*Panke*
Abin Bukata
filawa kofi 2
kofi 1/2 na ruwan dumi
ckb 1 na yis
1/2 na sikari
yadda za ayi
a zuba yis cikin ruwan dumi don ya narke
sai a zuba akan filawa tare da sikari,gishiri kadan a kwaba su baki daya yayi dan tauri a sami wuri me dumi a ajiye don ya tashi a sami kamar
Minti20,a dora mai a wuta idan yayi zafi sai kisa hannunki ki dinga yankowa kina sawa a cikin man. idan ya soyu zaki ga ya zama ruwan kasa.
*kada amanta kwabin kada ya zama ruwa-ruwa ko yayi tauri* urs nanadiso💕💕
No comments:
Post a Comment