BANDASHOO
KAYAN DA ZA KI
TANADA
1. Gurasa mai gishiri
2. Dakakken kuli-kuli
3. Albasa
4. Tumatir
5. Mai
6.cabegge
YADDA ZA KI HADA
Ki sami gurasarki ki saka ta a cikin ruwan dumi, tayi kamar sakan biyar a ciki sai ki cire, ki tsanar da ita, ko kuma ki turarata, abin da dai ake so shi ne gurasar ta yi laushi sosai,sai ki zuba mai gaba da
bayanta, sai ki kawo kuli-kuli ki barbada,Sai kisaka cabejinki shi ma gaba da baya, sai ki yanka tumatir da albasa akai, idan kina bukata kina iya kara mai domin ya ji. Ki tabbatar kuli-kulinki ya ji magi, ba sai kin zo kinakarawa bandasho din ba...NANADISOO💕💕
No comments:
Post a Comment