Wednesday, 8 March 2017

AN GAISHEKU MUTANEN KIRKI 1-END

[2/20, 2:58 AM] ✨kubrieh cier vervier: _1-20_

*MUTANEN KIRKI AN GAISHEKU*

  (HAKURI DAI SHINE....)

   _NANA DISO_

      WATA 'YAR TUNASARWA CE👌🏼👌🏼

*Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu*👏🏼

   *Dukkan godiya ta  tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halitta Annabi Muhammad da iyalan sa da sahabban sa baki daya*.....

🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻🚶🏻

Babban bala'in ma matan Aure masu safarar zuwa gurin malami  🚶🏻kaiconki kaiconki kaiconki abun takaice ma wai akan ta mallaki mijin tazama itace tauraruwa itace mowa👉🏼 wai akan da namiji akan dan adam da daga kasa yake kuma cikinta zai koma har kuna haukatar da kishiyoyin ku ko yayan gidan kokuma ku sa ayimusu mugun asiri wai duk dan karsuyi nasara arayuwar su..wai akan da namijin da ko kemutu ki barsa ko ya mutu ya barki😡 ki gama kashe kudinki dayin shirka da tozarta bayin Allah kokuma yakasance wanda kikeyi dashi din ba kabarinku daya ba😂 kunje wane tashin hankalin....Ta manta da duhun kabari da macicizai?????

😭😭😭😭😭😭😭

Abun yazama ruwan dare kaga mutum yatafi gurin wane mutum da sunan malami Wai yanada matsalar kaza Abu kaza ya dameshi Sai kaje yace Abun cikomin halin danake ciki😭 ko kun manta da hadisin fiyayyen halitta Abu Huraira Allah ya kara masa yarda daga Annabi s.a.w ya ce “wanda ya je wajen dan duba ya gasgata ya shi cikin abin da ya fada ya kafircewa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad s.a.w” Abu Dawud ya ruwaito a hadisi mai lamba 3904 A wani hadisin kuma da Imam Muslim ya fitar a hadisi mai lamba 2240 Manzon Allah s.a.w ya ce“ wanda ya je wajen dan duba ya tambayi wani abu kuma ya gasgata shi to ba za a karbi sallarsa na kwana arbai'n ba.....To wannan wacce irin asarace 😰 kaje Don abuncika Maka wane ko kaikanka kawai dan kaji mai zai faru dakai gaba🤔 to in kunje me zakuyi ko kun isa ku tsayar da abunda Allah yarubutawa wane ko yarubuta maka baka isa ka goge kaddaraba kokuma kasaka wane acikin balai face Allah ya rubuta tuntuni🤔🤔🤔 Zaman kabarin kuke mantawa kokuma zarar ran?????

😰😰😰😰😰😰😰

Abun ma babba ne fa🤔 domin sun sani sun karanta inaje har waazi sunje akan zuwa gurin boka sunje sun kuma je amma sun tauye sanin😡 bala'i ga ilimin ga rashin aiki da shi aiko jahili akace masa ya cuce wane yasan babu kyau ballantana mai ilimi kije kiyi kulombotan ki kisa miji yayiwa wata wulakanci kokuma ya kauraci mata kukoma tabar gidan...wai sai kiga ta dakko carbe wai ita mumina😂 kokuma kiga ta zauna adadduma wai tana lazimi, masu imanin ma fa kenan su sukeyin sallar wasu tsabagen shaidan yazama uwarsu da ubansu sallar ma ajiyeta akeyi saboda bokatuwar duniya🤔 Tamanta zuwa tayi kokuma dole ta barta kamar yadda taga wasu suna barinta...wai ke bunkusa ta gaban goshin mai gida kiyita wash shagali gali dinki ayayin da Allah ya damkeki tun aduniyar zakisan ashe dai zalunci babu kyau, kin sakankanci kije mala'ikan mutuwa yazo tafiya daki to yau ina alhajin da kikeyi danshi?😂😂 asara kan asara ga masifa ga zunubi ga kuma danasani....Ta manta da Azabar kabari da tambayar kabarin...????

😔😔😔😔😔😔😔

Wa'iyazubillah👉🏼 kaje ta zauna gaban malam ai waccan yar mijina ce ko dansani so nakeyi katoshi kofar nasarar su karufe samunsu nafiso nagansu awulakanci.... (kaje jahila ta manta Allah kiyin komai)🤔 komai isarki komai tukawonki baki isa kiyiwa wane abunda zaki wulakanta rayuwarsa ba! Ke waya wulakanta ki? Kokuma Allah ya wulakanta ki?...😂😂😂 sai ma kaganta tana dariya mai gida ai kasa yace to ai kaza zaayi yace to zanje can yace to zan dauki wancan yace to...ta mai dashi huhulawooo tazama mijin ma😔 Yana zaune jabar wai shi alallai mijin sahiba😂😂😂 ko danka Ne komai yace maka eh komai yace to kyaje tace tace Dan iska so kakeyi kazama rago😂 Amma kuma mijinta tasashi a cikin wani halin ,🤔 ko kunmanta kasamu mai kwabarka ma wane abunne kaji yace ina zakije, bazakiba, kudi kaza nakeso sunyi yawa shine soyayya...❤ Amma kince mai gida bani dubu goma ya bude baki yasaki lebe ya zura hannu a aljihu 😬😬 takaice kan takaice mijinka kazamar dashi dolo ayayin da Allah yafara saka masa kokuma yasaka musu karkiso kiga yadda rayuwarki zata kasance...????

     MU HADU AKASHE NA GABA....

*Urs Nana diso*

nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[2/20, 3:05 AM] ✨kubrieh cier vervier: _20-30_

*MUTANEN KIRKI AN GAISHEKU*

  (HAKURI DAI SHINE....)

   _NANA DISO_

      WATA 'YAR TUNASARWA CE👌🏼👌🏼


🚶🏿‍♀🚶🏿‍♀🚶🏿‍♀🚶🏿‍♀🚶🏿‍♀

Wallahi kuje tsoron ranar alkiyama ranar sakamako ranar da kowa aikinsa zai kwace sa kincuceta kinzalunci shi kin yimasa kazafi kin tozartasa amma sai kidinga murna wai ke mai boka👺 shi boka tsinanne mai binsa ma tsinanne ne mai yadda da maganarsa ma tsinanne ne mai yin aikinsa ma tsinanne ne!!!!!!! Ina mumuni ina zuwa gurinsa ina mai imani ina zuwa gurin sa komai halin dakike ciki mutum daya ne zai biya miki buka shi zai yayi miki Amma malam sai dai ya hadaki da mutane ya kuma lallata rayuwarki🤔🤔🤔 wai ko mantawa kukeyi kowa rabonsa yake ci acikin duniyar nan kowa rayuwarsa daban tayaya zaka kwafi ta wane?🤔🤔 miji yazo kin soki kishiyar ki kinzageta tun baya yarda har ya fara yarda yanzu kin hada mutum da mutum fada kin hada bala'i? Dadi kikeji? Kaje banza gabuwa wacce take munafurci wai dan namiji yasoka ohoooo zamani 🤔🤔🤔 kije tana cewa tine tine nayi waje da Shigeya,kunje gabuwa kee waje kikaye da ita in kwananki ya kare ki daukar ki zaayi ayi waje dake 😬 kozaki dawone😂😂.....kije abunda kika shukama ya isheki wallahi...Allah baya zalunci kuma bayason mai zalunci...

🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔

😰😰😰subhanallahi kin manta kin haihu abunda kikaye wa wata sai kiga itama mijin yana yimata kin manta abunda kayi sai amma ka kin manta..kin manta hatsare da azabar da ke cikin shirka bayin Allah dakuke kuntatawa kunsan tsakaninsu da Allah kunsan matsayinsu gurin Allah?🤔🤔Ita shirka tana tabbatar da mutun cikin azabar Allah har'abada, Tana sa mutun ya rasa ceton Manzan Allah -tsira da amincin Allah su
tabbata agareshi, Tana sa mutum ya yi asarar dinbin ayyukan alheri da ya yi a duniya, kamar taimakawa nakasassu, sadar da zumunci…'. Saboda haka dukkan wani aikin ibada da Allah da Manzanshi  su ka yi
umurni da ayi to mutum ya tabbatar ya yi shi ga Allah kadai kada ya hada kowa tare da Allah, Kuma idan akace Ibada ana nufin 'Gamamman suna ne
da ya tara dukkan abinda Allah ya ke so kuma ya yarda da shi, na maganganu da ayyuka na zahiri da na boye.'To kaga anan muna da nau'ukan ibada masu tarin yawa kamar, Karatun
Kur'ani, Sallah, Azumi, Salatin Annabi , Is'tigfari, Hailala, Sada
zumunci,Gaida mara lafiya, Yanka, Neman tsari, Neman Agaji, Tawakkali, Kauna, So da sauran su…, wadanda ba'a ambata ba dukkan su na Allah ne Kadai kada mutum ya kuskura ya karkatar da wani nau'i guda zuwa ga wanin
Allah, domin Allah yana cewa: “Ku bautawa Allah (Shi kadai) kada ku hada shi da komai” Suratun-
Nisa'i, aya ta 36..... kin manta da ayarne kokuma kina sane da itane🤔????

😞😞😞😞😞😞😞

😭😭😭ko kun manta? Sihiri/Asiri yana daga cikin abinda yake raba bawa da Allah cikin kankanin lokaci, mutum ya dauke dogaron shi da Allah ya sanya shi ga siddabaru ko wani mai siddabaru😭 wanda hakan zai iya kai mutum ya rasa addinnisa baki daya😰😭 innalillahi...

   Idan kana beye da tarihin musulunci ka san yadda Annabi Musa Alaihissalam ya yi fama da masihirtan zamaninsa mabiya Fir'auna, wadanda Fir'aunan ya gayyato daga ko'ina domin su kalubalanci Annabi
Musa😔😔 Wannan ya nuna lalle Matsafa sun ci karansu ba babbaka a zamanin Fir'auna, amma cikin taimakon Allah alokacin da suka ga Mu'ujizar Annabi Musa suka yi imani da shi sai suka watsar da dukkan kayan tsafe-tsafensu, ba irin barazanar da Fir'auna bai yi musu ba amma
suka ce:
١٧ :هط ﭼ ﯠﯟﯞﯝﭽ
Ma’ana: “Ka yi duk abinda zaka yi”. Suratu Taha, aya ta: 72....

👉🏼Wannan ya nuna mana tarihin matsafa dadadde ne, kuma a har yanzun nan suna nan👌🏼

  Abinda ake so daga dukkan wanda yake musulmi shi ne ya
sani Allah ya haramta tsafi/sihiri/asiri/tsubbu/bokanci/duba da dukkanin jinsin wadannan al'amurra, harma ga shi Ma'aikin Allah  ya sanya shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa,
😭Lalle Ma'aikin Allah 01
ya isar da Manzanci. yana daga ciki halayan matsafa/ masihirta asani 'Tintiran Makaryata ne'.....👉🏼 Dan Allah kina sane kokuma bacci kikeyi😰???

😇🙁☹

👉🏼👉🏼🚶🏻 Sau dayawa abinda yasa ake cewa ka tashi tsaye wai saboda magabta
da mahassada, ai ita hassada da mai rabo taki ce indai Allah yasoka da abu babu mai dakatar maka da abun kaidai ka kadaita Allah kakuyi imani dashi..👏🏼👏🏼anan nake cewa addinin musulunci baibarmu haka kara zubeba, ya tsara mana hanyoyin da ake bi don kaucema sharrin masharranta....👉🏼

😨😰😨😰😨😰

👉🏼👺Wanda zai duba abinda zai faru nan gaba, yin wannan aiki da zuwa wurin mai wannan aiki bai halatta... 😭Da bokanci da duba abubuwane masu matukar halakarwa, domin yanzu saisu raba mutum da mahaliccin
sa....Allah katsaremu👏🏼👏🏼👏🏼

😪😪😓😪

In kunne yaje👂🏽👂🏽👂🏽 jiki ya tsira! Wanda yayi dakyau shi zaiga da kyau wanda ya cuce wani kansa ya cuca, haramunne bin bokayi yan duba da yan bori masu camfi da sauransu😭😭😭 mutane bakwaje tsoron Azabar Allah ba? bakwaje tsoron wuta ba? bakwayi fatan hasken kabari ba? Ba kwaje tsoron matsalar kabari ba? Ba kwaso ku kyautatawa mutane nagare ba? Mu tuba mubi Allah mukuma dinga tunawa da azabarsa😭 yau in kaine gobe bakai baniba kana zaune zaace kamutu .....Allah yaganar da batattu yakuma shirye shiryayyun👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼

     MU HADU AKASHE NA GABA....

*Urs Nana diso*

nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[2/20, 3:07 AM] ✨kubrieh cier vervier: _30-50_

*MUTANEN KIRKI AN GAISHEKU*

  (HAKURI DAI SHINE....)

   _NANA DISO_

      WATA 'YAR TUNASARWA CE👌🏼👌🏼

🚶🏻‍♀🚶🏻‍♀🚶🏻‍♀🚶🏻‍♀🚶🏻‍♀

To Ina kike mata tagare An cuceki kin hada mutum da Allah, An rabaki da mijinki kinyi hakuri..😃

Nasan wata zatazo tace miki ai kitashi tsaye kinemi dafai ko tsare kokuma daukaka...

-🚶🏻😂😂kalleta kice Allah ko?

- In tace kwarai kuwa..

- sai kice mata ai ne tuntuni ina neman Dafa'i ina kuma tare da mai tsare bayinsa!

- Intace ashi ke kin bazama tuntuni👌🏼 cenemata ai Na dadi ina sallah nakuma dadi ina gayawa Allah A sujjada kuma nasan yanasani dani kamar yadda na yarda da kaddarar sa ina fata wannan kaddarar ta zamar min Alheri😊....

- zakiga tayi saroro tana kallonki sai kice mata Nema malamar kaina ce..

- zatayi mikaina dariya..

  - Kemah sai kiyi mata murmushi kice mata Ainema Allah yabani ilimi, zan tashi nema nayi sallah na rokeshi in sadakace ma basai wane ya sakane ba da kaina zanyi, babu mai cimin tashi nayi sallar dan bana tunanin yafine sanin kaina da kaina bana tunanin yafine son ubangiji yakuma fine tsoronsa domin nema ina salati ina sallah ina duk wasu abubuwan da Allah ya umarci ne dashi, Almahimmi ma bana shirka ballantana na hada wane da wane...

    " zataci miki ke bazaki gane ba!...

    " kiyi mata dariya kice mata aduniyar nan fa ke kadaice masoyiyar kanki kikadaice sahibar kanki ki kuma zaki gyara kanki kina tunanin akwai wane mahaluki da zaiyi miki sallah ya dinga cewa ai donke yayi? Kokina tunanin ba ke kadai zakiyi adduar ki kuma Allah ya amsa miki ba? Kije ana kwana akayi ana addua why not ke ki tashi ki kwana kina sallar mana?....Nasan batada amsa yanzu Sai tunani😂😂😂

😇😇😇😇

Ki kalle ta kice mata au baki gama tunanin bani ba??

   Zataci miki😂😂 ita no babu tunanin datakeyi....

    Kice mata aikuwa kina bukatar tunani...

    Shiru zatayi tana jiran Abunda zakice mata 👉🏼

    Ki kalleta kice Mai sihiri ko kuma mai neman a yi masa sihirin bai yarda da cewa Allah ne abin dogaronsa ba, kuma shi ne mai taimakonsa ba,👏🏼 kuma shi kadai ne mai iya fitar da shi daga kowace matsala,😰 ya kuma dauke masa kowa ce irin damuwa🤔 a zuciyarsa ko jikinsa ko abokin zamansa ko zuriyyarsa..
.
Allah Madaukaki yana cewa: “Duk wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar masa”....😃ko Kin manta da wannan ayar ce?

Haba baiwar Allah, ga mahaliccinki, mai kowa mai komai, wanda ba bu abin da zai faru cikin halittarsa sai da saninsa da izininsa, wanda shi ne Mabuwayi,👏🏼 babu wanda ya gagare shi, babu mai iya ja da shi, ga shi da kansa yana ba ki alwashi cewa in kin dogara da shi to ya isar maki, wato ya isar maki daga wata cuta da ta shafe ki daga wani dan Adam ko aljan sai da izininsa, 👌🏼ya isar maki daga abokin gabarki, ya isar maki daga zaluncin azzalumi cikin sammai ko kassai, cikin duhun dare ko ido-na-ganin-ido, ya isar maki daga mai nufin jefa miki badin ciki a zuriyyarki ko a dukiyarki ta hanyar raba ki da abin kaunarki, miji ko da ko dan uwa ko makaman tansu, 😭ya isar maki daga dukkan sharri daga dukkan mai nufin sharri.😭

  Don Allah ki daure ki dogara da shi, za ko ki ga cika alkawari. “Wa ya fi Allah cika alkawari?” (Suratut Taubah: 111).....

   Zatace kuma fa gaskiya kike fada fa?

  Kice Mata ko kin manta da ya shafi hakkin shi wanda aka cutar din, domin har abada Allah zai bi ki da alhakinsa har sai in ya yafe miki, bayan babban laifin shirkar da aka yi😭 Abu ne sananne cewa ba ya halatta mutum ya cutar da dan uwansa musulmi...😔😔

   " zakiga tafara cemiki kwairai kuwa...

    " cikin jindadi kikara cemata Jaddada imani a zukatan muminai, da komawa zuwa ga Allah da dogaro da shi, da tabbatar da tauhidi da kadaita Allah cikin bauta, da nesantar duk abin da ke da alaka da shirka🚶🏻🚶🏻👺 Kada kuma musulmi ya manta da fadin Allah cewa: “Kuma ba su cutar kowa da shi (sihirin) sai da izinin Allah”.......

    To yar'uwa wacce hanya zanbi domin Neman tsare?

    Tashi muyi sallah sai mudawo....

     MU HADU AKASHE NA GABA....

*Urs Nana diso*

nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[2/20, 3:31 AM] ✨kubrieh cier vervier: _50-60_

*MUTANEN KIRKI AN GAISHEKU*

  (HAKURI DAI SHINE....)

   _NANA DISO_

      WATA 'YAR TUNASARWA CE👌🏼👌🏼

🚶‍♀🚶‍♀🚶‍♀🚶‍♀

Tunda mundawo daga Sallar sanar dani addu'o'in tsaren to?

    " sai kiyi murmushi kice a takaice wannan hanya ita ce lizimtar dukkanin abubuwan da Allah Malicci Ya yi umarni da ayi daidai gwargwado, kamar
tsayar da Sallah akan lokaci a cikin kyakkyawan tsarki, da yawan nafifilin da Shara'a ta zayyana da yawan karatun Al'kur'ani mai girma, ya zamana akullum kana da abinda za ka karanta ba wai sai watan Ramadan ba, da
Is'tighfari da kula da zikiran bayan Salloli, da addu'o'in shiga bandaki, domin bandaki yana daga cikin wuraren da suke matattara aljanu, ambaton Allah yayin ako yaushe...

   Yar uwa ina zansamu littafin da yake kunshi da adduoin???

   mafi kyawun littafi na zikiri da aka rubuta anan kurkusa shine ‘Hisnul Muslim’
zaku same shi a wuraren masu saida littattafai an fassarashi zuwa Hausa da Ingilishi.....

    " yar uwa Zaki iya sanar dani wasu Addu'o'in ko nasiyo littafin?

    Ayatul Kursiyyi, Ma'aikin Allah  Ya ce: “Duk wanda ya karanta ta alokacin da zai kwanta Allah zai sanya mishi mai kula da shi har gari yawaye”. Bukhari ya ruwaito shi, kuma ayar: ٱللَّهُ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلْحَىُّ ٱلْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُۥ سِنَةٌۭ وَلَا نَوْمٌۭ ۚ لَّهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَ‌ٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۗ مَن ذَا ٱلَّذِى يَشْفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذْنِهِۦ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَىْءٍۢ مِّنْ عِلْمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَ ۚ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ ٱلسَّمَـٰوَ‌ٰتِ وَٱلْأَرْضَ ۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ ٱلْعَلِىُّ ٱلْعَظِيمُ ۝

Amanar Rasulu (Ayoyi biyun Karshen Suratul Bakara) alokacin da
mutum zai kwanta bacci, “Duk wanda ya karanta su sun isar masa”.
Bukhari da Muslim suka ruwai to, ga ayoyin: آمَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنْزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّ بِّهِ ۦ وَٱلْمُؤْمِنُونَ ۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِاللَّهِ وَمَلٓئِكَتِهِ ۦ وَكُتُبِهِ ۦ وَرُسُلِهِ ۦ ، لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ ۦ ۚ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا ۖ غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ ٱلْمَصِيْرُ ﴿٢٨٥﴾ ‏لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا ۚ لَهاَ مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا ٱكْتَسَبَتْ ۗ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَآ إِن نَّسِينَآ أَوْ أَخْطَأْ نَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تَحْمِلْ عَلَيْنَآ إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ و عَلَى ٱلَّذِيْنَ مِن قَبْلِنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلْنَا مَا لَا طَا قَةَ لَنَا بِهِ ۦ ۖ وَٱعْفُ عَنَّا وَٱغْفِرْ لَنَا وَٱرْحَمْنَآ ۚ أَنْتَ مَوْلَىٰنَا فَٱنْصُرْنَا عَلَى ٱلْقَوْمِ ٱلْكٰفِرِيْنَ ﴿٢٨٦﴾

  Kinje kadan daga cikin su ko?

   Yar uwa dankaromin wasu mana....

   Bari Nasha ruwa Na dawo...

     MU HADU AKASHE NA GABA....

*Urs Nana diso*

nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[2/20, 4:14 AM] ✨kubrieh cier vervier: _60-70_

*MUTANEN KIRKI AN GAISHEKU*

  (HAKURI DAI SHINE....)

   _NANA DISO_

      WATA 'YAR TUNASARWA CE👌🏼👌🏼

🚶‍♀🚶‍♀🚶‍♀🚶‍♀

Mashaa Allahu Na dawo Bari nakarasa miki...

   " yauwa yar uwa Ina jinki...

  ADDU'AR IDAN MUTUN YARAZANA ACIKIN BACCI ♥ *auzu bikalimatillahit tammati min gadabihi wa'ikadihi washarri ibadihi wamin hama zatis shayatin wa an yahadurun)*

Addu'ar Shiga gida.
Ita kuma wannan adduar itace take karantawa yayin Shiga gida.
ﺑِﺴْـﻢِ ﺍﻟﻠّﻪِ ﻭَﻟَﺠْﻨـَﺎ، ﻭَﺑِﺴْـﻢِ ﺍﻟﻠّﻪِ ﺧَـﺮَﺟْﻨـَﺎ، ﻭَﻋَﻠَـﻰ ﺭَﺑِّﻨـَﺎ ﺗَﻮَﻛّﻠْـﻨَﺎ
*Bismillaahi  walajnaa, wa bismillaahi kharaj naa,wa 'alaaRabblnaa tawakkalnaa*

Abu Huraira yace: "Annabi Muhammadu (S.A.W) yace, “Duk wanda yace *‘La’ilaha illallahu wahadahu lasharika lahu, lahul mulku, walahul hamdu wa huwa ala kulli shai’in kadeer’* a cikin yini sau dari, zai samu lada kwatankwacin wanda ya ‘yanta bayi goma, kuma za’a rubuta masa lada dari, za’a kankare masa laifuffukansa dari, kuma zai samu kariya daga shaidan na wannan yini dukkansa, sannan kuma babu wanda zai zo da ladan da yayi nashi a ranar kiyama sai dai wanda ya karanta wannan zikiri da adadin dayafi nasa”.
(Bukhari da Muslimu).

Sayyidina Usman, Allah ya yarda dashi, yace Manzon Allah (S.A.W) yace “Babu wani bawa da zai rika fadin wannan zikiri safe da yamma, sau uku face Allah ya tsare shi daga dukkan sharri watau; *Bismillahillazi la yadhurru ma’a ismihi shai’un fil ardhi wala fissama’i wa huwassami’ul alimu”* (Abu Dawud da Tirmizi).

*Allahumma anta rabbee la ilaha illa ant, khalaq-tanee wa-ana aabduk, wa-ana ala aah-dika wa wa’dika mas-ta-taat, Aa’oozu’bika min sharri ma sana’atu, Aboo-o laka bini’matika alayya, wa-aboo-o bi-zan-bee, Faghfir lee fa-innahu la yagh-firu-zunooba illa ant*( Wannan shine shugaban istigfari gaba daya duk wani istigfari da zakayi ka roki Allah (S.W.T) gafara wannan shine shugabansa daga bakin Annabin Rahama (kuma Annabin Rahama yace duk wadda ya karanta wannan addua’ar yana mai yakini idan ya mutu da safe ana zata masa zai shiga Aljanna haka zalika duk wadda ya karanta da yamma ya mutu yana mai yakini sai ya Shiga Aljanna.....

alokaci wanciya bacci ita ce: zaka buda hannayanka biyu, sai ka karanta Kulhuwa sai ka tofa a hannu wanna ka, sannan sai ka karan ta Falaki, ita ma ka tofa, sannan sai ka karanta Nasi ita ma ka tofa, sannan sai ka shafo jikinka daga saman (kai) zuwa inda ka tsaya, sannan
sai ka maimaita ‘Kulhuwa da Falak da Nas’, kana tofawa a hannayan naka sannan ka shafa a jiki, sannan sai ka sake maimai tawa, sau uku...

    " Alhamdulilahi nagode wa Allah da yabani kawa mai tunani gashi nema Allah yasa kin fadakar dani, ina fita zan huce kasuwa domin nasiyo littafim Nema nafara haddacewa....

   " Ne dai *yar tunsarwa ce*

    " To yanzu kawata wasu ayoyine Na karya Shiri? ??

    Za'a Nemi Ganyen Magarya Guda 7  a daka a tsre da duttse guda biyu Sai a zuba a cikin tsabtataccen Ruwa a rika sha ana wanka In shaa Allahu za'a samu Waraka da Iznin Allah.
Ayoyin da za'a karanta Sune;
FATIHA kafa 1
AYATUL KURSIYU sau 3
Suratul Aaraf Ayah ta 120-ta 122
Suratul Yununs Ayah 81-ta 82
Suratul Daha Ayah ta 79
Suratul muimin,Ayah ta 115-ta 118
Suratul furqan Ayah ta 23.....

   Toh  Nagode...

   Mutum ya tashi acikin Sulusin dare na karshe wato daga karfe uku kenan har zuwa hudowar alfijir.....

(Saboda lokaci ne mai albarka wanda Allah yake amsa addu'a sosai acikinsa)

Yayi nafilfili sannan ya
zauna yayi ma Annabi (saww) salati gwargwadon iko.

(Domin shi salati mabudi ne.).

Sannan ya karanta ayatul kursiyyi (domin ita ce ayah mafi girma acikin Alqur'ani).

Sannan ya karanta addu'ar nan ta Annabi Yunus (as) wacce Manzon Allah (saww) yace duk wanda ya
karanta Allah zai yaye damuwarsa, zai biya masa bukatarsa.
Addu'ar ita ce : "LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZWALIMEEN".
Sannan mutum fadi bukatunsa sannan ya Qara yin salati ga Manzon Allah (saww).
In sha Allahu Za'a samu biyan bukatu da yayewar bakin ciki ko damuwa.

Domin wadannan hanyoyin ingantattu ne daga Manzon Allah (saw).......

     Toh mungode miki sosai Allah ya biya ki👏🏼....

   Ameen

❤❤❤❤😰😪 Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah, kuma tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabishi Muhammad  da iyalanshi da kuma sahabban shi baki
daya...ALLAH YA YAFI MAMA KURAKURAN DAMUKA YI ALLAH YARABAMU DA YIN
SHIRKA....

    

*Urs Nana diso*

nanadisoo.blogspot.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

No comments:

Post a Comment