba ajikin hannun sa cikin gigicewa tace bari nasa akira mai magani....

    " Queen najlat zoki yimin dakanki...

       " Allah sarki najlat duk tausayi ya ki dimeta kasan mace da rauni sai hawaye ne ya zubo afuskarta...

      " Wane irin sonta ne yakara shigarsa cikin zafin nama yake kokarin mikewa aikuwa tayi saurin kwantar dashi ka huta bari nakokarta maka to nan ta daure masa gurin tasaka masa magani sannan ta mik'i zata tafi ya kamota...

     " Bari nasa asanar dasu ummi kaji??

     " ke kadai nake da bukatar gani please karki tafi najlat wallahi soyayyar ki tana kokarin halakar dani ....

      " Idonsa ta kallah dayayi ja tace Amma kuma ai...

      " ai me please kada kisani cikin wane hali kizauna kusa dani kiyimin firar kauna....

       " hawaye ne ya wanke mata fuskarta sannan tasa masa kuka aikuwa tuni yasa bakinsa anata duk jikinta ya mutu lokaci daya kuma tamiki...

    " Cikin fada tace nace maka..." Dakatar da'ita yayi yace kinci me? Bayan kin janye sharadan ...

     " Mikewa tayi zata fita yace haka zaki barni cikin yanayin soyayya wahala da gajiya???

    " Incen kanada wasu matan sai kakirasu...

    " Ummi ce tace yanzu kika tabbatar min bakyason sarki khaleel to kisani duk halin da sarki ya shiga akanki to wallahi bazan yarda ba....

     " Ummi please kibari bakisan maganar me mukeyi ba cewar sarki khaleel...

     Ummi ce tace you better keep quiet, so kake kamutu da sonta ne son ai ba dole baniba, ka kyaleta kadinga hulda da wayanda suke sonka ko so takeyi ta konaka ka zama garwashi???...

    " Queen najlat ce tace ummi wallahi...

      " Bana bukatar komai daga bakinki abeg move naji gurin d'ana .....

    " Mamakine duk yacika najlat ummi mai sonta yau ita ke gayamata wannan maganar? Kuka tasaka sannan taruga cikin fadarta....

    " Yadda najlat tafashe da kuka har cikin zuciyar sarki khaleel Amma ummi...

   " karkacimin komai akan yarinayar dabata sonka kawai karab.....

     _ASSALAMU ALAIKUM_

*INA NEMAN AFUWANKU DAKUKA JINI SHIRU KWANA BIYU, KUSANI CEWA SAKON NINKU SUNA TADDANI KUMA INA GODIYA MASU BADA SHAWARWARI KUMA NAGODE MASU YABON LITTAFIN KUMA INA GODIYA...ALLAH YASAKA MUKU DA ALHERI YASA KUNA AMFANA SA DAUKAR DARASI ACIKI....*

    _INAJIRAN RA'AYIN KU DANGANE DA SHAFINNAN_

      *THANK YOU OLL FOR BEING SUCH A NICE WONDERFUL READERS*

       _AM SORRY FOR THE SPELLING AND GRAMMAR ERROR..

   _PLEASE DO VOTE LIKE AND COMMENT_#TEAM SGN

*Manzon Allah SAW yace: Ina hanã ku/ku guji qaramar shirka. Sai suka ce: Mene ne qaramar shirka? Sai yace: Riya, Allah zai fad'a a ranar da zai yi sãkayya tsakãnin bãyi bisa ga ayyukansu, cewa ku tafi zuwa ga wad'anda kuke yin aikin don su gani a duniya; kuje kuga ko/shi zaku sami sãkamako a wajensu..(Musnad Imam Ahmad) Allah yatsaremu*

  _Wato riya na daga manyan zunubi, haqiqarta kuma shi ne bãwa ya yi wani aiki da akeyi don Allah kad'ai amma sai ya yi don a yabe shi! Duk wanda yake hakan to ya rusa lãdansa; don shi Allah mawadãci ne yana barin aikin da aka had'ã shi da wani ga wanda aka had'ã shi da shi din!!!_

   *Amma bayan cikin riya bãwa ya yi aiki don Allah sai kuma a sami wasu su yabe shi akan hakan; wannan ma d'aya ne cikin bushãrar da mumini zai samu tun a duniya kafin gamuwa da karamcin Ubangiji...*

  Allah katsaremu da aikata riya...

   Urs *Nana diso*

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[8/7, 10:51 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _57-60_

    *SO*
        *GARWASHI*
                        *NE*

_NA NANA DISO_

      http://nanadisoo.blogspot.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Haba ummi wannan maganar bata dace dake ba yadda kikeson najlat?

    " Kaga kasan mai sonka, duk wanda bayason d'anka ai ba masoyin ka baniba...

     " Amma ummi ai bakisan yadda take sona acikin ranta ba..

   " Kaga mai martaba ba dolene kafadi abunda kasani ba Amma yanada kyau kasan me kake fada...

     " Shiru yayi baice mata komai ba har ta fita....

    Queen najlat dake faman kuka duk hankalinta ya tashi umminta ce yau tayi mata haka?

     " Ruma ce tashigo tace me yafaru ranki shi dade?

      " jiyowa tayi tagyara mayafin dake jikinta sannan tace abunda ummi tayimin bantaba tunanin sa ba wallahi na dauketa amatsayin mahaifiyata wacce zata sharemin hawaye na Amma ki dubi abunda tayimin...

   " Hakuri zakiyi ranki yadade kuma kima sai kin gyara babu uwar da zataso a tsane d'anta...

   " Toh Allah yakaramin hakurin rashin uwata wato ako dayaushe takan cemin Karamin yabon da mutane za su yi maka, ya fi yawan yabon da ka yi wa kanka....Ada nayi hakuri da tozarcin da danta yayimin ya wulakanta ne yanuna baya sona Amma ki duba yanzu nice matarsa kuma ace Bazanyi zuciya ba? Ko kare ya cinye tawane??? Gwara arabu da ahargitsa zumunci...

    " Batasan sarki khaleel yana bayanta ba tuntuni yayiwa ruma alamar tafita...

    " gyaran muryar da yayi shiyasa ta jiyo fuskarta dake wanke da hawaye....Najlat nasan ummi bata kyauta miki ba Amma yakamata kiyi hakuri nasan bakyasona Amma kulawarki gari ne zai rufe sirrin zuciyarki...

    " kana tunanin zama da wanda bakyaso zai iya kwarar ka?...

    " Queen najlat abunda bazai taba yihuwa ba shine rabuwar mu, Nasani samu shine farin cikin mai nema.....

    " Ai kai bakada matsala tunda Ne kakeso Kuma kana tare dani...

    "Shi gani sai dai ido,karkisa natako garwashi, ina kaunarki inakuma son zama dake tarin dayayi shiyasa ya zauna abakin gadon ta...

   " Shiru tayi sannab tafita daga dak'in....

  
   Haba jakadiya wannan impossible ne tayaya zaace wannan jakar yarinyar tazo har tana kokarin shiga zuciyar sarki, naje ina yimasa sannu da zuwa amma kawai ambaton sunan najlat yake...ai wannan iskance ne wallahu ita wacece wai??

   " Jakadiya ce tace ranki yadade yana dakyau kiyi hakuri..kuma ita wannan sarauniyar wato queen najlat dakanki zaki fidda ita tunda daman auren dole akayi mata....

    " what kina da tabbacin abunda kike fada??

    " kwarai kuwa queen najlat ta aure sarki ne abisa umarnin mahaifin ta kuma batason sarki koda da kwayar zarrah.....

     " queen bilkisu ce tace really? Wannan labarin yayimin dadi sosai da sosai kuma sarki mutum ne mai mutukar son kulawa kuma bata bashi hahaha zatasan cewa queen bilkisu ba saar wasanta bace ba.....

     " haka yakamata kiyi sarauniyata ki kuntata mata da muggan kalamai kada ki raga mata...

   " Mekiwa tayi ta huce zuwa fadar sarki nan ta tarar babu kowa aciki sai ta huce dakinsa najlat na zaune kan wata kujera tana danna waya, queen bilkisu ce tace sannu fa...

    " Queen najlat ko dago kanta batayi ba tace sannun ki fa...

    " Queen bilkisu ce ta shagwabe tace tuntuni tunanin ka ya hanani sukuni dear...

   " Sarki khaleel ne yayi fara'a yace nima ai naki nakeyi...

     " Nasan balallai kace abinci ba dan bakowa ke damuwa da cikin nakusa dashi ba....

      " Shiru yayi yadda yaga najlat ta dago kanta yace zuba mana nida Queen najlat dan nasan bata ce komai ba...

    " Sauri tayi tatashi tsayi no na hutashar dake basai kin zuba ba Na koshi sannan ta fice tayi hanyar fadarta....

    " Daman nagaya maka wanda ya damu dakai shi keyin komai dakai...

    " Queen najlat ce tajiyo tace Kada ka bari girmanka ya fadi a kan kalma guda daya da za ka sosa kaikaiyin bakinka da ita, Kada ka bari tuntuben guda ya zubar maka da mutunci...

    " Ke ki iya bakinki domin ne auren soyayya mukayi kuma ba dole akayi mana ba...

    " Tsaki queen najlat tayi tace au ashe ku kunason junan ku? Ai ne kaya aka hadani da'ita kuma nakasa banbare ta da zaki taimaka kicire min da kin taimaki ne....

    " Cikin zafin nama sarki khaleel yace fita daga dakin nan kifita daga dakin nan...

     " Queen bilkisu kuwa kuka tafashi tashi tare da rungumar sarki khaleel yanzu kai take gayawa wannan maganar mijina kada kadamu ai ne ina tare dakai...

    " Lokaci guda idanuwan sa suka kada baisan lokacin da yace ku kyaleni na huta kada kusa kaina yafashe...

    " Queen bilkisu ce ta sumbaci bakinsa sannan tafita...har cikin dakin najlat tashiga tace yanzu mukafara zubawa dake kuma kisani sai nasaki kinsa an sakike da kanki...mijina nawani kuma zuciyarsa tawace duk kwarkwarorrin dake fadar nan bazu isa suja dani ba ballanta na kuma ke karamar kwaruwa bansan ma me yagani ajikin ki ba da yace yana sonki....

     "Amma kin bani mamaki..wato kashedi kikemin ko labari kokuma surutai? Miji dai nawane kamar yadda yake naki kuma soyayya ina tunanin kinfine sonta domin ne nasamu miji mai mutukar masifar sona kuma kisani Idan kai maciyin tuwo ne, kada ka zagi Sarkin noma....zaki iya fita queen bilkisu kuma gaba ki nemi izinin shigowa cikin fadata please...

   " Queen bilkisu ce  taji kunya sai kuma ta lallaba tafita...

♡♡♡♡

   Sarauniya hafsa ce tace me isa naga kanata haki yarima auwalu??

    " Farin cikin najlat shine bakin cikina so nakeyi atsanita duniya tayi mata zafi ki duba fa kiga inna najlat tafini matsayi yanzu fa matar sarki ce so nakeyi akashe ta kowa ya huta...

    " Adai kara kai sunanta gurin boka shine za'ayi maganinta cikin sauki....

    " Yanzu daga gurin bokaye biyar nake dukkanin su sunci tafi karfinsu in akayi aikin da kanta take karyawa...

     " Au itama tsafin takeyi datake karyawa???

    " Aa wai azkar da karatun alkurani kuma tanayin wane abu naganyen magarya...

    " Tsinanniya karka damu ni dakanta zan kashe mata auren ta kada kadamu ka kwantar da hankalin ka nima banason farin cikinta...

  " Sarki salim ke zaune afadarsa tunanin sa kawai najlat can yasa waziri yakirata awaya cikin murna tace babana nayi missing dinka kana lafiya?

    " kina dai cikin kwanciyar hankali ko? Baki da wata matsala kokuma kina bukatar wane abun?

   " Ina lafiya ranka shi dade bani bukatar komai ana bani kulawa...

    " Najlat kibi mijinki kiyi masa biyayya ki zauna da iyayensa lafiya mahaifiyar ki mutuniyar kirki ce kuma ina yimata fatan Aljanna tunda ta mutu wallahi ban samu mace kamar ta ba....

    " Shiru tayi tana fuskan tar mahaifin nata, ina inna da sadiya???

     " Kada kidamu da wayannan mutanen domin basa kaunarki duk inda kike kidinga addua kinji inajira haihuwa da jikokina....

    " Jikinta ne yayi sanyi cike da tunani ita da ko! Kwana gado daya basu taba yi da sarki khaleel ba...

     " yanaji kinyi shiruwa najlat ko kin kusa haihuwar ne?

     " Batare data bashi amsa ba tace duk naji ranka shi dade kuma zanyi yadda kace a gaida mutanen gidan...Allah yakara lafiya da nisan kwana...

   ♡♡♡♡♡♡

kowa yana zaune afada banda queen najlat dan batasan ma yau da zama a
Fadar ba...

    " Ne sarki khaleel bazanci komai dangani da sha'anin bawan Allah nan da ya kade wata baiwar Allah batare da sanin sa ba dan haka nake bada sanarwa acikin matan nan kowacce ta fadi hukuncin da yahau wuyan wanda yayu kisan....

    " Kowacce ta shirmen datake fada fatuwa ce tace kawai akashe shi sarki yayi alamar aa...queen bilkisu kuma tace shima akadeshi ya mutu....husaina ce tace to mai martaba ai duk wanda yakashe kawai akashe shi ...

    " Duk wanda ya amsa yanada tambayar da zaimun ko ta mecece zan amsa masa kuma na bashi kuma zamu fita dashi yawon gari tare....

     " Nan kowa yadage yanata sambado hauka wanda wasu amsarsu ko hanya basu kaiba...

    " Tunda naga kun...Ranka ya dade inada magana cewar najlat ....fatuwa da queen bilkisu sai faman hararar ta suketayi...queen bilkisu tace yana dakyau kiyi shiru domin baci zakiyi ba...
    
   " ko kinsan amsar tambayar ne cewa sarki khaleel...

    " Queen najlat ce tace tabbas kashe rai yana daga cikin Alkaba'ir wato manya manyan zunubai....

     " queen bilkisu ce tace kowa yasan hakkan muna bukatar bayanin ki akan tambayar da sarki yayi....

    " Queen najlat ce tace  Allah SWT yana fad'a cikin suratun Nisã' (93) cewa: Kuma wanda ya kashe wani mumini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta, kuma Allah Ya yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azãba mai girma...

    " Waziri ne yace kada na katseki queen najlat Amma shi wannan bawan ai da bada sanin sa ya aikata ba....

     " Kamar yadda kukasani  kashe rai babban zunubi ne, kuma musulunci ya hana mutum ya kashe kansa ballantana ya kashe waninsa ! Duk wanda yayi kisa bisa kuskure to zai biyan diyya ga ma'abota jini, bayan nan sai tsakaninsa da Ubangiji wanda zai yi dayan abu biyu: Yanta baiwa mumina ko azumin wata biyu a jere... 

   " 'Yan fadane sukace Allahu akbar wannan itace sakamakon wanda yayi kisa da gangan zai 'yanta baiwa kokuma yayi azumin wata biyu ajere...

    " Sarki khaleel yace queen najlat ce wacce ta cinye gasar nan...

    " Fita tayi mutumin da yayi kissan yace nagode sarauniya nagode dabadan kinada ilimi mai zurfi ba da tuni kasheni za'ayi....

    " Allah yakanyi yafiya akan abinda muka aikata bisa kuskure kuma kaima kaddara ce ta hau kanka kaje kabiya diyya sannan yanemi yafiyar Allah...

    " Nagode Nagode Nagode....

   Tana yin gaba zata shiga cikin fadarta tace wane bafadi yana cewa ai na bar tsofaffi a kauye ina nan inacin dadi suje susha kauyincin su...
 
   " Kai abokina bakada kirki wallahi.

    " Allah kuwa to me zasuyi min hahaha ai sai su kwafsan barsu acan cikin gidan kasa susha wahalarsu...

    " Queen najlat ce tace subhnallahi kaga ahaka kamar mai ilimi...Anya kanada imani kuwa kasan darajar iyaye? Kasan asarar dake cikin rashin binsu? Kayi tunani yayana wasu ma neman iyayen sukeyi amma sunyi nisa dasu wato Allah ya karbi ransu, lokacin dakana karami idan taga mota mai kyau hakura takeyi kai tasaka ka, lokacin da kana karami idan tasamu kaza hana kanta ci takeyi domin kai kasamu...queen najlat ce ta goge hawayen fuskar ta tace kasani kuma Kauyanci shi ne ka yi kudi da babbar riga ko fankaceciyar mota ko dankareren gida a birni alhalin iyayyenka na kauye suna cin bushashiyar gurasa......

     " jikinsa ne yayi sanyi yace nagode ranki ya dade inshaa Allahu zangyara nakuma yadda da maganar da ake cewa zama da mai ilimi da mai tsoron Allah da mai ibada zai kara maka tsoron Allah....

    " Murmushi tace naji dadin fahimta ta dakayi Allah yasa mugyara...

   
Queen bilkisu ke zaune kusa da sarki tace ina dauke da ciki wata biyu Sarki khaleel ne ya rungume queen bilkisu tare da sumbatar ta ta ko ina....

    " murmushi tayi tace inasonka mijina kuma kakusa zama baba...

     " banida Abunda zance miki matatah kuma zan baki kyauta ta daban sannan yayi murmushi gaba daya ranar kula yakeyi da ita, ita kuma sai nannarke masa takeyi...

Queen najlat ke mamakin yadda yau kwata kwata sarki khaleel bai shigo cikin dakinta ba...ruma ce tashigo ranki yadade queen bilkisu tana dauke da juna biyu...

    Cikin fara'a ta miki danAllah kai naji dadi bari naje na bata kyautar ta, cikib girmama tashiga fadarta fuskar ta cike da faraa tace ina tayaki murna Allah yasa 'Yan biyu ne ga wannan fidar a ajiye musu...

    " Queen bilkisu dake takama da isa tace fida kuma?

    " queen najlat ce tace itace abunda jariri yake bukata da wuri domin soyayyar da nake musu sannan ta bar dak'in...

     Queen bilkisu ta dinga nuna wa sarki kyaututtukan da aka bata da tazo kan najlat wane dadi yaji da kuma kara sonta...
h
     Fatuwa ke faman zirga zirga adakinta ko kinada labari jakadiya??

    " labarin me?

" Queen bilkisu ke dauki da juna biyu wata biyu tayaya zamu zubar dashi???

     " haha ai ranki shi dade abuni mai sauki ga wannan gidan jakar koreni ki zuba maganin bokan kije kibawa queen bilkisu kice turareni aciki koyaya ta shaka cikin ya zube....

    " Jakadiya uwar ganganba abiki ki halakar akyaleki mutum ya halaka ina godiya yanzu kuwa zanyi abunda kikace, wannan jakar gurin danbuja nasiyota kuma yariga ya bar garin....

Ruma ce tazo kusa da najlat ta zauna tace naso aci keki ke da cikin nan...

    " Hmm ba abunda ki damuna kamar maganar mahaifina cewa yana jiran jikokinsa....

    " Kema kin kusa kada ki damu sarauniya...

     " Murmushi tayi sannan tace yau kwanan sarki 5 ko likoni baiyiba kinga halin namijin ko matarsa nada ciki ya tare akusa da'ita...

    " Koma menene ai kece sili lokacin da yake shigowa ai korarsa naga kikeyi...

    " Hmm kawai tace sannan ta bar palour din...

   Fatuwa ce tayi sallama acikin dak'in queen bilkisu cikin kissa tace sunnu mum twins ga kyautata turare ne nasan zaiyi miki amfani...

   " Kai Amma nagode fatuwa irin wannan kyauta haka?

    " ke dai ki bude tukunna kafin ki gode mani...

     " Shaka tayi sannan ta sulale akasa sumammiya...

   Fatuwa kuwa babu inda ta nufa sai dakin queen najlat nan ta tarar babu kowa aciki tana shiga ta ajiye mata jakar maganin akan kujerarta....

     " Queen bilkisu kuwa jini ne ya tsinke mata kota ina hankalin ta ya tashi nan likita tazo sai dataga dubata ta kalle sarki kayi hakuri cikin jikinta ys bare....

    " Wane kuka queen bilkisu tasaka sarki khaleel ma sai da ya tausaya mata rungumeta yayi yanata bata hakuri amma ina duk hankalinta yafita...

     " Menene sanadiyar barewar cikin dr???

   " Akwai wane ganye mai kanshi indai mace ta sha'ki shi to zaiyi wuya bata samu matsala ajikinta ba ko cikinta...

    " Cikin jan ido yace wanene yabaki turaren...

    " Queen bilkisu ce tace nidai nashaka Amma bamsan wanene ya bani ba....uhmmn Natuna abun koreni cikinsa akwai kamshi.....

     " Duk wanda ya barar miki da ciki sai na hukuntashi daidai da abunda yayi....

       " cikin kuka tace dole a hukunta kowanene kokuma nakashi shi....

   Fatuwa ce tayi dariya tare da fadin yau najlat zata bar gidan nan....

     " Kice kinhada mata gamji?

     " Ah ai kwado nayi musu nabata tashaka nakai dakin kishiyarta....

     " Hahaha shikenan mungama da kananan kwari...

    Queen Najlat anzubar wa da queen bilkisu ciki...

    " what? what ??what??? Wane mugun ne mara imani?

     " baa san kowacece ba yanzu sarki ki bincike wai maganin acikin koren abu ....

    " To Allah ya bayyana muguwar da ta aikata abunnan...

     " Sarki khaleel ne yayi sallama ya shigo najlat saboda haushisa yau kwana7 ko likota baiyi ba yasa bata kula shi ba....

    " Najlat meke damunki?

    " Dan Allah kakyaleni kada kasamin ciwo kace nabaka kulawa yanzu ta haka zan baka? baka damu dani ba?

    " haba najlat kizama mai adalci mana kullum nazo gurin ki bakyajin kunyar cimun mutunci ki duba kiga magajina nake ta jira tsawon shekara amma anzo anbarar mata da cikin...

     " Kawai wane koren abu ta hango akan kujerar ta tace kaga wannan abun kalarsa mai kyau ko?

    " Tsayawa yayi yana tunanin maganar queen bilkisu datace masa koreni cikin sa mai kamshi baisan lokacin da ya fuzga ba ya wanka mata mari tsanar da kikeyi min har ta kai kikashemin d'a....

    " d'a kuma ni ni sai tasa kuka yaza'ayi  nakashe maka d'a?

    " Lallai najlat kin tabbatar min bakyasona bakya son farin cikin wannan shine abunda kika shakawa queen bilkisu tayi bare...har da dakkowa ki nunamin domin nagani to na yarda na yarda najla nayarda bakyasona sai hawaye....idonsa ne yayi ja yakara turata jikin bango kigayamin me isa kika zubar mata da ciki....

    " Innalillahi kawai take ambata bani bace ba wallahi ka yarda dani...

   " tayaya kigayamin ya daka mata tsawa wallahi in baki sanar dani dalilin zubar mata da ciki ba sai na hukunta ki sai kuma...

   Wallahi...anan ta sulale kasa....

    _Assalamu Alaikum_

_Kuyi hakuri da rashin typing akan lokaci.._

  *Wannan shi ake kira k'wado...Allah kadai ke fitar dakai...*

   KO YAYA NAJLAT ZATAYI?

   KO SARKI KHALEEL NASANAR DA QUEEN BILKISU???

   SARKI KHALEEL NAYARDA DA BA NAJLAT CE TA BARAR DA CIKIN BA??

    *Godiya da jinjinan ban girma zuwa ga Masu turomin da sakonni da addu'oi...banda bakin godiya sai dai Allah yasaka muku da  alheri*Ameen...

    _*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku...you really made my day and also make me smile and happy when ever I read your comment's..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....as i couldn't get enough time to reread some page and make correction #TEAM SGN..*

   GOD BLESS YOU OLL...

******
    _Barin sallah_

*Allah SWT yana fad'a cikin suratu Maryam (59-60) cewa:Sai wad'ansu 'yan bãya suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su had'u da wani sharri () Fãce wanda ya tuba, kuma ya yi Imãni, kuma ya aikata aiki na qwarai...*

_Abdullahi d'an Abbas RA yace game da wad'annan ãyoyi:Abin da ake nufi sun tõzartar da ita; ba shi ne sun daina yinta bãki d'aya ba, Aa sun daina yinta akan lõkacinta ...._

*Sa'ed d'an Musayyib shugaban Tãbi'ai AH yana cewa: Abin nufi shi ne mutum yaqi sallar azahar har sai la'asar ta zo, kuma bã zaiyi la'asar ba har sai magriba ta zo, haka ma magriba sai ishã'i, ita kuma ishã'i sai asuba, ita kuma asuba sai rãna ta fito; duk wanda ya mutu a irin wannan yanayi kuma bai tuba ba; to Allah ya yi masa alqawarin azãba/uquba da wani sharri !!!*..

_Yan'uwa kusani barin sallah akan lõkaci yana daga manyan zunubai wanda idan bãwa bai yiwa kansa karatun ta nutsuba to akwai tsõratarwa ga wata irin azãba ta sharri, ya kamata mu qara kula da sallah ya 'yan uwa musulmi!_

    Allah yasa mudace...Ameen

   Urs *Nana diso*

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[8/11, 11:24 PM] Kubrieh Cie Bervier✨: _60-63_

    *SO*
        *GARWASHI*
                        *NE*

_NA NANA DISO_

      http://nanadisoo.blogspot.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

  Tana sulale wa yayi saurin rik'eta cik'in sanyin murna da Nuna k'ulawa yake k'allon manyan idanu wanta da suk'a tafi dashi, Ga damuwa a  fuskarshi Amma K'allo fusk'arsa Na kokarin fitar da damuwar, jik'insa a sanyayi ya ajiyeta nan ya sanar da fadawa k'ada wanda ya shiga fadarta...

    " Ruma ce tafi tare da lik'ita Nan ta duddubata sannan tayi mata allura ba'afi minti talatin ba tafarka idanuwanta cike da hawaye cikin tak'aici tace ta yaya zan k'ashe masa d'a....

    " Likita ce tace ranki yadade k'ina bukatar hutu dan haka k'i k'wanta k'i huta...

    " Directly ta Nufi fadar sarki k'haleel dake rik'i da sandar girma yana magana da fadawa can aka bawa lik'ita izinin shigowa daga Nan ya d'agawa fadawa hannu cik'in isa irin ta sarakai yace meke damunta likita...

    " Ranka shi dade matark'a tanada damuwa which is not small, ya kamata kana lura da'ita saboda yanayin damuwarta zata iya barar da cikinta Nan gaba idan ta samu...

   " Cikin hanzari ya dago kai zuciyar shi cike da bakin cikin barewar cikin queen bilkisu yace shikenan za'a kula da'ita...

    " Yes! Nasan kana cikin damuwa kuma zuciyarka zatana raya maka abubuwa da dama dangane da sanadiyar barewar cikin queen but yakamata kayi hakuri please komai dakake gani kaddarane mai hankali ke hakuri daga karshe yaci riba....

   " Tabbas...

" Kuma is good k'a daina tunanin wanda ya b'arar da cik'in queen k'asa aranta daga Allah ne....ina fata maganata batayi tsauri ba?

     " Alamun godiya yayi mata sannan yace zai za'akula...

    Waziri ne ya shigo fadar cik'in kasa da murya yace ranka shi dade Naji bayanin ka Amma bana tunanin queen Najlat ce zata zubar sai dai idan sharri sukayi mata...

     " Wa zaiyi mata sharri waziri kasan dama bama shiri kuma ita da kanta ta tabbatar min da itace...

     " Ranka shi dade kasan Duk wanda yake saurin amsa tambaya, lalle ne sai ya yi kuskuren bada amsa, kuma queen najlat ko ada ban tunanin ta da mugun hali ballantana yanzu yana da k'yau ka rufe maganar....

     " Tabbas haka za'ayi Allah yakawo min 'ya'ya goma lokaci guda....

    " Fiye da hakama ranka shi dade, Ai fata Nagari lamiri...

Jak'adiya ke faman dariya ranki shi dade k'inje kin hada gwarma fa queen bilkisu tana can tana bala'in kama wanda ya zubar mata da cik'i.....

     " Fatuwa ce tayi dariya tace hank'ali na bazai k'wanta ba har sai naga sunfita a masarautar Nan inaso k'ije k'i aik'a kice queen najlat tana neman queen bilkisu ta hakane zataga jakar daga Nan rigima ta kaure...

    " Kai ranki shi dade haka Tara inji kishiyar mai magijiwa...

    " Haha Ai bala'i bama su fara ganinsa ba sai sunfara tone tone....

   
     Queen Najlat ke faman hawaye cikin mayafinta tace Ruma yaya zanyi da wannan maganar idan kowa yaji? Bama ace queen bilkisu....

    " Ranki shi dade kin taba ganin rana tafasa rufin kwano?

     " A'a sai dai yadau zafi....

   " To haka mai gaskiya yake komai karyar mutum baya fasa gaskiya....

    " Amma ruma da wani idon zankalli sarki bayan yayi fushi dani???

     " Wallahi inkina wata maganar mamaki kike ban kefa da ilimin ki ba jahila bace ba jahilai ma suke makirci ballantana ke *Mai gaskiya*??? Kuma banda abunki Ai sharri sak'oni ko yatafi zai dawo....

    " hmmm ruma yafa riga yaganni da jakar ahannuna kinga babu ta inda zanfita...

      " Wannan abun na tabbatar ajiye miki akayi domin akala miki sharri kuma duk kalar data canja tuwo ai tuwo yake sunansa bazai canja ba, Yanzu ne time din da zakibi da soyayyar da yak'eyi mik'i k'i k'ara siyi zuciyarsa....
 
   " Murmushi Najlat tayi tace Hik'ima k'ashen k'wance in bak'a iyaba sai k'a dameta...

    " Ruma ce tace gwara dai ki farfado ai Hutseyar rakumi tayi nisa da k'asa...

     " Nagode da shawarwarin dakike bani Allah yabarmu tare....

     " Murmushi tayi tace badamuwa bari naje nakarasa girki...

Queen bilkisu ke faman mita nagama baka damu dani ba naga baka damu da matsalata ba ka duba kaga how many years nake bukatar haihuwa Amma bansamu ba yanzu ansamu anzubar min kakasa daukar mataki?

    " Murmushi yayi yace ai afuska ma akan gane damuwa, Nasan kina cikin damuwa Amma Nakasa gane wanda ya zubarmiki ko kinaso Na baza malamai ne afara shirka....

     " To in kai bakayi ba ni zan gayawa mahaifina sai ya baza mana wallahi tunda shi yadamu dani....

     " Wai meke damunki bilkisu kina iya maganarki fa...

   " Is okay please tunda baka damu daniba...

     " Shiru yayi yana k'allonta sai mita takeyi Ahaka yafita yabar mata gurin...

    " Queen najlat ke zaune tana cin tufa sallamar sarki taji hakan yasa ta gyara  zama tace Kayi hakuri...

   " Kallonta yayi yace hakurin me kuma?

     " Hakurin komai mana, Allah bani Nabarar mata da ciki ba kuma bansan wa yakawomin jakar nan ba....

    " Cikin wani yanayi yace Amma wanda yace ya tsaneka kina tunanin akwai abunda bazai iya yimaka ba???....

     " Cikin sanyin murya tace shi zato ai zunubi ne wata maganar ak'an fad'ita k'awai dan aji dadi acikin zuciya amma bahaka take ba, kuma bazaka iya aikatawa ba....

     " Toh yayi kyau, Banajin dadine...

     " sannu kokana bukatar wani abun ne?

    " Yunwa dai Nakeji ko zaki dafamin abinci....

    " cikin rashin damuwa tace to kitchen ta shiga dama ita tasaba dan bata yarda taci abincin kowa agidan sai dai ta girka...

   " Cikin shaukin kaunarta ta k'wanta baisan lokacin da bacci ya kwashe shi ba....

    " Tana fitowa dauke da plate ta ajiye takawo fruit daga kanta dazatayi taga bacci yakeyi, bandaki tashiga sannan tayi wanka tayi sallah har karfi hudu yanata bacci ga meeting yakeda shi karfi 4 Sai hudu da rabi ya farka tana zaune tana karanta novel...

    " Salati yayi sannan yaci ya mik'e cikin fara'a yace karfe nawa uku tayi...

    " cikin rashin sakin fuska tace karfi 4 da rabi...

    " 4 kuma tayaya me'isa baki tashi ne ba kinsan karfi nawa ina zanyu meeting kuwa ko sallah...inna Lillahi..

    " Naga bacci kakeyi tayaya zan tashika wai tayaya?

    " Ne ba mijink'i bani ba? K'o k'uma haramun ne k'i tabani? Tabbas najlat k'infara k'aini bango... wallahi dan k'inga inasonk'i shine zak'i yimin abubuwan da basu dace ba sallar ma bazaki tashi ne ba, wai in baki soni ba wa zaki so? Ne ne mijink'i kuma bazan taba rabuwa dak'e ba....

   " K'ayi hakuri cewar queen najlat...

    " wane irin hak'uri zak'i bani? wai ya k'ikeso nayi da soyayyar k'i?? naga Allah ma munayi masa lefi ya yafe mana Amma? Nayo kamuwa da sonk'i acikin zuciya!... k'i aminci dani k'ada na zauci, najlat dukkan namiji bayada kwanciyar hankali sai da kulawar matar sa....

    " Queen najlat ce tace Amma kasan dai....

    " D'uk abunda zak'i fada bazai gamsar dani ba, duk matar garinnan kece gimbiyata, ki kudurci aranki sam bazan barki ba, kukan zuci nasan bazai barni ba, inna rasaki kinsani bazan rayuwa ba!...in na rayuwa ruyuwa ba bazai yitaba...Akwai kalubale ga wanda keson wanda bai sonsa fa...kin zama garkuwa jikina k'uma sayi ba...inna ganki sai k'i dinga yimun kwarjina...

    " Kalamansa gaba daya suka kashe mata jiki cikin sabulewar jiki tace abincin Naka fa?

    " k'i cinye banaci k'ije k'i cinye yayi fitarsa har cikin harta sai data tausaya masa haka yasa ta miki ta huce bangaren queen bilkisu flask ta ajiye agabanta...

    " wannan flask dinfa queen Najlat?

     " Cikin murmushi tace queen bilkisu kenan Naga kwana biyu bakyajin dadi shine nace bari na dafamiki keda sarki sai kuci....

    " Me isa bazaki bawa sarkin dakanki ba....

    " Ina ai kullum zancen girkin ki yakeyi min, kuma nasan yunwa yakeji tunda ne yakicin nawa...

    " Queen bilkisu ce tace to mungode asauka lafiya duk da bakiyimin takaicin abunda yafaru dani ba...

   " Queen najlat ce tace Kudi ba su da amfani sai an kashe su, Idan an kashe su kuma ba za su dawo ba, sai dai a sake nemo wasu, karki damu 'yan hudu suna tafi tayi dariya ta fita...

   " Queen bilkisu ce tasaka dariya ai dole kibini karfi 5 sarki khaleel yashigo ta zubamasa yace can yace girkin ki kamar na najlat yau yayi dadi...

   " Allah ko ai naga yau ranka yabaci shiyasa Na tsara maka abunda zai faranta maka...

    " Rungumeta yayi sannan yasa dariyar data bayyana hakorin mak'ansa..

Jak'adiya ce tace fatuwa boka na bukatar rigar sarki da'ita zaayi masa asirin da zai saki matan nasa tayaya zaki dakko?

    " Fatuwa ce tace abu mai kamar wuya kuma babu wuya kada ki damu zan yaudari queen bilkisu na dakko a d'ak'inta...

    " Nan da sati biyu ake bukata ya kamata ki gaggauta kawowa....

   " Karki damu jakadiya kamar ansamu ne...

   Queen najlat ce ta shirya cikin hijjabinta ta dafa kaza tasa aflask ta huce gidan ummi tana shiga taga queen bilkisu da gimbiya sumayya da gimbiya Amal...

    " Ummi ina kwana yajiki jiki?

    " lpylou ya jikin naki yace min bakya jindadi?

    " Lah bafa wata cuta baciba ciwon kaine har na warware...

    " Queen bilkisu ce ta harareta uhm ummi dawa sarki zaiyi tafiya ne?

     " Baisar dani ba bilkisu sai dai in yasanar....

     " Queen Najlat ce tace Amal bakida kirki wallahi ko kishigo masarauta...

    " Kinjiki ne ai baki taba zuwa gidaba ke bama haka ba ban sanar da mijina zan shigo gurin ki ba...

    " Uhm masu miji inji najlat lallai nan da nan har sai ansar dashi?

    " Ai wannan hakkinsa ne, Bazanyi abunda zan bakantawa mijina ba....

    " gimbiya sumayya ce tace nema abban sajida ko dadewa nayi aguri kyaji fada...

    " Ummi ce tace ai wanda ke kuntatawa mijinsa yayi asara, kuga matan yanzu suyita kuntatawa mazaje suna wahalar dasu sai kuma ance aljannah suce amen..

   " Queen bilkisu ce tace wallahi kam ummi ko kunya basaji mutum ko ya girmi maka baka yimasa rashin kunya ba shiyasa kullum nake kara godewa Allah da yabani miji mai mutukar sona...

    " Queen najlat ce taji wani iri kamar da'ita suke...

    " Hmm inji gimbiya amal ne abun mamaki yake ban wai kiga yarinya ta aure mutum wai daga baya tazo tana ta tsaneshi? Wane tsana kunzama daya...

    " Queen najlat ce ta daure tace aikam ba'a kyauta wa...

Queen Najlat dai duk ta shiga wani yanayi maganganun su kitchen ta shiga tana fitowa husaina ta shigo suka gaisa tace kinganni sai yanzu ko queen...

    " eh inata sanya ido gimbiya husaina...

     " Wallahi na shishigo kina kitchen kina burgeni yadda kike dafawa sarki abinci da kanki..
  
     " Hmm ai nariga na saba shiyasa wallahi...

    " Amma me isa kika iya girki kika damu da kiyiwa sarki da kanki??

    " gimbiya kenan labarin yanada d'an tsawo...

     " Amma zanso ki dan bani labari Dan Allah...

    " Husaina kenan mumy kakatace tayi aure bayan tagama phd dinta sanadiyar karatun da sukeyi agidansu...ta aure kakana lokacin yana likita aduniya babu abunda yakeso sama da abinci mutum ne mai son kulawa mumy babu abunda bata iya ba sai girki tunda sukayi aure take samun matsala a aurenta akwai lokacin da zaizo yayi mata habaici saboda yace mata bata cika mace ba, ita kuma agidansu anriga an sangarta su kwatakwata basa shiga kitchen, mamata taban labari mumy bata shiga tashin hankali ba sau da yace ko taji akoya mata ko kuma su rabu hakan ba karamin tayar mata da hankali yayi ba yadda ya nuna mata da gaske yake, bashiri mahaifiyar ta ta fitar da kudi dubu dari domin 'yarta tazauna lafiya agidan mijinta...

    " Husaina ce duk jikinta yayi sanyi tace to me mahaifinta yace?

    " Haka yace laifin iyaye mata ne da basa jan 'yayansu ajiki suna koya musu yadda zasu shiga kitchen, domin ta'iya girki yaya akesu miyar kubewa kuka su pizza su soya nama, domin yana taka mutukar rawa arayuwar 'ya mace har yabada labarin abokin sa da yayi aure ya siyo semovita yace ayi tuwo ta kwara masa ruwan sarki ta kaimasa shi ba kunu ba shi ba koko ba daga karshe mahaifin nata shi yace asaketa kinga wagari ya waya?

     " Tabbas da matsala to queen bayan an koya mata ta koma gidanta?

    " eh ta koma amma sunkara samun matsala watarana yak'awo alk'ama yace ayi masa tuwan alk'ama tace bata'iya ba yace zata'iya k'omawa gida akoya mata, lok'acin data k'oma gida mahaifinta ya cewa mahaifiyar ta ita zata zage ta k'oya mata komai da komai cikin ikon Allah kuma zamansu yafara dadi mahaifiyata sai data koye girk'i k'ala kala gurin gyatu marta kafin tama gama secondary...k'e nima ina dawowa daga mak'aranta mameta take cewa na dafa abinci duk da ni 'yar sarki ce amma sai da na bambanta da sauran mata....

     " k'ai amma naji dadin wannan bayani naki nima zan dage sosai kuma laifin matan ne ba mazan ba domin k'ulawa rabi tana hannun mata, Amma kuma queen wasu k'almomi ne mahaifiyar k'i ta sanar dake kuma ta haka k'ika zama k'wararriyar chef?

      " Mamee tak'an gayamin K'omai yana buk'atar k'wadawa indai k'ana gwadawa to zakayi nasara ak'o da yaushe, Amma indai k'ace bazak'a dinga gwadawa ba to k'omai ka k'oya zai tafi a iska,Shi girki sarrafawa ne ba kayyan hadi ba wata sai ta k'ashe masa dubu 1000 k'e sai ki kashe dubu biyu kuma nak'i yafi dadi, sarrafa abinci shine sai kuma kayan hade,K'uma dagewa tanada mutukar amfani indai k'adage da gwadawa to inshaa Allahu sai k'azama k'wararre gurin sarrafa abubuwa sai tak'aima Kai kake tsara nak'a, K'uma k'o da k'in girka wane abun idan bayyi dadi ba kada k'iji haushi k'ici k'in hak'ura...wannan shine ma lok'acin koyan girk'i ma alok'acin ya k'ama kitsaya ki lura k'i k'uma k'ula wane abune yayi kadan menene yayi yawa me zaki gyara me zaki rage!!! wannan shine sirrin k'oyan  girk'i hak'uri da k'uma jajerciwa....hak'an tak'an cemin ako yaushe...

   " Amma Nagode 'yar uwa yanzu ne lokacin da zan fada kitchen Allah yakawo miki 'Yan hudu....

     " Murmushi tayi tace babu komai gimbiya...

Da daddare queen Najlat tana kwance tunanin sarki khaleel kawai takeyi cik'in mintuna taji sakkon gobe da safe da'ita zasuje kauye zaayi kwana biyu....

   Da sassafe sarki da fadawa suka shirya queen bilkisu tayi bak'in ciki sosai da sosai yadda sarki khaleel yace da queen najlat zasuje, haka aka shirya motoci suka dauki hanya driver ne yaja sarki khaleel da queen najlat tunda suka shiga mota babu wanda ya k'ula wani fadawa na biye dasu wasu amota wasu a doki, tunda suka fara tafiya sanyi yafara damun queen najlat dan garin sanyi tarasa yadda zatayi gashi bacci tak'eyi cikin damuwa tace sanyi nakeji please...

    " Uffan baice mata ba...

    " Hannayenta guda biyu tasa ajikinsa sanyi nakeji...

     " Cikin bacin rai yace ai gajikina sai ki lulluba...

     " Batasan lokacin da ta rirrik'i shi ba har suka isa garin suna shiga sarkin kauyen da mutanen sa sukayi musu sannu da zuwa cikin girmama wa ta gaidasu suna shiga masaukin su wane gadone da mutum daya kadai zai isa zama tayi agefansa shi kuma yafita dezza ce tashigo tace sannu sarauniyar birni...

    " Cikin murmushi queen najlat tace ke kuma sarauniyar kauye? Da fatan mun sameki lafiya?

    " Lpylou kalou kuka samemu Amma nayi mamakin kece najlat...

     " saboda me?

" Yadda nakejin ki ba haka naganki ba nayi tunanin zanganki da kwalliya da kunshi mu mutannen kauye ma mukeyi ballantana ku mazajen ku Na burni...

    " Kinfiya zolaya wallahi...

    " Allah kuwa bakiga yadda nake lallaba sarki na ba Amma kada nacika ki da surutu bari akawo miki abinci kici sai ki kwanta....

    " Tohm nagode, Abincin nasu shinkafa da salad sai markadaddiyar aya da rake sai kuma zuma haka tace su sannan tayi sallar isha'i...tunda tagama tsigar jikinta ke faman tashi wata irin sha'awa ke dawainiya da'ita haka dai ta dinga babbasar wa....

    " Lokacin da sarki khaleel ya shigo tana zaune kam tabarma yace mikomin lemon nan...

    " Sauri tayi tace aa kace shinkafar...

     " Saboda me?

" Uhm uhm uhm babu dadi ne banaso ka bata bak'inka ai...

      " Murmushi yayi yagani abunda take nufi, to sai kizo ki kwanta agadon...

    " Wannan gadon karami ne namutum dayane kuma sarki ne nakwana nan kasa...

     " Da k'in barni a k'asan ke sai ki kwanta anan din kinga....

     " cikin shagwaba tace a'a nak'i wayon sai da safe...

     " Amma fa kasace kina gani kada...

     " Nifa bana tsoron komai...

    " Kasa bacci yayi yanata kallonta dama ace akusa dashi ta kwanta...

    " Wayooo Allah na tasa kuka miciji miciji tayi saurin d'anewa gado ...

    " Azabure yamiki miciji kuma?

      " Eh tanuna saman kirjinta tana kuka tace Anan ya cijeni yana kokari ciremata mayafi...

     " Ta Ruk'un k'umeshi ne karka tabani zafi...

    " Dariya yasaka ba miciji bani ba sai dai cinnaka fa... muga yadda ya cije ki..

    " Ni dai karka tabani takara fashewa da kuka...

    " To aini duk k'in rik'ine...

    " k'ara rungumeshi tayi tace ni ka kyaleni wa zan ruke in bakai ba?

    " Ashi dai kina sona??

    " Shiru tayi bataci komai ahaka bacci ya kwashe shi ko yaya yayi kokarin ganin inda cinnakan ya cijeta sai ta rungumeshi haka sukayi bacci rabin hankalinshi atashe...

     Da sassafe suka shirys tawowa dezza ce tace najlatu kina matsawa kusa da mijinki kidaina nisa da shi ga kumbar mata inkinje kyata ci sai nazo suna...

    " Sarki khaleel duk yanajin su yajiyo yayiwa dezza godiya suka kama hanya...

    " Saboda me kayiwa dezza godiya?

    " Saboda tana bawa matata shawarah ta gari...

     " Hmmm haka suka koma masarautar fablita kowa sai maraba yakeyi musu directly jakadiya tagani a bangaren queen bilkisu sun dauki rigar mai martaba fatuwa tana cewa wannan ce rigar da zaki kaiwa boka kinji...

     " Angama ranki shi dade.....

    " Hakalin najlat bai tashi ba sai dataga fatuwa suna hira da sarki tace ita kuwa mai take nufi dashi asiri?

     " Ruma ce tace yakamata kije ki lik'a kiji yadda mai martaba ya sauka...

     " queen najlat ce tace sai kace wane yaro?

    " Agurinki ai jaririne....

     " Ummi taje suka fara gaisawa sannan tabiya shashensa ya fito daga wanka kenan yana kokarin saka kaya tana shiga ta ganshi zaisa kayan da futuwa ta dauka sauri tayi tace kada kasa...

   " cikin mamaki yajiyo yana kallonta yace wannan rigar fatuwa ce tabani akanme zanki sakawa?

    " murmushi tayi tace aiko bak'a fada ba nasan goro yanasa amai...

    " Kamar yaya???

   " Tunani ta shiga yanzu wacce dabara zatayi masa can kuma Rigar ta kwace tayi saurin jifarwa sannan tafara sumbatar sa.....

_Assalamu alaikum!!!_

_*ALLAH MUNGODE ABUNDA KAYI MANA MUNGODE ABUNDA KAKE MANA MUN GODE ABUNDA ZAKAYI MANA MUNGODE....*_

     *Ina gaisuwa gareku tare da baku hakurin shiruna da kukaji Allah yasaka da alkhairi  Ina kuma baku hakuri na shiga wane dan uzuri ne....*

    _Onelurv oll.... I oll read your comment's which make me happy ...soyayyar ku ga wannan littafi is very important and precious agareni..._

    *I requested all of you to avoid all the grammatical and spelling errors..*

_Menene ra'ayin ku dangani da wannan shafin...please all my reader's should try and comments akan littafin nan...In naga comments da yawa gobe zanyi 2 page da yardar Allah....onelurv_

   *Please do vote comments and like your vote and comments give me more courage to continue writing my story...and your comments help me to write better...#TEAM...SGN.....SGN LOVERS...*

   

   _Allah SWT yana fad'a cikin suratul Muddatthir (42-48) cewa:.."Su ce musu" "Me ya shigar da ku a cikin Saqar?" () Suka ce, "Ba mu kasance munã a cikin mãsu sallah ba. () "Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba. () "Kuma mun kasance muna kutsãwa tãre da mãsu kutsãwa, () "Mun kasance munã qaryata ranar sakamako..."Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana"...Sabõda haka ceton mãsu ceto bã zai amfãne su ba..._

   *Kuma ya zo a hadisi cewa: Alqawarin da ke tsakãninmu da tsakãninsu ita ce sallah, duk wanda ya barta, to, ya kãfirta..Imam Tirmizi.*

_A wani hadisin kuma cewa:  Lalle -banbanci- tsakãnin mutum da tsakãnin shirka da kãfirci; shi ne barin sallah..Muslim_

   _*Wato dai sallah tana da babban matsayi a addini, don haka ma ita za a fara dubawã cikin ayyukanmu a rãnar alqiyama.*_

  _*Sannan sallah ce ibãdar da ke nuna ban-bancin musulmi da kãfiri, shi yasa malamai da yawa suka tafi akan cewa duk wanda baya sallah to kãfiri ne.*_

   _Allah katsare mana imanin mu_

   Urs *Nana diso*

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

No comments:

Post a Comment