_64-66_
*MATA NAH*
_NA NANA DISO_
Gurin karfe hudu Amina tana bakin Gado azaune tana kokarin Kiran haris Sai ganin Amira tayi da tabarya bilkisu da wayar kebur..
" cikinta ne ya kada nan da nan ta tsorata ta danna number Haris ta kifa wayar..
" dariya suka saka ashi ke yar iskar karyace to yau saimun cere abunda yake cikinki amira ki kwala mata ta baryar ne zan zanita yaufa saimun illata ki, Amira ta karatun fashewa da dariya ko kinada wasiyya ne?
" Amina batasan lokacin da tafara kuka ba....
" bilkisu ta daga wayar tana kokarin zuba mata Amira tace Haris dak'e faman cike wasu files wayar na shigowa ya dauka hello sweetheart ya'akayi?
" sautin k'uk'an ta yaji tana kuje tsoron Allah he just end the call, muta ya shiga directly gida ya nufo..
" Amira tace gwara mu kashek'i ai damu zauna muna ganink'i da cikin nan har ki haife!
" kusani Allah shike rayawa kuma yake mutarwa rayuwar Nan tafi karfinku! kuma ne yar'uwar kuce a musulunci zakuyi danasani mafe asara arayuwar ku..
" hahaha cewar bilkisu kinje bullshit yanzu idan muka kashek'i wazai San munyi?
" Allah Yana k'allon ku ai haba kishiyoyi na kudaina abunda kukeyi! Ku dinga cutar da yan'uwan ku Akan d'a namiji? Har kuna yi musu asiri! Duk Akan D'a namijin da bazaku zauna tare dashi a kabari ba! Wannan ai ba kishi bani wawance ne?
" bilkisu ce tace zakiyi shiru ko saina fasa Miki jiki!
" Sai shigen kyawun Hali Duk kinga da mijinmu...
" kuka tafashe dashi Sai ga Haris ya shigo Kai lallai kun nunamin bakwa kauna ta bakwa sona matar tawa zaku kashe min? Kisa?
" Amira ce tafara sakin tabaryar sannan bilkisu itama ta saki wayar hannun ta please kayi hakuri sharrin shaidan ne!
" yau zan nuna muku ne da namiji ne wayar kibur din ya dauk'a ya fara zubawa Amira, Sai kunje ajikin ku ai tanata ihu..
" Amina ce ta mik'i jiki Sai rawa yakiyi hannun sa ta rik'e sannan tace Dan Allah kakyale su!
" kyalene na koya musu hankali kinje..
" Yaya Hakan Bai dace ba!
" kinga Amina ja gefe wannan ai iskance ne idan da sun aikata fa?
" Amina ce tafashi da kuka ai dama ne sukayi wa Kuma na yafe musu!
" Zama yayi akusa da'ita ya riko hannun ta..
" Bilkisu da Amira kuwa da rarrafe suka bar dak'in yanzu da ya zane mu kincuce mu cewar bilkisu..
" Amira tace muna fuka kawai dama ai keki ka bada wannan shawarar zaki kashe mana aure!
" bilkisu tace nice munafukar? Nan fa suka fara dambe wannan tana ihu waccan tanayi..
" Amina ce tace yaya kaje kayi musu magana mana!
" Amina kenan narasa wannan hali irin naki Allah yayi miki albarka ya sauke ki lafiya..
" Amin tace sannan ta tashi tashiga bandaki domin gabatar da sallar azahar...
" bilkisu tana daki tanata huce zuciya tayi fal tanaji anata kiran sallah sai ta kwanta tayi baccin wahala ya dauke ta...
Amira ce tatashi tsaye Tama kasa zama wanke fuskar ta tayi sannan taja hijjabin ta direct Sai hanyar fita kicibus sukayi da haris!
" Ina zakije?
" kuka tasaka tace hajiya ce batajin dadi shine zanje gurin ta!
" okay dama Abu zansiyo muje na kaiki!
" sai data danyi diris nadan lokaci sannan tace ai..
" ai me dallah shige muje..
" Tunda suka shiga mota babu wanda yace k'ala Amira kuwa tsoro duk ya k'amata yanzu in hajiya ta karyata ta fa?
" suna isa cik'in gidan suk'a tarar da'ita zaune akan tabarma..
" sannun k'u da zuwa yan Albarka sai yau?
" haris yace yauwa hajiya ina yini?
" lafiya lou ya kok'ari? " lpya lou
" ya jiki jikin nak'i daman Amira tana yawan cemun baki da lafiya..
" hajiya ce takalle amira cikin mamaki..
" Amira kuwa tadage sai alamu take mata da hannu..
" Aikuwa hajiya sai cewa tayi ai ita karya babu kyau jik'i ne na tsofa sai a hankali..
" to hajiya ga wannan Allah ya k'ara sauk'i..
" k'ai k'wa 'dan nan bak'a gajiya to nagode sosai...
" bakomai hajiya Amira by 5 zanzo na dauk'e k'i !
" to...
" hajiya ce ta k'alle ke Amira bazaki tuba kidaina abunda k'ike yi ba kidinga jin tsoron Allah wallahi badama nayi magana yanzu sai bakin uwa ya kamaki! Gidan uban wa kike zuwa dakike tambayar unguwa ince dai ba yawon maza kikeyi ba?
" haba hajiya yaza'ayi nabi maza? Wannan banzar uwar haris dince ta takuramin!
" ke kinada hankali kuwa? Idan Kika Raina Uwar Mijin Ki,toh Ke kuma taki Uwar Fah? Yaya Zata Kasance Agurin Matan Y'an Uwan Ki! Kwata kwata bakwa abu da hankali uwar wani ai uwarki ce..
" Amma hajiya Amina fa takusa haihuwa ko ciki banida shi!.
" Shak'arya ai haihuwa nufine na Allah! Kije ki tuba kisaka tsoron Allah aranki kiyi addu'a inda rabonki sai Allah yabaki...
" to kawai tace batare da ta gamsu da shawarar ta taba...
Assalamu Alaikum!
" lalala sannu da zuwa maryam ai da nayi fushi kullum farouk yace mun zakizo amma shiru?
" wallahi ke dai bari abun ne sai hakuri yanzu dai gani nazo sannu mai ciki irin wannan kokari haka!.
" hmm maryam kenan yakke?
" lpylou nake ina abokan zaman nake ne?
" kafin amina tayi magana bilkisu tace ganinan ince dai lafiya?
" maryam tace sannu dama gaisawa zamuyi!
" mtseww ke kuma daga ina?
" daga dangin mijinki cewar maryam..
" to sannun ki tv taje ta kunna sannan tasamu ta kunna wata tasha kida kawai sukeyi...
" Amina tace dan rage volume din!
" bazan rage ba idan kingaje ki tashi kibar palour din mana sai shigen fi'ilin tsiya wai ke me ciki mtseww...
" Amina tace tashi mukuma daki maryam...
" maryam tace gaskiya kina hakuri amina ai sai kicemun jahilai aka auro miki inbanda tsabar rashin hankali la'asar tayi banda kije kiyi lazumi da dan karatun alkur'ani shine kikazo kika zauna kinajen kayan shedanu!
" Ke dakata cewar bilkisu kinyi kadan nayi dake..
" ai duk wanda yaraina dangin miji tofa shima sai an raina danginsa ai dama gaba da gaban ta...
" amina tace please kubari mana sai kace yara?
" kinga yi shiru Amina wayan nan kindai haka zaki dinga yimusu shiru sun raina ki suje su saka miki ciwon zuciya kinga ne sai anjima...
" Muna fuka gwara dakika tafi din kinzo zakiyi mana wane mulki banza kawai...
" bilkisu kenan ya kamata kisan me kikeyi, please ki koma makaranta ki k'asance mai son ilimi, ki zama mai hakuri, uwa uba ma mai kamun kai, tashin hankali banaki baniba kizama mace tagare da mala'iku zasu dinga yimiki addu'a rahamar Allah ta lullubeki!.
" sannu malama uwar malamai kije kije da tunbuli lin cikin k'i Amma kinyi kadan kiyi mun wa'azi...
" Amina ce tayi dariya kaji sauna? Ta shige daki..
Hello Amina wallahi nagaji da wannan halin mijin nawa fa haba ne fa zance masa ya sak'e ne fa?
" haba safiyya ai wallahi ki zama mai tattalin mijinki Kamar yadda Allah ya umarce mu, dan zaki iya samun aljannarki a wajen Allah ta hanyar mijin ki, hakuri zakiyi kidinga samar masa Abunda yakeso kina faranta masa, kidinga tsaftace kanki kinje! Kiyi masa d'a i'dan yayi miki umarni, zan kiraki safiyya bare zan kiraki..
" tohm nagode...
Bayan wasu mintuna Amina tafito daga daki Jik'in nata babu d'adi hak'a taje ta dafa zogale ta had'ashi tasak'a k'uli k'uli da maggi sai albasa da attaruhu da mai da ta dan soyasu ta samu plate ta juye sannan ta dora musu taliya da miya bata gama ba sai gurin 6 ta jera komai ak'an dining hutawa ta tafiyi ad'aki..
" Amira ce da haris suka shigo atare sunata hira bilkisu kuwa ta dage sai cin zogale takeyi a dinning haris ne ya zauna shima yana cin Abincin...
" ashe unguwa kikaje? Cewar bilkisu..
" eh unguwa naje sai me?
" haris yace ke bilkisu ince wannan ai zogalen Amina ce ko ke kika hada?
" tayaya inason abu zank'i ci? In tadamu dashi ta hada wane...
" will yoy shoutup? Ita batacin abincin Amma haka tak'e dafa muku! Abunda take ci din shine zaki cinye mata to wallahi sai kin gane k'uran k'i,..
" Amira tace ai kasan abunda mutum bai iyaba shine take mata bak'in ciki
" to ke iyawa kikaye ne?
" Amina ce tafito tace sannu da zuwa yaya dafatan kadawo lpya?
" lpylou my meena ya karfin jiki?
" Alhamdulilh ya ba'a dak'ko maka juice din ba yana frige ai mikewa tayi ta dak'ko masa amma yau da wuri ko magrib ba'ayi ba kuke cin abinci?
" meena yunwa nakeji shiyasa..
" bilkisu kuwa dan Amina taga zogalen nata sai cewa tayi me ciki sannu da aiki!
" yauwa billy ashe kinason zogalen kema ai da kinsanar dani da nayi dayawa!
" lah wannan ma ya'isa..
" Allah yasa yayi miki dadi dai?
" sosaima...
" Dallah yi manah shiru cewar haris sai wane magana kikeyi dan taje haushi?
" la bakomai yaya ai nadamu lada ai yanzu ma nace dabino adaki ya cika mun ciki Ai duk daya muke...
" bilkisu da Amira mamakin halin Amina sukeyi...
" Haris kuwa sai cewa yayi Allah yayi miki albarka matata!
" haba yaya ai sai kace matan ka!
" my sugar ai wannan baka kyauta ba?
" ina adalci anan?
" subhnlhi ai banyi sallar la'sar ba!
"Amina cikin mamaki tace wacce sallar kaddai kace sallar la'asar haba yaya mik'akeyi har sallah la'asar ta huce...
" Haris yace to aine nazata nayi bari na karasa cin Abincin naji nayi..
" haba yaya sallar la'asar tana da falala sosai kamar yadda yazo acikin hadisi da mutum yak'iyin sallar la'asar da wuri gwara yayi asarar duk'iyar sa, kuma sallah ba abun wasa bace ba Allah yabaka lafiya ya baka abunda kakeso yakareka, ido, kafafu, hannu, lafiya daga abubuwa da dama amma katsaya ka bautawa Allah nadan lokaci shine har...
" Malama kin ishemu da surutu ko kinje yace ba zaiyi bani ba? sai wasu bayanai kikeyi yan yan yan mtseww cewar Amira...
" bilkisu tasa dariya kema kyafada ita alallai komai tasani mtsew aikin banza k'awai...
" Ku narasa wasu irin matane wannan ai gaskiya tagaya mini har ma daku mikewa yayi yaji yayi Alwala sannan ya fara sallah...
" Duk sunyi shiru kowa da Abunda yake sak'awa acik'in zuciyar sa..
" to mashaa Allah to na idar!
" haba yaya ai bakayi addu'ar bayan sallama ba!
" opps mata ta tak'aina nagode bari najira ayiwa magriba..
" magriba kuma agida ka tafi zuwa masallaci kayi samu ladan k'a mana...
" tohm meena bari na tafi direct waje yafita ya nufi masallaci...
" mtseww uwar munafurce kawai wai k'ai a lallai sai an soka!
" ke ni banda lokacin ku sallah zanje nayi Amma kusani Har abada akwai zukatan da ke son ka ko da kana munana ma su Akwai kuma ma su kin ka duk yadda ka kyautata ma su,Kowa da kiwon da ya karbe shi, Dak'in ta ta shiga tayi ..
" hmm wallahi na tsaneki cewar Amira..
" nema na tsanike mtsw..
Assalamu Alaikum!
" Assalamu alaikum!!
" Assalamu alaikum!!! Bayin Allah inata yi muku sallama amma kunyi mane shiru aiko baku kulani ba kwa amsa sallamar kodan samun lada!
" Dallah malama bak'in san dakin dakika zo ba?
" Amira tace ke kikaye mata magana ma!
" hmm to Allah ya sawake Dak'in Amina tashiga sallama tayi...
" tana zaune Akan gado ta amsa mata, fatima barka dazuwa!
" yauwa anty meena inayini ya gida, yak'arfin jikin nak'i?
" lpylou
" to Allah yaraba lafiya..
" Amin..
" Anty meena wallahi ina cikin matsala?
" fatima me ke faru ne?
" kinga kullum yawan mafark'ayi marasa kyau kunar rai wallahi in zanyi sallah sai kasala!
" to subhhi Allah ubangiji ya yayi miki! Bakomai zan gaya miki ba illah kisaka tsoron Allah aranki, kikuma tuna Cewa duk wata jarraba ta rayuwar k'i Allah yariga ya rubuta, Aduk lokacin dakikaje kiran sallah kidinga gaggautawa gurin alwala da kuma neman tsare daga shaidan, Ahaka inshaa Allahu zakije kin dage,kuma Duk lokacin da baki da Aiki sai ki dak'ko kur'ani kidinga tulawa, kuma kidinga daurewa kina jajercewa gurin sallah dare domin duk mai yin sallar dare babu abunda zai tsoratar dashi..
Ba ruwanki da mtsalar wani ki fusk'an ce taki matsalar, kuma kidinga kok'arin yin zik'irin k'in k'ikazo kwanciya subhanallah33, walhamdulilah33, wallahu akbar 34 domin annabi (saw) ne yasanar da nana fad'ima zaki iya duba shi acikin /sahihul bukari /...
ki dinga k'wanciya a bangaran dama, ki karanta ayatul kursiyu domin tsare da amanarrasulu,falaqi da nasi da dai sauran su ki daina zama da babu dak'wali daure ki zauna da Dan kwali ko Awane haline! K'i dinga shiga bandak'i da k'afar dama k'i kuma fita da k'afar hagu k'i dinga zik'irin shiga bandak'in dana fita...
k'inga zaki iya zikirin ki ko ak'wace ko azaune, bismillah, innalillahi wainna illahir raji'un ba'ason harshen ki ya k'atse daga ambaton Allah, k'o tafiya kik'eyi k'aga wane abun sai kice innalillah, abinci zakice bismillah, inkin koshe Alhamdlh, kinyi tuntube innalilahi, k'uma Yawan sadak'a yawan istigfari da kuma da kuma salati ga shugaban halitta..
" (saw) tohm anty meena wallahi nagode domin abunda kika fadamun nasan zai amfani a rayuwa ta kuma wannan shine musulunci komai zamuyi sai mun ambace Allah, nagode madallah dake Allah kuma yaraba lafiya..
" Amin bakomai yar uwa...
Bayan fitar fatima Amina ta mik'i taje ta markada zogale ta Sak'a madara sanna taji daki ta zuba zuma tana cikin sha farida takira hello Amina?
" Naam sister ya'ayi?
" Ina asubuti zan haihu please kiyimun Addu'a..
" bari natawo kinje...
" basai kinzo ba sai anjima kiyimun Addu'a..
" Amina ce tafita palour hankalin ta duk atashi yaya yaya!
" me yafaru Amina?
" Dan Allah kakaine Asubuti farida tana chan zata haihu fa..
" haba amina addu'a zakiyi mata ki daina tada hankalin ki, me isa ma tagaya miki ai wannan bai dace ba...
" wane rikitaccen kuka ta saka ne k'a k'aine please!
" hannun ta ya rike sai dak'in sa menene na k'ukan haba mata ta kiyi shiru mana!...
" tohm yaya ta rungumesa..
" Nan hankalin sa ya tashi kayan ta yafara kokarin rabata dasu tun tana yaya ka kyaleni har ta saki jik'in ta nan ya dinga sarrafa ta..
" Da asuba kuwa har dana sanin ashan hadin zogalan tayi wanka tayi ta nufi kitchen..
" Haris yana dawowa yaga sai jira abinci takeyi Kai yanzu bazasu tausaya mik'i ba? Ke bilkisu! Ke Amira kuzo..
" haba my sugar wannan kira haka?
" wannan wane irin rashin tausayi ne? To daga yau duk ran girken Amina kudinga haduwa ku kunayi bazata kara shiga kitchen ba..
" haba yaya..
" yimun shiru kiduba kiga dakyar kike komai! kundai je mai nace ko?
" aciki suka amsa...
Karfe 2 aka kirata akace farida ta haihu mace! Murna ba'acewa komai! ta gayawa Haris yace ta shirya kafin yaje ya sha mai ya kaita!
Tagama shiryawa kenan tafito palour ta tarar dasu bilkisu sai kuwa cik'inta yafara ciwo Abu Kamar wasa ina sai ihu yakeyi tana kiran sunan!
" suka saka dariya ai acikin mu babu mai kulaki sai dai ke mutu cikin nakuda..
" ku taimaka min kukira haris wayyo ya Allah cikina cikina wayyo Allah ya arhamar rahimin...
" mtseww sukace kowanne ya shige dak'in sa...
" wata kara tayi tare badin cikina la'ilah ha'illal lahu, shikenan.....
*Urs Nana diso*
http//:nanadisoo.mywapblog.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/19/2016, 9:53 AM] Cvrieh sier verbier✨: _66-70_
*MATA NAH*
_NA NANA DISO_
Ta gama shiryawa kenan ta fito palour ta tarar dasu bilk'isu sai kuwa cik'inta yafara ciwo Abu Kamar wasa ina sai ihu takeyi tana kiran sunan!
" suka saka dariya ai acikin mu babu mai kulaki sai dai ke mutu cikin nakuda..
" ku taimaka min kukira haris wayyo ya Allah cikina cikina wayyo Allah ya arhamar rahimin...
" mtseww sukace kowanne ya shige dak'in sa...
" wata kara tayi tare badin cikina la'ilah ha'illal lahu, shikenan mutuwa zanyi...
Haris ya shigo palour din kenan yaji alamun nishin ta daga nan ya lura da halin da take ciki arazane yaje ya kamota..
" baba baba...
" naam alhaji budimun gate yi sauri..
" to alhaji.
" cikin kankanin lokaci ya bude masa gate daga Nan ya suri mota Sai asubuti!
" suna isa yakira nurse din akayi dak'in haihuwa da i'ta, Haris hankalin sa ya tashi kubarni na shiga kada mata ta ta mutu!
" Dr ya dafa ka fadarsa cool down haris zata sauka lafiya so just pray for her!
" okay doctor Bari na zauna anan..
" nurse tace Kaine haris?
" what wrong nine?
" baku tawo da kayan baby's ba!
" oh shit aimun manta Bari naji na dakko...
"Okay kayi sauri..
Suna jin karar fitar su dukk'a nin su suka fito, Amira ce tafara cewa shigea gwara ma ta mutu kowa ya huta..
" bilkisu tace ke dai bari mata sai kine bibin tsiya aikin banza, ne wallahi naso haris bai dawo da wuri ba..
" karki damu bilkisu sai tana jego zamu hada mata wane tuggun!
" ai dole ne wannan domin baby zai gane kuransa..
" Duk maganar da sukeyi a kunnen haris k'ada kansa yayi ya shigo tare da sallama...
" Duk sun rikece suna tsoron kaddai yaji abinda sukace, nan bilkisu tace sweetheart kaddai ta mutu naga kashigo jiki duk asanyayi!
" nema haka nagane..
" ai mutuwa sai lokaci yayi..ya shiga dak'inta ya dak'ko akwatin, bilkisu?
" Naam mijina..
" ki dafa abunci kikuma dafa tea zan aiko auwalu ya karba..
" tohm angama..
" yana fita tace kaji banza Wai nayi mata girke aikuwa zanyi maganin ta yaji zan cika da gishiri!
" Amira tace dadina dake kema makira ce, ai a tea din ma ki saka barkono!
" Ai kuwa kinkawo idea's bari na tafi kitchen din..
" tana barin gurin ameera ta saka dariya kije kikashe auren ki, kema na tsaneki..
Haris yana isa asubitin nurse ya mika wa kayan ya jikin nata?
" Kai dai kawai kayi mata addua Allah yaraba lpya domin Kuwa haihuwa ba wasa bace ba!
" hannun sa ya zira a aljihu ya ciro dubu goma ya mik'awa nurse din..
" wannan kudin fa cewar nurse din?
" please ina rokonku da ku kula da mata ta domin asibiti da yawa in ankai mata bakwa kula dasu, ku dinga jin tsoron Allah kuna tunawa da cewa kuma mata ne kuma zaku haihu abunda kukayi shi za'ayi muku..
" nurse tace tabbas hakane Amma kasani imani imani ne kuma karik'i kudin ka indai kabani don na kula da matar ka tofa bazan karba ba wallahi abunda zansamu lada ai ba sai an bine da cin hanci ba!
" aa k'irik'e nabaki dan Allah..
" tohm nagode...
Haris ne fara kiraye kiraye a waya ya sanar dasu mumy Amina tana asubuti, nan mumy ta sanar da dady!
" cikin rabin awa mamie ta iso, haris ina Aminar?
" tana ciki sun hanani shiga..
" tun yaushe takeyin nakudar?
" tun safe takeyi..
" subhnlhi bari na shiga tana karasawa labour room din taganta tana ta ceza bakinta, sannu Amina Allah yaraba lafiya sannu kinje!
" k'ada k'anta tayi sannan tace Mamie ki yafemun Allah yajikan abi da ummi ta, kema Allah ya biyaki da Aljanna..
" sannu Amina sannu kinje zaki haihu wa lapia inshaa Allahu....
" mumy ce ta shigo da saurinta sannu 'yar nan Allah ya sauki ke lafiya...
" to ameen. ..
" kana ganin Amina kasan tana cikin nakuda gaba daya ta chanja...
" kashi nakeji wayyo cikina..
" nurse ta shigo a kayi dak'in haihuwa da ita!
" dr ne yace haris i think sai mun yiwa matarka aiki!
" nop this is impossible babu tayarda zan yarda kuyi mata aiki wannan bazai yihuba...
" okay inbaka yarda ba ai ta mutu!
" haris yace wannan ai son zuciya ne..
" nurse ce tazo da gudu dr ta haihu baby girl,
" good good inji doctor sannan ya nufi dak'in..
" haris yana daka tsalle yace zai shiga akace yayi hakuri ana gyarasu ne...
" barka barka harisu anyi da!
" sun kuyar dakai yayi yana murmushi,
" mames ta sanarwa dasu goggo su zara'u, Asiya,..
" nurse tamik'o musu y'ar haris ne ya karbe ta yayi mata kiran sallah akunne sannan yayi mata huduba, sai kuka takeyi, ya dak'ko zamzam da dabino ya lakuta mata abaki, kuka tafara yi inya inya inya...
" wai ina babarta ne?
" tana toilet tana wanka!
" bari naje na dakko abinci nasanar da sauran *MATA NAH*...
" tohm sai kadawo...
" mumy ta kalle mamie tace kinga ashe yaiya kiran sallar da akiyewa jarirai!
" lah kinje mumy mai zai hana ya'iya ai kiran sallar yanada amfani sosai ga jarirai!
" hakane kam!
" kayanta tasaka tasa pad sannan tafito akan gadon ta zauna!.
" barka barka Allah yakawo yan biyu gaba!
" Amina kunya duk ta i'sheta Wai yau itace da ya!
" mamie tace kinga kamarsu daya da babanta!...
" Aka mika mata yar tana Ansa jitaye wane dadi ya lulubeta, acikin zuciyar tace maihakuri dama shi yake da riba, bantaba tunanin zan haihuba gashi Allah ya sauke ne lafiya!...kallon yar tayi cike da kauna da soyayya, falaqi, da nasi ta tofa mata, da addu'oin tsare, sannan ta tofa mata alhamdulillahi rabbil alamin abakin ta!
" mumy tace wallahi ilimi nada dadi yanzu gashe duk kin tofi y'arki da addu'a..
" murmushi tayi..
Haris yana isa gida ya tarar dasu atsayi sunyi shiru, " bilkisu ya rungume da baya sannan ya kaiwa Amira kiss cikin annashuwa da jindadi ina sonku *MATA NAH* amina tazama tsoka ajikina domin ita Allah yasa tafara faranta min!
" me yafaru cewar Amira?
" nasamu baby girl mai kama dani sak!...
" kana nufin ta haihu lafiya?
" kwarai kuwa kitchen yahuce ya dauki abinci ya shige...
" wayyooo nashiga uku Amina ta haihu ko bari bantaba yiba wallahi yanzu za'afara bala'i...
" duk mugayen adduoin da mukayi mata?
" kowacce tafada dak'inta..
Su anty fadila duk suna asubutin sai zolayar ta sukeyi.....
" Asiya tayi sallama nanne maman baby ta haihu, sannu me jego Allah ya kawo wasu, yajiki jikin nake..
"Da sauki..
" baby din ta dauk'a kai Amma mashaa Allah kamarsu daya da yaya بَارَكَ اللهُ لَكَ وَ بَارَكَ عَلَيْكَ، وجَزَاكَ اللهُ خَيْراً، وَرَزَقَكَ اللهُ مِثْلَهُ، وأَجْزَلَ ثَوَابَك
" ameen
" Gashinan na dafa miki hanta da kaza sai tea da taliya..
" nagode Allah yabar zumunci..
" Ameen mumy tace..
" anty fadila tace taran suna yazama dole ma karma kice baza ayiba, har masu kida sai mun dak'ko..
" uhm cewar Amina ai wallahi baza ayiwa ayata kida ba daga zuwa duniyar nan yadda abubuwa sukayi yawa...
" kema asma'u ai kinsan amina ba kida zatayi ba!
" hmm kyaje dashi dai duk wannan ra'ayin nake kyama sauke shi..
" suka saka dariya...
" haris ne ya shigo, Nan suka dinga yimasa barka!
" abincin ya ajiye sannan yace fadila zuba mata tace...
" tohm yaya ....
"Mumy tace ayir dinka yan'uwan ta sun dafa mata abinci wazaice Abincin matanka!
" but momy ai su suka dafa!
" me sukace sunce Allah yaraya ne?
" a'a to kai kazuba kace!
" fadila zuba mata nak'i...
" amina tace ai mumy duk daya ne dakin barni nace nasu bazasu cuce ni bafa!.
" ina kikasan kanki ai makashinki yana tare dake abunda kikeso shi bayaso!
" mamie tace hakane kam!
" amina takarba tafara ce!!
" fadila ta zubawa haris yana fara ce sai ya zubo dashi mikomin ruwa nan yasha Amma ina yaji...
" mumy tace mikaje?
" maggi is to much ga kuma yayi yawa hmm kishiya Allah yahada kowa data gare!
" Amin
Assalamu alaikum
" Amina tace sannu da zuwa!
" baba sannun k'u
" ina yini baba?
" lpya lou..
" amina Zata sakko daga gadon...
" yizamanki yar albarka, Allah yakara karfin jiki!.
" Ameen Akace..
" kubani yar naganta, mashaa Allah nan yayi mata addua sannan ya mika kata...
" duk kunzo kunsata agaba kubarta ta huta mana!.
" Amina tasan halin baba da sauri tace baba dan lokaci daya..
" to shikenan..
" harisu ina office din?
" baba sai gobe zanje!
" Katashi ka tafi ga kayan ku chan sunzo, zaku rarraba Akasu imran ma yanata nemanka Amma wayarka bata tafiya!
" zan kirashi baba Amma sai gobe zamu raba kayan!
" kasan dai order dinku daya da alhaji yahaya shima yau zai raba idan ya rigaka kasan zakayi asara!
" baba kowa fa rabon sa yake ci..
" hakane! ne zan huce gidan farida..
" mamie tace bari mu tafi tare in mun dawo sai ka ajiyemu agidan Amina..
" Tohm..
" mumy takira su fadila suka tafi..
Haris yana dawowa yazauna kusa da Amina!
" sannu matata Allah yakara miki lafiya ina sonki ina kuma kaunar ki kice ruhin zuciya ta, yabata kiss Abaki...
" ya sunan babyn?
" asma'u sunan ummin ki nasaka!
" yauwa mijina nagode!
" ne zan gode miki domin kikekayi dawainiyar ciki gashi yanzu harkin haihu zaki shayar!
" babyn ce ta saka kuka nan haris yace Bata tasha..
" yaya zafi wallahi kuma ruwan nonon kadan yake zuwa!.
" common kibata mana!
" A'a..
" hannun sa yafara kokarin sawa a rigarta!
" haba yaya Dan Allah kabari a asubuti fa!
" to bata..
" ansar ta tayi ta saka hijjabi sannan tafara bata...
" au harda saka hijjabi wato nida Abuna...
" dariya tasa masu Abu manya..
" bari naji ya rubuta mana sallama!
" yaya kabari nakara kwana mana!.
" a'a wallahi sanyi akeyi tafiya zamuyi....
" tohm tace masa sannan suka yafara ibar kayan yana sawa a mota yana...
Lokacin da suka koma gida shiru babu kowa a gidan kayan ta yakai mata dak'i,
Amina ta samu guri ta zauna..
" yaya yace sannu matas..
" tasa dariya tace sannu mijin, yaya Ina su Amira ne...
" bari na kirawo su, waya yayi musu suka fito..
" rungume yake da inteesar a hannun sa!.
" in banda harara babu abunda suke jefan amina dashi..
" babu wacce tama ce mata Allah yaraya duk idanuwan su suka baza..
" haris ne yace gafa inteesae baku kar beta ba!
" Amira ce takarbi ta cikin kissa! Zuciyar tayi malolo..
" bilkisu ta amsa ta cikin towel tadinga mintsenin ta, kuka tafara yi...
" Amina duk jikinta yayi wani iri kamar tasan mitsenin ta akayi..
" haris ya anshita yana jijjiga ta amma batayi shiru ba!
" Amina ce ta fara bata tana sha duk a idon haris!
" yaya lafiya?
" nifa k'in rikirkita ne wallahi kinkara cikowa...
" hahaha..
" Amira ce ta katsesu naji kace kar ayi abinci take away kayi ne!...
" oh daman Amina ce tace kadan sannan tace kuma bazakuyi wahalar girka wa ba kuma kuke ce!
" aikuwa sai mun dafa wani!
" ke kin isa? Duk wacce tadafa wane abu ma to wallahi sai jikin ta ya gaya mata in bazaku ce Abincin ba ku kwana da yunwa!
" Yaya hadamun tea kaje!
" tohm but tashi kigoyan baby inteesar kinje...
" hahaha yaya goyo fa kace?
" kwarai kuwa!...
" ya shiga kitchen amina tace ninarasa wacce irin kiyayya kukeyi mun? Allah yaraya ma bakuce ba?
" mtseww kinje banza to zaa soki ba ballantana y'arki! Cewar bilkisu!..
" kimayi shirin ganin kaide da sharri kala kala!
" hmm wallahi kuna cikin duhu kusane wannan yarinya dana haifa kamar kuka haife ta ki dauketa tamkar taku!
" gaskiya baki da hankali, suka ja tsake sukayi tafiyar su..
" amina tarasa me tayiwa bayin Allah nan suka tsaneta goge hawayen ta tayi taje su mamie sun shigo..
" haris ya kawo mata tea tasha Haka suka dinga hira..
" wai ina abokanan zaman nake ne?
" suna dak'i...
" fadila tace Allah yatsareki daga sharrin su!
" Amina tace Ameen dai dan Wallahi ko Allah raya basu ce ba!
" karsu ce din inje asiya duk wacce tayi miki kice ubanta wallahi...
" amina tasa dariya muhadu muzama mahauka kike nufi to bada niba!
" mamie tace dadina dake hankali wataran sai labari..
" sai 11 suka bar gidan..
Pad ta canja tayi alwala ta karkade gadon ta ta saka kayan bacci sannan ta tofawa inteesar أُعيـذُكُمـا بِكَلِـماتِ اللهِ التّـامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْـطانٍ وَهـامَّة، وَمِنْ كُـلِّ عَـيْنٍ لامَّـة sannan ta kwanta!
" haris ne ya shigo yace au dan bakida tsarki shine bazaki kwanta kusa dani ba!
" a'a ne bance ba. .
" kwanciya yayi ya rungume inteesar...
Da safe Amina tayi wanka ta shirya cik'in duguwar rigar ta tayi k'yau! A hank'ali taje k'usa da Yaya tace dadyn inteesar bai masan tanayi ba, hannun ta tasaka a kirjensa ta dan shafasa..
" a hank'ali ya bud'e idon sa yarike hannun da take kokarin cirewa Yana kallon ta yace kidaina sakane a wani yanayi kinsan kuma kin haramta agareni na wasu kwanaki!
" kayi hakuri Yaya wallahi tun dazu nake tashin ka kak'i tashi, kuma lokacin tashin ka tayi fa!
" never mind wifey to in natashi what i my Going to do?
" opss office fa, karkayi late kuma kasan kana da orders da suke jiranka!
" I wish baki tashi ne ba! Zankira farouk nace ya rarraba!
" haba my husband shima farouk mutum ne kamarka kuma he also need to rest, yana wife yana kuma bukatar kulawa kamar yadda kakiye ayanzu, actually kuna nasu kudi is on fair kuna wahalar dana kasa daku!
" oh that's true oo bari na shiga wanka..
" inteesar ta dauka tana shayar da ita..
Assalamu alaikum..
" waalaik'is Salam tan fito palour dinta am hearing some voice kamar na grandy da khalil?
" yes sister mune, rungumeta yayi..
" khalil karka matse mata y'a man!
" haba grandy nayi missing din ta fa!
" ina kwana grandy?
" lpylou, barka aminatu barka Allah yaraya..
" ameen ta mik'a mata 'yar..
" gatanan kuwa kamar babanta ooo!
" i swear sai nan da 7days zantafi, wannan cute girl haka....
" hahaha yauwa broz...
" sister sunan ummi fa za'a saka mata wala kinaso wala bakyaso..
" Ai kasa am already in love with ummi name gashi nasamu baby girls so he named her asma'u, but inteesar za'adinga ce mata..
" yauwa thanks to uncle haris for naming her ummi's name!
" Grandy tace hope ba matsala? Kuma kin tabbatar anbinne mahaifar?
" eh sun bunne! But banida ruwan nono sosai!
" wannan ba matsala na tawo miki da Garin kunnun k'anwa kina fara sha ruwan nono zai sauka!
" tohm grandy nagode!
" haris ne yayi sallama ya gaishe su!
" grandy ta amsa ankuma samu karuwa Allah yaraya..
" Ameen goggo bari naje..
" Allah yabada sa'a
" Ameen..
Su Amira yagani a palour babu wacce ta gaishe shi..
Amina ce tace ina kwanan ku?
" dabamu kwana ba kya ganmu anan?
" bilkisu tace kekika kulata ma..
" you're still growing stupid! Common greating bazaku iya yiwa mijinku ba, to menene amfanin ku babu hakuri babu tawakkali, to let me tell u, I swear duk wacce tanunawa Amina hauka to zan rabo da'ita ne!
" kana nufin sak'i?
" Gashi kin fada!
" haba yaya magar bata kai haka na kayi hakuri,
" kuma grandy tazo so ku dura abinci da'ita! Ayi lemo a kuma dafa kaji!
" shiru su kayi..
" haris ne ya daka musu tsawa!
" to to munji ai..
" i won't tolerate any nonsence again u better watch ur step's..
" yana fita Amira tace idan baki fitar damu ba to mu zamu fitar dake wallahi..
" ku dai dunga tunani shine mafitar ku!...
" grandy ce tayi wa inteesar wanka, sannan tasaka mata kaya Amina ta an shita ta tofa mata arrahmanur rahim abakin ta!...
" Amina waccan ne kitchen din ko?
" A a grandy kiye ana dak'ina!...
" Saboda me?
" saboda abokanan zamana!
" tohm bari nayi anan..
Da daddare haris ya dawo yana cin abinci ya kira su, duk suka fito..
" Amina ta dakko inteesar sannu da zuwa yaya!...
" yauwa bani inteesar din..
" ya karbe ta yana tayi mata wasa!.
" ga kayan da zaku saka da sunanan blue and pink lace ne!
" Duk suka dauke nasu Hawa Sama yayi da inteesar Amina ce ta bishi...
" bilkisu tace wallahi bak'in lace zamusa,
" Gobe zanje na siyo mana bak'in..
" yauw gwara ki siyo mana mu nuna musu kararar bak'in ciki...
Yaya wallahi ne banason suna please kar ayi!
" kinsan me kikecewa kuwa meena?
" eh nasani mana...
" suna dai sai anyi!...
" nidai gaskiya banaso..
" kinga fitarmun adaki na huta...
" to bani natafi da inteesar din!
" babu inda zaki da'ita agurina zata kwana!
" bafa girke na baniba!
" fita..
Tana shiga daki ta zauna akasa tasaka kuka!
" wannan wane irin shashanci ne? A k'asan zaki zauna to ba'a zama ak'asa bakuma a yawo babu takalmi!
" saboda me grandy?
" saboda mace budewa take karayi!
" hawaye ta share wai nace haris yabani inteesar tunda ba'anan zai kwana ba!
" ke dai Allah yashirye ki! shine kike kuka? to ayir dinki ai 'yarsa ce..
" haba grandy duk fa wahalar cikin ni nasha..
" haka Allah ya dura mana mu mata sai dai kiyi hakuri tohm..
" bari naji na kwanta ina broz?
" yana gidan mamie...
Da safe Amira tasa aka siyo mata kifi kitchen ta shiga ta dauki k'ayoyin sa guda uku. .
" bilkisu tace mikikeyi a kitchen?
" hmm wannan yarinyar zan kashi!
" kisa fa kikace?
" ki tsaya kigane..
Amina tana zaune a palour haris ya sakko daga kan sama zama yayi kusa da'ita,
" ina kwana tace ba tare da ta kalleshi ba..
"Lpylou inteesar sai kuka takeyi gata kibata tasha..
" banza tayi masa..
" kokarin cirowa yakeyi ai naga komai na jikinki mallaki nane..
" Ne kadaina tabani bari naje nadawo sai na bata!...
" Mikewa yayi ya hau sama..
" ta ajiye inteesar a kujera ashe amira tana kallonta tana fita Amira ta bude bakin yarinya tazuba k'aya..
" Amina ce tafito agigice sak'amakon kukan dataje tanayi..
" haris ne ya sak'ko yana mikikaye mata? kasheta zakiyi, mota yahau ya surita sai asubuti..
" grandy tace Allah dai yasa lafiya Naga bak'i dadi da shiga dak'in ba ai!
" wallahi ban mata komai ba kuka ta saka ta dauki key din motarta directly tayi asubuti.....
*Urs Nana diso*
http//:nanadisoo.mywapblog.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/19/2016, 9:53 AM] Cvrieh sier verbier✨: _70-75_
*MATA NAH*
_NA NANA DISO_
Ta ajiye inteesar a k'ujera a she amira tana k'allon ta! tana fita Amira ta bude bak'in yarinya ta zuba k'aya..
" Amina ce tafito agigice sak'amakon kukan dataje tanayi..
" haris ne ya sak'ko yana mikikaye mata? kasheta zakiyi, mota ya hau ya surita sai asubuti..
" grandy tace Allah dai yasa lafiya Naga bak'i dadi da shiga dak'in ba ai!
" wallahi ban mata k'omai ba k'uka ta sak'a ta dauk'i key din motarta directly tayi asubuti....
Lokacin da haris ya'isa nurse ne suka kaita dak'in emergency Nan likitoci har uku sukayi kanta...
" Amina data rikirkice wallahi ban mata komai ba yaya!
" get out dallah aikin banza kawai wallahi in 'yar bata tashi ba wallahi sai na kaik'i Kara kotu!
" kakaine mana saime narasa kai wane irin namiji ne? Kuma bakasan kaddara ba kwata-kwata inteesar jaririya ce yaza'ayi na illatar da 'yata?
" Dr ne ya k'atse mata maganarsu I hope kune kuk'a kawo babyn nan?
" haris da yakasa magana yazata cemasa za'ayi ta mutu..
" Amina ce cikin rawar murya tace eh mu muka kawota!
" wane numfashi doctor yaja sannan yace kubiyo ne office!
" Da k'ayar haris ki tafiya hank'alin sa duk atashi,
" Amina ce tace haba yaya kaddara fa tariga fata kuma...
" kuma me yimun shiru kibarne da abunda yake damuna!
" dr ne yace haba maza u need to cool down known! Yanzu yarinyar nan ansaka mata kaya acikin wuyan ta wanda cikin ikon Allah bata shiga wuyan ba sai ta tsaya iya harshinta!
" haris yace wannan kukan da tasaka da gigicewar datayi shine zak'ace k'ayar bata shiga ba? To ma wanne azzalumin ne ya saka mata!
" wannan kuma tsakanin *MATAN KA* what am telling you anan shine kayar ce ta caki harshen ta kuma munyi iya kokari komai is normal munyi mata Allura ga magunguna can!
" Amina da i'd'on ta yacika da hawaye tace me nayiwa *MATAN KA* sun tsanine basa sona basa son farin ciki na? Kullum ina kokarin naga munzauna lafiya Amma su kokarin su cutar dani dukeyi? Rashin imanin har yakai ga 'yata tafashi da kuka!
" haris yarasa me zaice wane irin hakuri zai bawa Amina sai cewa yayi kiyi hakuri tashi mu tafi..
" suka anshi baby suka tafi haris a mota yana bawa Amina hakuri Amma bata kulashi ba, can sai cemata yayi karki cemusu ga Abunda ya faru!.
" wannan kuma ba matsalarka bace tafita daga motar tashiga cikin gidan dak'inta ta huce..
" Grandy ce ta miki sannu yar nan me yafaru?
" Amina tayi tsake wane irin mugun zalunce akaso ayimata datune 'yata ta mutu, kishiyoyi ko jaraba, ina dalile sun tsanine sun tsane ta idan gidan sukeso sai na barmusu wallahi kullum kokari nakeyi Amma kwakwata basa gani!
" grandy tace kince gidanku Amina nace kince gidanku kowa fa da irin tashi jarabawar....
"Haris ne ya karaso yace wallahi grandy na bata hakuri!
" Amina ta mike kaga dakata haris Abun ya ishine kullum da sabon d'a Namiji ga kishiyoyi ne abun ya ishine kunkaine bango in kagaje dane ka sauwake mun naje nayi rainon 'yata baza asaka min ciwon zuciya ba! Bed room d'inta ta shige ta....
" kayi hakuri haris daman mai hakuri bai iya fushi ba, idan ta sak'ko sai kakara bata hakuri....
" To yace sannan ya tafi part dinsa yana kwance idanun sa sunyi jajir Amira ta shigo my sugar naji hayaniya dazu lafiya....
" fitarmun daga daki!
" yaufa girke nane!
" kifita nace...
" cikin bak'in ciki tace to, haka tafita tana sak'i sak'i, ko yagani ne!.
"Sai da haris yayi wa Amina waya more than 15 bata daga ba!...
Da safe Amina tagyara dak'in sannan ta shiga wanka lokacin da tafito taje kamshin turaren haris da alama ya shigo ya fita ne!
"Amira tagama hada breakfast ba yarda batayi da haris ba ya tsaya ya karya Amma bai be ta itaba fita yayi..
" bilkisu ce ta bude baki me yahaduku da sweetheart ne?
" ke dai bari tub jiya bai kulane ne ba akasarima sai korata dayayi!.
" to ai nema bai amsa gaisuwa ta bafa ko!
" Amina ce tafito palour ta zauna babu wacce ta k'allah acikin su domin ranta a bace yak'e!!!
" khalil ne ya shigo sister ina kwana?
" lpya ba gurina kazo ba shine zaka tafi gurin mamie!
" haba yar uwa ai kinsan danke nazo garin nan kuma babu yara agidan nan gidan mame kuwa akwai!...
" To ai nema zan iya tayaka hirar!
" hahaha inteesar cute girl tayi kyau! Wallahi sak yaya haris! Lah ai ban kula daku ba ina kwana yan'uwa?
" da kyar sukace amin!
" Sister kinsan me yafaru jiya agidan mamie!
" a'a sai ka fada!
" Anty saddika takirawo duka yayansu suk'ace abinci tana ganina tak'i kulane! Nema ina zaune sai ga mamie da delicious ta k'awomin sai naji dadi,
" hmm ai shiyasa nace kayi zamanka anan!
" aa sister karkice haka itama anty saddika batasan ladan ciyarwa ba shiyasa!
" hakane broz!!
" amina ce takira surayya ki dafamin tuwo da kunu..
" ai ina kofar gidan ki!
" sallama sukaje sannun ku cewar surayya!
" amira tace uwar rok'o ba'a dogara da na miji ba gashi nan take gwalek'i..
" rufe bak'in Amira yato ya shigo da fulasai...
Surayya tace banda abinki Amira ai wanda yakeyi shi ake yiwa! Amina babu abunda bataima na ba!
" wannan kuma badake nake magana ba..
" Amina ce ta bar palour khalil ya bita surayya ta dauki kwanu kan ta shiga dasu!
" bilkisu tace kinga sun kwashi kayan dadin?
" ai yau girke na ne to bazan dafa komai ba idan my sugar yazo ya ansar mana!
" kwarai kuwa wannan ideas tayi..
" Amina ce taga grandy ta fito da jaka cikin mamaki tace ina zakije?
" ah ai tunda ban isa dake ba gwara na bar miki gidan...
" haba grandy menene yayi zafi haka DanAllah kiyi hakuri!
" haba aminatu agabana kika cewa mijin ki mutunci?
" haba grandy duk hakurin danakeyi yazakiga laifi na yanzu ma fa kofada bai musu ba!
" haba amina hakurin nan shine ribarki kuma rayuwar kenan wallahi hakurin shiyafe can-canta! abinda zai k'awo muku mafita shine kowa ya kudurce a zuciyan sa, k'an cewa idan wani ya faranta maka, toh lallai dole wani sai ya bakan ta maka, Saboda haka, abunda yafi dacewa ga kowannen mu shine, muyi kokari mu sanya hakuri cikin zukatan mu, mu zama masu yafiya, rangwame, da kuma uzuri wa juna, shi mutum Tara yake bai cika Goma ba, da yardan Allah komai zai wuce, kuma da sannu zamu ci ribar rayuwar mu da kuma zaman _takewar ku Komai yana da iyaka, idan watarana kaine, toh lallai watarana ba kai bane,Duniyar nawa take? Komai yayi zafi maganin sa Allah.....
" hakane Grandy cewar surayya..
" Amina tace nayarda nayi lefi Amma kiyi hakuri sai gata kwa tafi kinga jibe suna!
" jibe dai zamu tafi saboda makarantar khalil yanzu zanje gidan farida nayi mata barka taso muje khalil!
" to yar tsohuwa ta!!!
" sai kundawo...
" gaskiya amina baki kyauta ba mijin naki guda!
" nagaji ne wallahi rainin hankalin yayi yawa!
" Ai wallahi mazan nan sai hakuri..
" aikam..
" bani inteesar din! Mashaa Allah cute girl..
" bari nayi wanka nafito..
" tohm cewar surayya...
Bayan tafiyar surayya kawo adamu yazo tafito palour suka gaisa ya dauke inteesar yayi mata addu'a..
" kince sunan babbar yaya Allah ya jikanta!
" Ameen k'awu inasu anty fatima...
" ai na koreta gidan su!
" kawu kora fa kace?
" ah to me zanmata kullum batada magana sai na bana kula da yara na bana kula da'ita bansan damuwarsu! Nikuma dasu zanje ko da kasuwancen nawa!
" gaskiya kawu baka kyauta ba kuma duk avunda tafada gaskiya ne kunfi bawa k'asuwan cin ku mahimman ci fiye da matan ku!..
" saboda me kikace haka?
" Da farko dai kukan dage akan mace bata kulawa daku? Kuma ita mace yar tararraya ce yau kasameta bayan ta gaisheka ka tambayi ta menene matsalar ta..to fa kaima anjima zata tambayi ka menene matsalarka, indan kanuna mata kulawa kaso 20 ita 90 zatayi maka! Idan kadawo daga kasuwa kirawo yayanki cine musu me akayi musu a makaranta meke damunsu suna fahimtar karatu? Duk ka fahimce inda matsala take! Amma kadawo daga kasuwa katafi ka kwanta kawai burinku kusadu da matanku, da safe kayi ficewar ka baruwan ka da ya'yanka matsalar su data mahaifiyar su, k'anunawa 'ya'yan k'a so kanuna musu kauna suma su soka kayi musu tarbiya ka hukunta su in sunyi lefi matarka ka kula da'ita kanemi shawarar ta itama sai ta nemi taka....
" hakane Aminatu matsalar da wasu ke fama da'ita kenan, yau zan dawo da'ita kuma nagode 'yata..
" haris ne ya shigo suka gaisa da kawu yasamu guri ya zauna, nan yayi musu sallama yatafi..
" haris ya dauke inteesar sai wasa yakeyi mata..
" amina kuwa mikewa tayi tabar palour din..
" su Amira suka fito sannu da zuwa sweety...
" yauwa yanata fara'a wai ku bakwa ganin kamar mu ne!!!
" Amira tace kawai dai kayimana bori..
"Ai dole ayi muku tunda bak'uda shi....
" Allah zai bamu cewar bilkisu...
" Amira ina abinci nah??
" ai dazu surayya tazo takawo abinci kusan k'ula biyar! Shiyasa banyi girke ba banso adinga barnar abinci...
" to Ina abincin yake?
" waccan matar taka ta kwace ta kai dak'in ta!
" okay bari na anso mik'ewa yayi....
" bilkisu tace bafa zata bayar ba Amira!
" hmm haris fa yatafi ansowa..
" bakiga yanayin ta ba yau babu alamun mutunci?
" nagane ai..
" sallama haris yayi tayi masa banza...
" ke aka kawowa abincin ne dazaki kwashe...
" eh ne aka kawowa ai....
" haris ne ya dauke plate zai zuva..
" karka tabamin Abinci tunda ba girke na baniba?....
" su kuma fa?
" wallahi babu macen dazataci abincin nan!
" kin dauke karan tsana kin doramin to zan rabu dake bazan kara kulaki ba...
" da yafi ai, ka ajiye mun 'yata..
" bazan ajiye ba ai nema tawace yafita rai abace yanata masifa...
" ke Amira nan da minti goma ki dafo amin abinci if not wallahi saikin gane kuranki idiot kawai...
" bilkisu tasa dariya mai nagaya miki bazafa muci abincin nan ba!
Tun daga ranar haris baya kula amina tsanin shi da ita sallama da gausuwa sai kuma inteesar dayake zuwa yana dauka!
" Yau asabar anata shirye shiryen suna su mumy su mame duk sun cika, yan uwa kuwa ba'a magana daga gari daban daban!
" mamie kinga yaya bai kawomin din kuna na ba har yanzu!.
" to kikirashi awaya mana?
" wayarta ta dakko yak'i daukar wayar, mamie ban wayarki..
" ya akayi bai dauka ba?
" wallhi dont know!.
" hello yaya?
" menene?
" kayana baka...
" suna door dinki ta baya!
" to tace ta katse wayar..
" mike'wa tayi ta bude kofar tadauka nan tacire less din tasaka tayi kyau sosai..
" mamie tana shirya inteesar tace lallai haris yana ji daku ba gake ba baga yar ki ba!
" ai dukan mu ya siyawa..
" ya kauta kam!
Amina tana fita ta gag gaisa da mutane suna zaune mumy tace ina inteesar din?
" tana gurin baba mansurah!
" to ga shican rago da sa ya yanka...
" to mumy suna zaune su bilkisu suka fito sunsaka wane bak'in lace ko kyau basuyi ba...
" sannu mumy?
" sannun ku wannan bak'in kayan fa?
" bak'in cikin mu muke nunawa cewar amira!
" mamie tace kai amma hakan yayi kyau yadda zakuyi tayin baya ba!
" kallon ta sukayi suka fita waje yadda suka ga rago da sa haka hankalin su ya tashi..
" yanzu tayane mu kai dak'in baba me gadi? Cewar Amira..
" to bilkisu tace suna shiga Amira tace baba wannan ragon karka bari kowa ya dauka megidan ne yace in gaya ma!
" tohm hajiya angama..
Gurin karfe hudu anata cin abinci Amina ta canja kayan ta..
" Amira kuwa tarasa ta yarda zaa fita da naman!
" sakina ce tace Amina ba aga ragon da sa ba!
" nan baba asabe tafara masifa kowa ya taru awaje..
" baba mai gadi bakaga wanda yafita da ragon nan ba ??
" A'a hajiya Amira da bilkisu kuka kawo dak'ina!
" mumy tace amma kunje kunya wallahi Allah wadaran halinku!
" nan fa aka dunga masifa Amina ta fashi da kuka mamie kinga ko shiyasa bana son taron suna kwata kwata walhi....
" kiyi hakuri Amina Abunda Allah ya tsara dole sai anyi..
" hakane mamie tashige cikin gida..
Amira kuwa ta bude baki kishiya ko jaraba? Wallahi sai na fitar dake a gidan nan gwara na zauna ni kadai...
" baba asabe tace ohh 'yar nan da karfen hali kike Tun farkon al’amari, Allah (S.W.T) ne ya amincewa mace ta zauna da namiji d’aya a matsayin mijinta, namiji kuma ya auri mace hud’u idan ya samu iko, Ko shakka babu, Allah ya fi mu sanin hikimar da ke cikin hakan. Saboda haka babu abin da ya rage ma kowa face mi’ka wuya ga al’amarin Allah kai tsaye, Idan kuma akwai wata mai dabarar da take ganin za ta iya fitar da kanta daga wannan tsari da Allah ya tsara, ‘kila ta hanyar shiga malamai (Bokaye) ko ‘kullawa abukkiyar zamanta sharri, ko d’aukar matakin muzgunawa miji don ya saki wadda ya aura ko ya fasa auren wadda zai aura, sai mu ce “GA FILI GA MAI DOKI kuma *DUNIYA CE...*
" ai zan iya fitar daita din kuma kujera zuwanta gida ne zaa nunawa bambanci..
" ai sai kiyitayi yar nan duniyar kike gani da fadi, Mun dai tabbatar da cewa har a nad’e duniya Allah da hukuncinsa ne masu rinjaye akan kowa! Kuma bayan duniya akwai lahira! Ranar da Allah zai tambayi kowa abin da ya aikata a duniya......
" kinga kiyimun shiru ai badake nake ba??
"Banda ma jahilce irin nake cewar baba asabe Da kud’i da ilmi da mulki duka na Allah ne, ‘ko’kari da zafin nema ko rigima ba za su ta’ba sanya wani ya samu ko d’aya daga cikinsu ba sai Allah mad’aukakin sarki ya lamunce masa. Haka shima mijin da wata mace ta ke aure da shi ko za ta aura. Duk masifar da take tunani ko dubara da wasu shawarwari na miyagun ‘kawaye da za su iya ba ta domin ganin ta mallake mijin ita kad’ai, to babu wani tasiri da suke iya yi face idan Allah ya yarda,Ashe ko da mace ta wahalar da kanki tana ‘bata ma kanki lokaci, gara ki fara komawa Allah Ta’ala...
Bayan karfe 8 ko'ina angyara agidan!
" haris ne yashigo Amira yaji tana cewa bilkisu kinsan wane plan zamuyi yanzu?
" aa sai kin fada!
" to inteesar zamu sace sai mu kaita wane kauyen?
" haris ne yakarasa maganar da kije na sakike saki daya!...
" Amira kamar daga sama taje zancen tace saki??
" bilkisu data riga ta tsorata tarasa me zatace!
" Amira nan ta dinga kuka!
" Bilkisu kibashi hakuri mana!
" salan nema ya koreni nikinga tafiyata sai anjima..
" na shiga uku mamie DanAllah kisa baki, taga babu wanda ya kulata ta dakko mayafin ta tafita!...
" grandy tace menene haka? Harisu haba harisu...
" mamie wannan yarinyar itace annobar gidan nan...
" Amina ma kallon sa kawai takeyi takasa cewa komai..
" mamie kiyiwa Amina fada..
" kallon sa tayi sannan ta sun kuyar da kanta!
" grandy tace nagaya mata alhasan albasary (rahimahullah) yace:mumini mai haquri ne baya wauta koda kuwa an masa wauta, mai haquri ne baya zalunce idan aka zalunce shi yana gafara! Baya yanke wa zumunci, idan aka yanke yana sadarwa, baya rowa idan Akayi masa rowa sai yayi haquri..
" mamie tace kwarai kuwa hakaneh kullum ina gayamiki kidinga kokarin zama da mijinki kidinga faranta masa kinje?
" tohm inshaa Allah...
Yau haris kwata-kwata bai sak'ko daga sama ba shiru gidan su grandy duk jiya suka tafi!
" Amina ta saka duguwar rigarta ta dauke inteesar sai kamshi sukeyi tafito palour bilkisu ce azaune tana k'allo! Nace please haris yafita?
" bilkisu tace nema ke nakeso na tambaya ai!
" bari na hau sama na duba..
" inteesar ansha wanka bani ita na dauka!
" Amina tace A'a nagode Barta ma a hannu na!
" bilkisu sai ma taje kunya!
" Amina tana bude daki taga Haris a kwance tsigun nawa tayi har kasa ta gaishe mijina kagafarce ni abunda nayi maka! Kayi hakuri please yaya kaje!
" haba Amina yanzu 9 ace ban karya ba baka kulawa dani Bama kidamu dani ba to ne Aure zan kara!!!...
*Urs Nana diso*
http//:nanadisoo.mywapblog.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/19/2016, 9:53 AM] Cvrieh sier verbier✨: _75-85_
*MATA NAH*
_NA NANA DISO_
Amina tana bude dak'i taga Haris a k'wance tsigun-nawa tayi har k'asa ta gaishe sa! mijina k'a gafarce ni abunda nayi maka! Kayi hakuri please yaya kaje!
" haba Amina yanzu 9 ace ban karya ba baka kulawa dani Bama kidamu dani ba to ne Aure zan Kara!!!
Lok'aci daya taji ta shiga wane yanayi hawaye ne yafara wanke mata fuska tarasa ma mai zatace sai cewa tayi toh ina maka fatan Alkhairi!
" yauwa amina haka nakeso kidinga tawakkali da kuma hakuri!
" cikin kunar rai tace Na dai kara aikasan ina yi..
" any way tashi k'i soyan chips..
" to tace sannan ta mika masa inteesar rungumeta yayi yace my inteesar my heartbeat inasonk'i ina k'uma kaunar k'i ya cigaba dayi mata wasa...
" Tana gama soya masa ta kai masa k'an dining bilkisu ce tafito tace sannu da aiki uwargida maman inteesar!
" wane murmushi tayi sannan tace yauwa! Ga breakfast din nagama!
" okay tohm!
" haris yana sak'kowa yace weldone wifey suna karyawa haris yace kinga inna tashi karu aure tagare zan dak'ko muku!
" bilkisu da tea ki hannun ta sai data kusan kware wa tace what?? Aure??
" kwarai kuwa soon ma zan kara!
" Amina kinje mai yace?
" yeap to what i my going to do??
" thats good ai actually bakida kishi ko kadan yanzu in ya auro mana mayya fa?
" serously kidinga sanin words din da zaki dinga fada fata nagare lameri!!!
" ki inzaki jure to am not going to tolerate any nonsences!.
" haris ne yasa dariya u better watch ur mouth before i stand up! Let me All tell you idan baku nutsu ba! MATA 2 zan aure thesame time!
" bilkisu tsabar takaice kuka tafashi dashi Amina kinje WANE SABON SALON D'A NAMIJI! menene bama yimaka kagaya mana sai mu gyara!!!
" ba lallai ku'iya gyarawa ba ai!
" Amina da ta tsaya tana kallon su takaice da bak'in ciki duk ya ishe ta!
" dariya haris ya saka ai gwara na auro biyun kunga afi nunamin so da kauna! Da kamar gaske ayimun girke ayimun kwalliya! Kananan kaya akwati guda nasiyo muku Amma bakwa sawa, asamun Kaya afeson perfume with a big hug inzan fita!
" zamu gyara amma ka ajiye maganar Auren!.
" mikewa yayi yace impossible sannan ya fita...
" Amina gwara mu hada kanmu mudinga yimasa biyayya please!
" Amina cikin murmushi tace yaushe kikasan karatun biyayya? Ai ne nadadi inayi sai dai ko ke zaki fara yanzu! Kuma please mind ur business...
" Au haka zakice lallai kin nunamin ke makiya yata ce tunda kinaso ayimun kishiya!
" kinje rashin iya magana ayi mana dai! Hala baki fahimce maganar tasaba kishiya yace zai yimana not only u!
" tsake taja tashige dakin ta sannan ta rufe kofa!
Haris yana shiga office yatarar da farouk sai shirye shirye sukeyi!...
" yanaganku anan??
" tafiya fa ta matso Nan da 2days k'uma zamu iya yin wata fa!
" wai aine namanta ma bare naji office to, Bai dadi dashiga ba Farouk ya biyoshi...
" kayan da muka raba a kasuwa anfa samu faduwa!
" kamar yaya?
" kayan million 30 ne kuma million 29 muka samu!
" a'a u need to search kafin kace haka akwai na million goma gurin alhaji ashiru harsu kalissafa?
" Aine na manta ma banda su hahaha..
" yauwa nifa yanzu naje magana!
" hajiya DanAllah kije kibawa mumyn su haris hakuri wallahi inason mijina ina kuma kaunar abuna!
" Yimun shiru malama shashasha wawiya kowacce mace tana zaune gidan mijinta lafiya komai wuya komai dadi Amma ki kinsaka jaraba da hauka aranki to gaki ga duniyar ta'isheki ai!
" haba hajiya aikinsan sharrin shedanne!
" shedano ba shedan ba! Ke Alallai bakyason kishiya ke wacece? Sauran matan nasa da kika tarar ko su ba mata baniba? Kinsaka hassada da bakin ciki aranki mugunta kala kala to wallahi ki tuba zuwa ga Allah, ga wanke nacan ki tashi kiyimun wallahi in har naga kin fita kawunki zankira yazani mun k'e...
" haba hajiya wanke fa kikace aine ko agidana bana wanke!
" yau zan koya miki dan ubanki, banda sakarya ce ke ai ko vest din miji kya wanke ki samu lada kikara shiga zuciyar sa!
" ai sai ya raina ne?
" ai ya dadi da raina k'i...
" haba hajiya wai...
" tashi kiyimun abunda nasaki sha-sha-sha kwata kwata baki san menene aure ba to yanzu zan nunamiki yadda rayuwa take!
" wayyo nashiga uku cewar Amira!
" shiga ukun ki tukunna tashi ko na hambare ki!
" da kukanta tabar tsakar dak'in!
Mamie gaskiya abunda mijina yakeyi mun banajin dadi, bai damu daniba dagane har Yata hakuri kawai nakeyi!
" farida kicigaba da hakuri kinje kikuma cigaba da addu'a, rabuwar auren nan bata da dadi, rabuwar aure sai dole in mijinki baya sake ibada babu hanyar shiga aljanna to anan sai arabu....
" to mamie inshaa Allah, Amma kinsan baya dawowa gida da hure Sai gurin 11, ko hira bayayimun!
" K'uncin rayuwa fa dole ne, mutum yasamu kiyi hakuri da halin mijinki wataran sai labari Allah yana sani dake!
"Mamie kenan..
" ki daina kuka farida kuma fa da laifin ku farida!
manzon Allah (saw) Yaje sallah ta idi, kamar yadda yakeyiwa Mata huduba indan yaje sallar idi mata na zuwa maza na zuwa ya idar da sallah yanayi wa mata wa'azi yace;- yaku taron mata ku bada sadaka naga mafiya ya wanku a wuta kuke!
Suka me yasa haka ya rasulillahi?
Yace kuna yawaita zage...
(sai k'iga uwa ta dage tana zagen dan ta k'o shige k'o d'an isk'ah ko Allah wadai da kai tana fada sai kuga mala'iku sun amsa sai kuga d'a ya lallace)
Na biyu sai Annabi saw yace kuna kafircewa zaman tare (kafircewa zaman tare sai kuga duk alkhairan da yayi mata a duniya ta manta, kayi alkhaire dubu/dare ba ruwanta
,rana daya da idan taga ba'a siya abu ba ta dinga mita! Kaje ka kokarta kasiyo kaza sai ta dungure maka tazo tana gaya maka bakar magana awaje an gaya maka agidan angaya maka, to ta'ina mata zasu samu albarka?)
Mata suna da yawan zarge:- maza kuma bazuson zarge wane kafita dan ya dan samo muku abun dadi sai kuga yana dawowa ta rufeshi da masifa wai zai kara aure? Ku da ba'a aure za'a aure! ku?
" A'a mamie!
" to kinga yawancen laifin na mata ne! Mata suna tunanin ana mallaki miji ne ta karfe? To ba haka baniba shi d'a namiji ana mallakar sa ne da dabara da k'uma iya magana, da ladabe,to shi namiji yadda k'ik'asan tirela yake a hankali ake jansa! Namiji bayason ana al mabazzarance ko maggi bayaso yagani a kasa ba! Dan haka kiye hakuri da duk Abunda ya sameki kuma ya gifta miki! bare natsaya Anan kinga lokacin sallah yayi kije ku gaisa ki tafi...
Mahaifiya ta banda bak'in yi miki godiya bazan daina yimiki addu'a ba, samun uwa tagare yayi,Amma ki cigaba dayimun addu'a kinsan bak'in uwa!
" farida inayi muku zan dai k'ara akan ta da!
" yauwa mamie Allah yakara girma!
"Ameen
Bilkisu ce tace kwalliya ta saka pink din riga da siket tayi kyau sosai!...
" Amina da take faman gyara dining ta goya inteesar! Lok'acin da bilkisu tafito tayi mata kyau guri tasamu ta zaune tana giftawa sai kamshi!
" Uwargida yakika ganne nayi kyau ko?
" amina tace sosaima ai kyan ma ba'a magana!
" hahaha cewar bilkisu ai yau tsohuwar soyayyace zata tashi...
" bare naji nayi tilawa magriba tayi kinga!
" okay nema bari naje nayi sallah!...
" Amina tana shiga dak'in ta tafara lissafin ranar da zatayi arba'in...
" wanka tayi sannan tasaka wata doguwar rigar ta tayi daure ta dauke inteesar tayi mata addu'oin neman tsare!
" bayan sallar isha'i Arif ya shigo!
" sai kallon bilkisu yakeyi aa billyta kinyi kyau fa irin wannan kwalliya?
" Abunda mijina yakeso ko bana so adole nayi masa! Nidai fatana ka kasance cikin nishadi!
" Allah yayi miki Albarka!..
" amina taje ciwon maganar Amma sai ta kyalesu..
" hum yaya kayi sallah ne?
" yup ai alhamdulilah tunda naje abakin matata cewa sallar asuba'i da magariba tana daga cikin alamomin munafikai ga wanda baya yinta akan lokacinta!
" eh nema dazu ina karatu a umdatul ahkam acikin kitabul salat nayi kicibus da hadisin!...
" haris yace mashaa Allag ai haka akeso kullum adinga samun cigaba, mum intee?
" naam dad intee!
" Barakallahu fiyki..
" murmushi tayi tace Ameen cike da jindadi..
" gobe zanyi tafiya so ina rokon ku kuzauna lafiya kowaccen ku tasan zaman aure takeyi naso natafi da mum intee amma kuma tafiyar tamu under company take but next time be ready!
" okay nagode safe journey!
" bilkisu tace gaskiya zamuyi missing dink'a dear tafara k'uk'an munafurci!
" like wise!!
" Amina tace yaya yaushe zaka dawo da Amira?
" karki kara yimun zancen ta nagaya miki!
" tohm Sai da safe!!!
Bilkisu ce ta shiga dak'i Nan haris ya bita, kalaman da zasu kashe mata jiki yafara gayo mata my wifey kinsan Am in need..
" hugging dinsa tayi cike da soyayya nan salo ya chanj jinta tayi kamar a aljanna!.
Da safe haris ya shirya su farouk, Sai waya sukeyi masa! Ahaka sukayi sallama da bilkisu ya fito yana shiga dakin Amina akwance ya tarar da'ita tana chan duniyar tunani sai bakin sa taje anata azabure ta miki!
" yaya tun yanzu?
" wallahi meena flight din 10 zai tashi inteesar ya dauka sai sumbatar ta yakeyi! My intee i gonna miss u please ki kula da'ita! Mum intee yana ga kinyi shiru?
" dago fuskar dazatayi sai hawaye!!!
" to menene na kukan sokike natafi hankali na atashi?
" A'a tace cikin sarkar kiyar murya hannun sa yasa ya goge hawayen inason ki matata kikula mun da kanki please kinje, ga intee nan adinga bata abinci tana sha!...
" to cewar amina!...
" hug me sai nasan kina cikin murna!
" rungumesa tayi tare da fadin danAllah yaya ka kula da kanka! Kayi addu'ar matafiya kaje?
" karki damu mum intee duk zanyi.. wayace takara katse sa palour suka fita tana biye dashi..
" har mota suka rakashi yajiyo yace *MATA NAH* ina baku umarni da ku zauna lafiya!
To suka ambata!!
Tunda ya tafi airport yak'e tunanin intee wayar sa ya dak'ko ya k'ira Amina bugu daya ta dauk'a hello sweery?
" naam yaya kaga intee Sai kuka tak'e tayi!
" ohh my sweery kiyi mata wasa mana!
" haha kaganta dariya takeyi tayi yanzu!...
" yauwa, acikin room Dina ak'wai kudi na ajiye Sai ku raba kida bilkisu!
" okay!!! Yayana Allah ya tsaremin ka!
" Ameen sweery miss u dear!
Dak'in sa ta shiga lokacin da ta sak'ko bilkisu tana palour!
" Amina nifa banda ko sisi na manta ban gayawa mijina ba!
" murmushi tayi tace ga dubu hamsin!
" yeah yau sai shopping!
" kin tambayi shine?
" nop ban tambaya ba but ai yasan zamu fita kuma yau zanje gida fa!
" okay agaida su umma!
" zasuje!!!!
ke Amira fito ki dura girke!
" hajiya kaina ciwo yake!
" oo kina nufin ne zan dura miki dallah taso kafin na karyake?
" hajiya danAllah ki dura nayi nadare!
" k'in fito ne? K'okuwa sai na k'arya k'i ?
" cikin k'uka ta fito risho ta k'unna!
" me zan dafa?
" tuwo miyar kubewa! Kuma kiyi wanke wanke!
" cikin kunkune tace to!
" hajiya ce ta wanka mata mari! Ne kikeyiwa k'un k'une? To wallahi kikeyine nagaya miki dai!
" wayyo Allah wayyo Abbana...
" zakiyi mun shiru ko sai na zanek'i? Ai zak'iga k'in k'aso auren k'i, bari naji nayi bacci!
Sallamu alaikum!..
" lah bilkisu sai yau?
" walhi umma ina taso nazo Allah ne baiyi ba!
" to sannu da zuwa yasu Amina?
" tana gaisheki ma!
" to ina Amsa wa Amma bilkisu Dan Allah kije tsoron Allah ki zauna da mijinki lafiya kinje, Amina ba makiyar ki baciba har duniya ta nade tayi miki hallacci, karki manta da Alherin da tayi miki dan haka ku zauna da'ita lafiya kinje?
" umma inshaa Allah zan kokarta kuma zankai zuciya ta nisa!
" yauwa ga tuwo can a kitchen kije ki zuba!
" yauwa umma!
Ah bilki? Yaushe kikazo?
" Tun dazu nazo baba ya aiki?
" lpylou! Ya mai gidan nake?
" lpylou walhi yayi tafiya Amma ya k'usa dawowa!
" To a dinga hakuri da juna!
" to baba sai anjima!
Lokacin da Bilkisu ta isa gida jinta tak'eyi a cik'in farin cik'i waka ta kunna nan ta hau rawa!
" subhnlhi bilkisu daga dawowarki sai rawa?
" mtswe menene to mutum bazaiyi farinciki baniba?
" Ne bahaka nace ba Amma kuma ai ne kina cutar dani tunda banason kid'e kide please kirage volume din!
" gaskiya kina tak'ura min haba kibarne na sakata mana!
" ai kuwa karya kikeyi kice ina takura miki duk takura ai tabi bayan tsabar da kikayi mun!
" ne ban tsanike ba kidai kawai kinayen bakin ciki ne dan kinga zan haihu! Kuma gado ne saina ci ko kinaso ko bakyaso!..
" ke dakata naga bakida hankali, wayasan gawar fari?...
" yayana dai suna tafi dan naji amai amai nakije kwana biyu!...
" Alhmdlhi ai haka akeson ji!..
" hmm abaki ba!...
" sai dai a hanci hahaha..
Yau Amina tayi arba'in waya takira haris hello sweery hope ina cikin koshin lpy?
" Am fine dear!
" wallahi na matso na dawo am in need sosai sha'awa ta sani agaba!..
" yaya ai naga kana azumi!
" yauma nayi dear but shigarsu ta banbanta da taku kinga!
" anyway kaciga da hakuri!
" au haka zakice?
" to what i my going to see!
" Ina intee?
" tana chan tana wasa!!!
" ah lallai gobe by 8 nadawo fa!
" tohm amma yaya please yau zanje gida!
" nop ban amince ba!
" haba yaya Amma Bilkisu taje?
" da izinin wa?
" to gobe da safe zanje kaje!
" tohm amma by 2 kindawo!
" yauwa na yarda!
" yauwa sweery ta see u tomrw!
Hajiya nagama abincin naman duka za'a soya?
" eh duka zaki soya!..
" toh Amira tace sannan ta zauna akofar kitchen sallamar sakina taje!
" yauwa yar gari inata nemanki ina cikin bala'i!
" abun mamaki wai kinkaso auren?
" tsautsayi ingaya miki amma please gidan dan boka zakije min kinje?
" me zance masa to?
" so nakeyi nakoma kuma kishiyata a haukata min ita!
" laah ha'ila ha'illal lah Amira shidancin nake har yakai nan anya kina tsoron Allah! Amma sakina kin ban mamaki ke bazaki gayamata gaskiya ba!
" aa hajiya..
" zakiye min shiru ko sai na karya ki? Sakarya jahilai zuwa makarantar ku bata aikata muku dakomai ba! Akwai Wanda ake nema agurin shi Sama da Allah, boka dayake kazami mashiriki, fasiki, la'annane shi kukezowa gurinsa to wallahi kukuje duniya da rudinta ke kuma fita agidan nan kafin nafitar dake!
" hajiya kiyi hakuri...
" hakuri na shine karki kara hulda da 'yata...
" Amira garin fushi man kaskon ya wado mata akafarta wayoo Allah na hajiya kafata!
" Ai wallahi idan baki gyara halinki ba wallahi kina cikin asara kin maida mahaifiyarki kamar sa'arki ina zakiyi Albarka gaki ga duniyar ai ta ishe kuwa!!!
H
" washegari da safe Amina tatafi gidan mamie bata dawo ba sai gurin hudu haka suka shiga kitchen sunata girke girke sai gurin magariba suka gama!
" oh intee bakida rigima tunda muka fara aikin nan kina baya kinyi luf!
" Amina tayi murmushi tace nema haka nace ai bari muje mushirya! Wasu riga da wando Amina ta dak'ko yellow da rigar milk gaba daya tabi lafiyar jikinta intee ma shi tasaka mata sunyi kyau red lipsticks tasaka tayi turare adak'in tana cikin makeup taje an rungumeta! Jiyowar da zatayi taje yafara kissing dinta! Ture shi tayi yaya daga zuwanka!
" haba meenah ki dinga tausayin...
*Urs Nana diso*
http//:nanadisoo.mywapblog.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/19/2016, 9:53 AM] Cvrieh sier verbier✨: _85-90_
*MATA NAH*
_NA NANA DISO_
oh intee bak'i da rigima tunda muka fara aikin nan kina baya kinyi luf!
" Amina tayi murmushi tace nema haka nace ai bari muje mushirya! Wasu riga da wando Amina ta dak'ko yellow da rigar milk gaba daya tabi lafiyar jikinta intee ma shi tasaka mata sunyi kyau red lipsticks tasaka tayi turare adak'in tana cikin makeup taje an rungumeta! Jiyowar da zatayi taje yafara kissing dinta! Ture shi tayi yaya daga zuwanka!
" haba meenah ki dinga tausayina mana nifa mijin k'i ne k'uma ina buk'atar k'ulawarki!
" haba husby muje to kayi wanka kashirya! Bayan ya shirya ya sakko kan dinning..
" welcome back sweetheart!
" nasa miko lafiya?
" lpylou! Meena Ina intee ?
" tana bacci adak'i!
" actually kidaina barinta ita kadai yarinya ce fa!
" to yaya yanzun ma zumudin dawowar ka yasa na barta!
" hehehe ne dangatan Mata nah sai ma nacike ta hudun tukunna!
" bilkisu da ta hassala haba haris agaban mu kadinga cin fuskar mu! To gaskiya bazaiyi huba ke kitsaya kina kallon sa wai miji dadi? Tayi shigewar tq dak'i..
" meena itama cikin bacin rai tace gaskiya yaya baka kyautawa kishiyar lafiya?
" oh har dake? To aure sai nakara sai dai kuyi abunda zakuyi!
" babu abunda zamuyi, kuma ne matarka ce dolene nayi kishin ka! 'Miki wa tayi tatafi dak'i itama! Alwala tayi sannan ta kwanta!!
" haris yana gama cin abincin yace kowaccen ku sai na saita tah!
" gurin karfe biyu Amina taje mutum ya hargetso ta mik'ewa tafara kokarinyi nan yafara sarrafata kota'ina!
" yaya kayi a hankali..
" kibar ne please meena!
" Da asuba amina tayi wanka tayi sallah Amma shiru Haris bai tashiba,zama tayi kusa dashi yaya! Yaya!! Yaya?
" naam meena?
" katashi kayi sallah please! hadisai sunzo suna tsoratarwa kan Rashin halar asuba da isha a jam'i,Har manzon allah yace sune su kafi nauyi ga munafukai, kayi kokari ya kai mijina ka ceci kanka daga fadawa gungu munafukai da barin sallar asuba lokacin sanyi domin ba kasa sanda mutuwa zatazo maka ba! Haka nan hadisai sunzo suna bushara ga masu kiyeye sallar asuba a lokacinta cikin jam'i, malamai su kace wadannan hadisai sun kunshi kusan busharori goma ga masu kiyayeta...
k'aifa kace alamomin munafika tana ga wanda baya sallar isha'i da Azuba akan lokaci!
" afirgece ya mike am sorry dear bacci ne ya kwashe ne!
" to ne bari nayi al-azkar!....h
Da safe bayan yayi breakfast bilkisu tafito daga Dakin ta sai cin magani taketayi!
" haris yace ohh kina nufin nizan gaisheki?
" kaje dai gurin amaryar taka sai ta gaida ka!
" amina abun yabata mamaki wannan kishin irin na bilkisu akwai ban mamaki, ke bilkisu karki zama uwane haure-haure ba'a girmana miji sai cika baki!
" bilkisu da ta fahimce maganar amina sai ta zauna k'usa da haris tafashi da kuka ai kasan ina sonka mijina shiyasa nake kishin ka! Wallahi I love u...
" haris yaji dadin maganar Amma sai cewa yayi, meena anshi intee, kishiya dai bazan fasa ba so kiyi hakuri!..
" Amina tace sai kadawo yaya Allah Yatsareka!
" Ameen matata shiyasa nake son k'i!
" mtsw cewar bilkisu hala bakyajin zancen kishiyar da yakeyi?
" Amina tace labudda ma abarshi kishiyar zaiyi, akaina zata zauna kowa Aljannar sa yake nema ke da wahala bata isa ba sai kiyitayi!...
Haris yana fita yahadu da wane mutumi..
"Assalamu alaikum
" haris yace w/slm..
" barka da asuba alhaji, Dan Allah nazo kataimaka min kaje?
" bawan Allah wane irin taimako?
" wallahi Alhaji gurin aikina ne aka sallame ni yau sati daya kenan ina yawan samun abunda zan rufawa yayana da matanah asiri amma kullum Bana samu! matanah biyu uwargidan bata tausaya min, amma amaryar jiya ma dana koma gida kamar tasan banida kudi sai cewa tayi haba mai gida ka godewa Allah abisa jarabawar da yabaka, shekara nawa kana cikin rufin asiri dandai kwana bakwai? To kazo muje nina dafa abinci, Anan naji dadi sosai Amma sai uwargida ta fito tana cin zarafin mu!...
" subhnlhi, yanzu bawan Allah mikakeso ayi?
" Alhaji aiki nakeso duk da inada master's ko wanne kasamar mun zanyi murna!
" haris yace yanzu dai banaci komai ba! Sai zuwa gobe innayi tunani..
" Allah yasaka da Alheri! Nagode nagode..
Hajiya hajiya??
" Amira lafiya tunda an miki tofin ai shikenan..
" haba hajiya Kidinga tausayi na kidinga tunawa ne yarki ce dubi yadda na k'one??
" Ai duk wanda baibi iyayen sa ba yana cikin nadama da kuma asara! Yadda kika k'one kina ganin gurin babu kyan gani, to na tabbatar zuciyar ki haka take! Kuma yadda kika kwana kina kuka saboda azabar konewar da kikayi haka zaki kwana kina istigfari sai zuciyar ki tayi fari!
" wallahi hajiya na tuba!...
" ai ina lure..
Bilkisu naje shiru baki dura abincin rana ba lafiya?
" Amina cikina ne yaketa ciwo bakiga ko fitowa palour banyi ba?
" nagane Allah yasawake kinje kukan intee bari naje..
" addu'oi Amina tayiwa inteesar sannan bacci ya kwashe ta!
" kitchen ta shiga ta dura musu taliya gurin 6 tafito tayi sallar isha'i sannan ta zauna tana tilawa..
" oh karatu kikeyi?
" rufe kur'anin tayi tamike sannu da zuwa yaya!
" yauwa ina bilkisu?
" tun rana batada lafiya ciwon ciki takeyi..
" subhnlhi bari mu tafi asubuti..
" ufan bata iya cewa suk tafi, sai da suka jira numbersu tazo sannan suka shiga!
" what wrong with her?
" stomach pain!
" okay taje ayi mata test da scanning!
" mik'ewa tayi ta nufi dak'in test din, bilkisu bari naji nayi sallah kafin nadawo angama ai!
" to mijina tana shiga room of test din zuciyarta sai sake sake takeyi ko ciki ne! Cikin 30 min aka gama yabata result gurin Dr suka koma..
" Dr yace mashaa 'Allah babu abunda ke damunki it seem like period zakiyi soon so kikeyaye sweets..
" yauwa dr thanks suka nufi gida, a mota bilkisu ta fashe da kuka, haba haris ne yaushe zan haihu ne ne wallahi nazata cikine dani!
" Bilkisu watch ur mouth karkiyi sak'o wane irin magana ne aikinsan haihuwa daga Allah ne kiyi tawakkali kowa da irin nashi kaddarar kuma continue praying ur children are in the way..
" shiru kawai tayi masa ta cigaba da kuka!
" Suna i'sah, inteesar sai kuka takeyi, Haris yana shiga ya dauketa!
" me yasata kuka?
" Wlhi dont know kawai rigima takeji..
" ruwa ta bata sannan tayi shiru, bilkisu sannu Allah yakara sauke!
" Ameen tace sannan tayi shiru..
" yauwa daman inason magana daku, dazu wane bawan Allah yazo akan na nemasa aiki, ne kuma ina tsoron mutane da sharrin su!
" Amina tace idan kanada halin taimaka mai kataimaka mai, kamai Allah wataran zai taimaka makah, kuma kadaina jin tsoron komai Allah kiyin komai arayuwa...
" bilkisu tace yanzu haka yana cikin wane hali kuma nasan akwai mata da 'yaya!
" to zanyi bin cike akansa!
" yauwa mijin mu Allah yakara bude ya kuma taimaka!
" Ameen mata nah
Mumy ce tayi sallama tashigo cikin gidan Bilkisu ta rar azaune tayi tagume sai da tayi sallama sau biyu sannan ta Amsa lafiya bilkisu?
" lah mumy banjiki bani ina wuni?
" lafiya lou..
" Amina ma tayi sallama ta durkusa ta gaisheta..
" inteesar hat tayi wayo kenan?
" ai mumy tayi fushi sai yau kika tuna da ita!
" hahaha Ayimun afuwa to..
" bilkisu batasan lokacin datace nema Allah yabani ba!
" Ameen Amina tace..
" oh bilkisu ashe abunda yake damunki kenan, kin manta shekarar amina nawa bat ahaihu ba? Kiyi hakuri komai lokaci ne..
" hawaye ne ya wanke mata fuska mumy danAllah kiyiwa haris magana kada yakara aure!
" aure kuma? Aine bai sanar dani ba, da zuma muna tare..
" Allah mumy yace aure zai kara!
" karki manta manzon Allah saw yace:-mamaki ga al'amarin mutum musulmi, al'amarinsa duka alherine, idan farin ciki ya sameshi sai ya godewa Allah sai ya zama alheri a gareshi, in ciwo ya sameshi sai yayi hakuri hakan ya zamar masa Alheri,/muslm/ Dan haka koda kishiyar zaiyi muku kudai kukasance masu hakuri masu kyautatawa miji komai zai huce..
" to mumy mungode..
"Sun fita kenan zasu raka mumy sai wane yaro ya tsaya, bilkisu tace kai lafiya?
" yace danAllah anty ki taimaka min da Abinci yunwa nakeji..
" bilkisu tayi tsake dallah tafi kabani guri..
" kai zo cewar Amina Amma gaskiya baki kyauta ba maraici ba abun gudu bani ba kana ganin dan nan kasa maraya ne kuma An karb daga Abdullahi bin Amr rta Hakika wani mutum ya tambayi manzo saw
wane Aiki ne mafifici a muslunci?
sai manzon ALLAH yace:shine ka ciyarda
Abinchi {ga mabukata} sannan kayi sallama ga
wanda kasani dwanda baka sani ba/Bukhari da muslimu suka Ruwaitoshi/
" mumy wannan shine zaman amana kana tunatar da dan uwanka falalar bautawa Allah!
" Amina tace ai mumy muma haka muka tashi munayi ana gyara mana!..
" bilkisu tace kayi hakuri kanina bari na dakko maka Abincin..
" haris yana tsaye daidai kofar gidan sa! Wannan bawan Allah yayi masa sallama cike da murmushi afuskar sa! Alhaji ina fatan kayi shawara!
" ya sunan ka ne?
" ilayasu sunana ina zaune a medile..
" haris yace me zai hana kadinga neman taimako agurin mutane!
" Alhaji banki nace abani ba sai dai kuma wane hadisi da naje Annabi (ﷺ) Yace: " 'Dayan ku yaje yayi itace ya goyo shi a bayan sa shine yafi masa alkhaire fiye da ya tambayi wani,ya bashi ko ya hana shi/Bukhari 1968, Muslim 1042/ shiyasa nafison nasamu aikin..
" tabbas haka yake kuma inshaa Allahu zan dauke ka aiki acikin company dinmu!
" nagode nagode sosai Alhaji..
Hajiya hajiya Dan Allan kiyi hakuri kinje!
" hajiya banza tayi mata!
" cikin murya tausayi tafara karatun Alkur'ani *سُبْحَانَ الَّذِي أَسْرَىٰ بِعَبْدِهِ لَيْلًا مِّنَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ إِلَى الْمَسْجِدِ الْأَقْصَى الَّذِي بَارَكْنَا حَوْلَهُ*Ma'ana: Tsarki ya tabbata ga wanda yayi tafiyar dare da Bawan sa da dare daga masallaci mai alfarma zuwa ga masallaci mai nisa wanda muka sanya albarka a gefensa..
" ya dai fiyi miki kidinga karatun al'kurani, Duk abinda kakeyi kasa tsoron Allah, Kuma ka ji tsoron ranar da Allah zai kamaka!
" hajiya kiyafemun kinje nadaina komai..
" wai Amira tazo ana kiranta..
" toh kace ganinan!
" hajiya bari naje naji wanene!
" tohm Allah yayimiki Albarka!..
Tana fita daga idon da zatayi taga haris ne!
Batasan lokacin data rungume sa ba kayi mun afuwa mijina wallahi nayi kuskure!!
" Amira haka kika dawo??...
*Urs Nana diso*
http//:nanadisoo.mywapblog.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/20/2016, 11:31 PM] Cvrieh sier verbier✨: _90-95_
*MATA NAH*
_NA NANA DISO_
Wai Amira tazo ana k'iranta..
" toh k'ace ganinan!
" hajiya bari naje naji wanene!
" tohm Allah yayimiki Albarka!..
Tana fita daga idon da zatayi taga haris ne!
Batasan lokacin data rungume sa ba k'ayi mun afuwa mijina wallahi nayi kuskure!!
" Amira haka kika dawo??..
Mijina ka taimaka ka mai dani gidana na tuba na kuma gane kuskure ne...
" aa amira babu alamar nadama acikin idonki wahala ce tasa kika fadi haka!!!
" haba my husby please help pls ka tausaya min!
" any way bakomai Amma idan kikace zaki hadamun fada kamar na bayan to..
" my sugar kadaina fadin haka..
" namai dake tun lokacin dana sakike nabarki agida ne dan ki kara hankali kikuma san rayuwa to yanzu Alhamdulhi hajiya ta kokarta muje na gaisheta...
" ta kada masa ido to kayi alkawari yanzu zaka tafi dani?
" muje dai tukunna...
" sannu da zuwa sannu da zuwa ashe kaine agidan namu?
" nine hajiya ina yini?
" lafiya lou, kardai kace kome kazo?
" eh hajiya shinazo!
" to gatanan abundai bakamar da ba sai dai acigaba da hakuri kuma kadinga yimata fada kaima..
" toh hajiya inshaa Allahu...
" to ke sai kitashi kibi mijinki ku tafi kuma wallahi kar naji karna gani ki zauna da kowa lafiya domin kun riga kun zama *MATAN SA* ke guji mugun halin da bak'in kishi, in zakiyi kishin sai kiyishi mai ma'ana rige rigen farantawa miji...
" inshaa Allahu hajiya zakiyi mamaki na!
" to hajiya sai anjima..
" au har zaku tafi gashi ko ruwa ba'akawo maku ba?
" bakomai nagode..
Suna cikin mota suna tafiya Amira ta daqo idon ta ta kalle haris cikin sanyin murya tace mijina abin kaunata, bansan irin kalaman dazasu isa ga nuna godiya ta gare kaba, wallahi inajin dadin zama dakai fiye da komai ina tsananin godiya ga Allah daya zabamin kai amatsayin mijina kaine mutum na farko da ka chanja rayuwata!..
" Amira wannan kalaman nake ina mutukar jindadin su, suna kashe mun jiki sosai, shiyasa kike shiga raina kuma kin kwanta male male shiyasa banazan iya rabuwa dake ba..
" murmushi itama tayi har suka karasa gida bilkisu suka tarar a palour sallamar su ita taja hankalin ta! Cikin mamaki tace Amira?
" Naam bilkisu ya gida?
" lafiya..
" haris yace ke tafi dakinki ke huta!
" to Amira tace sannan ta hau sama..
" billy ina mum intee?
" kamar garden naje tace zataji..
" Juyawa yayi hanyar fita yana zuwa garden din yaga tana skippn cikin mamaki yace mum intee?
" yes yaya me yafaru?
" mikikeyi haka?
" wallahi dear am tired of this fat so nake na ragu!
" matsowa yayi kusa da'ita kallon juna suka farayi sannan yayi hugging dinta, nafison ki da kibarki so babu wane slimming ko'ina nake yana burgene look at know yadda kikaye kyau ko'ina is full!
" kai yaya please kabari ta saka dariya..
" aa tun safe na lura fa kina cikin farinciki?
" tabbas hakane domin jina nakeyi nafi kowa!
" kamar yaya?
" murmushi tayi ta taba bakin sa sannan tace miji mai kaunata, ga mumy yanzu tazama kamar ummi na!
" shikenan farin cikin nake?
" ga Allah ya azurta ne da Abunda nadadi inaso wato inteesar!..
" dariya yayi yamatso kusa da kunnan ta yace kwanan nan za'ayiwa intee kane!
" aa nefa ba yanzu na har yaushe na haihu?
" haba mata ta kinsan fa yadda nakeson 'ya'ya!
" nifa kome zakace inteesar ta isheni..
" hmm tawo muje kinje tana wane mammanne masa suka shiga daki zuciyar amira kamar tacere dakyar tace ina yini?
" sannu da zuwa amarya yasu hajiya?
" lafiya
" bilkisu kuwa ko daga kai batayi ta kalle su ba saboda kishi..
Bari Na shiga kasuwa akwai kayan da zank'ai!
" yauwa yaya kasiyo fruit da salad please!
" bilkisu tace mai ma yakare fa..
" yaushe aka kawo mai din? Ko to weeks ba'ayi ba gaskiya adaina barna da kayan abinci..
" haba my sugar banda abinka tunda amfani ake dashi ai sai ka gode Allah!
" actually bazan kara maimaitawa ba adunga tattala abinci adinga sanin darajar nema kuma!
" inshaa Allahu cewar Amina..
" intee yaje ya dauka daga nan ya huce kasuwa!.
" Amina zata shiga dak'inta kenan amira tace mum intee?
" Naam ya akayi?
" bilkisu tace pls have a set mana..
" Inajinku to..
" gaskiya kirage soyayyar dakike nunawa haris afili kibare sai yashiga dakin ki! Cewar Amira..
" bama wannan kimin ciwo ba shigar da takeyi any how girken ki ne ba girke bani ba Amma u dont mind!
" Amira tace tayaya miji bazai dinga marmarinka ba yana ganinka da irin kayan nan gaskiya kichanja kina shiga hakkin mu kuma Azo ayi magana daga karshe yazama fada!
" Amina ce tayi shiru na dan lokaci sannan tace ince dai kuma matansa ne?
" kwarai kuwa cewar bilkisu!
" to naga kowa zaman samun aljannar ta takeyi? Idan ku baku farantawa mijinku ba nima sai naki faranta masa? To banda karfin hali irin naku da wacce na hana saka kananan kaya kokuwa nataba yimuku magana dangani da shawagwaba ga mijinku! In kunje haushi sai ku kwaikwaya tunda farantawa mjinku zakuyi! Kaya kuma nasaka kuma zan cigaba da sawa indai har ba shiya umarci ne da indaina ba!
" Amira tace Amma gaskiya Amina kina kwace mana miji..
" kwace muku miji??? Ku bari kuje bansan ma hanyar malami ba Amma nasan hanyar tsayar da sallah da kuma biyayya da miji sai kuma kubi ku kwacha...
" zakiga abin mamaki ke riga da wando kike sakawa to mu da mini siket zakigan mu!!! Cewar Amira..
" wow thats fantastic indai kinye ne dan ki faranta wa mijinki bana ce miki komai kallo ma sai naga dama zanyi miki, dak'inta ta shiga....
" tabarsu cikin duniyar tunani bilkisu tace ai gaskiya tafada sai anjima kowa ya kama mijinsa...
Mamie tana palour ta azaune! Muryar baba taje ko sallama baiyiba Alamun masifa yakeyi..
" baba lafiya kake ta masifa nagaji kijawa farida kunne in bahaka ba wallahi har gida sai naji naci mata mutum ce bata ganin mutuncin mijinta!
" me kuma farida tayi namiji da baya rasa hade..
" na dai gaya miki in ba haka ba wallahi zance masa ya kara aure!
" haba baba aure fa kace 'yarta ka?
" to menene ai sai ya aure wacce zata kula dashi!
" yi hakuri zan mata fada ayi hakuri...
Bayan fitar baba mamie takira farida mekikayi masa? Yanzu farida da bakiyi fitina agidan mijinki ba sai yanzu da ke zanje ko da rayuwar duniyar zanje?
" haba mamie bafa ya dawo gida sai sha biyu kuma mata suna kiransa awaya, shiyasa nayi masa rashin mutunci, wallahi nina gaje da auren!!
" lah ilah kingaje? Kifito kiyi uban ne? Mudunga jira kafada muna hawa masai daya ko kuma kisane agaba kina damuna? Kowacce yarinya akayiwa aure tsit kikeje, kowa yasamu ya shiga rufawa kansa asiri yakeyi babu! Kokuma wane abun kikafara shane??
" haba mamie Allah ya tsarene..
" ke yar kissar nan ta mata baki iya ba hakuri ai shine zaman aure! Kifito kina yawo agari ana tsine miki ana zagen mu! Kinsan dai kinada yayye sai na hadaki dasu wallahi..
" to mamie inshaa Allahu zan gyara Amma shima kiyimasa magana!
" zan masa, ko kefa kidinga koyi da halin Amina ga kishiyoyi ga matsalar miji Amma dif kikeje tayi shiru!
" tohm namie sai anjima mamie...
Amira ce tashiga ta dura girke sai gurin magariba tagama dak'inta ta shiga wanka wata duguwar abayarta tasaka sannan ta kwanta!
" bilkisu da Amina sai hira sukeyi intee sai dariya takeyi, haris yana dawowa yace abinci lafiya Amira bata sakko ba?
" Eh muma tun data gama girki rabon mu da'itah okay bari naji..
Yana shiga wanka yayi yayi shirin bacci Amira yagani akwance tanata bacci ahankali ya tashita Amira kinye sallah??
" mikewa tayi tace ai ba'ayi magriba ba!!
" haris ne yarike kansa amira yaushe zaki gyaru?
" am serious fa yan zu na kwanta!
" haba Amira kin huce matak'in wasa da sallah wallhi sai kace yarinya sallah fa ba abar wasa bace ba itace farkon za'a tambayi mu akabarin mu dandai 20mn? Haba Amira gaba fa yaya zaki haifa kuma kinaso suzama nagari!
" mijina kenan nagode bari nayi Alwala to..
" sallama sukayi dasu Amina sannan ya koma dak'in Amira ganinta yayi da atamfa..
" Amira kidinga saka min kayan bacci please!.
" kallonsa tayi tace karka damu mijina dag yau!..
" yauwa my sugar!!
Da safe Amina ta gama yiwa intee wanka taje Amira akofar dak'inta tana cewa..
Ke karamar jaka! Mai bin boka fito yau sai anyi wacce za'ayi....
*Urs Nana diso*
http//:nanadisoo.mywapblog.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/27/2016, 11:14 PM] Cvrieh sier verbier✨: _95-100_
*MATA NAH*
_NA NANA DISO_
Da safe Amina ta gama yiwa intee wank'a taji Amira a k'ofar dak'inta tana cewa..
K'e k'aramar jaka! Mai bin boka fito yau sai anyi wacce za'ayi Dan rashin mutunci duk kingama da mijin mu..
Bilkisu ce tafito lafiya masifa da sassafe? Lpya amira?
" kinje wane rashin mutunci bilkisu wai da Amina da yarta zaiyi tafiya wannan ai wulakanci ne shiyasa nace gwara ayi wacce za'ayi idan ma asiri tayi masa gwara yakaryi!
" lallai kina cikin wahala Amira!
" ke dai kike cikin wahala amma badai niba kuma ni dole na kwace hakkina!!
" Amina da take cikin dak'inta shiru tayi tana sauraran ta hawaye ne ya cika mata i'donta! Chan kuma ta ink'ayi muryar haris yana wato baki shiryu ba kenan? Bashiri amina tafi ta kalli yadda Amira take faman huce...
" ai indai akan wannan matar takace to bazan shiryu ba...
" atake zai kai mata mari Amina ta rike hannun sa! Haba yaya ai abun bai kai na mari ba, tafiyar takeso kayi da ita shine tarasa ta inda zata gaya ma!
" ina ai Amira batada hankali amma kibarta nayi maganin ta!!!
" haba dady intee kaji intee tana kuka dak'in suka shiga a tare ya dauke intee..
" wallahi indai zaman gidan nan kikeso to ki raba kanki da Amina, kuma ke banda abinki bakisan Amina ta tsane ayi tafiya da' ita ba, kuma gamawa da miji tariga tagama bakiga yanzu cikin siyasa tabi ba ke kintsaya kina hauka ita kuwa a nutse tayi magana cikin kissa..
" ai abunne ya bani haushi wallahi....
" ohoo miki dai kije kiyi yadda kikeso lokacin da zaiyi waje dake babu mai bashi hakuri...
" Amira ce ta zauna akan kujera tarasa me keyimata dadi yanzu ita ta'ina zata fara basu hakuri!!!
Amina ce ke kallon haris babu shiri idonta ya ciko ahankali haris ya saka hannun sa domin ya goge mata hawayen..
" rike hannunsa tayi cike da kallon cikin idon sa yaya wallahi bana bin malamai bansan hanyar su ba amma me isa amira take zarge na???
" amina kedaina saka kanki a damuwa amira bata da hankali kuma nasan halin ku tun kina yarinya..
" Amma su sun kasa fahimta ai danAllah kasanar dasu wallahi ne bantaba nufar wane da sharri ba!
" Amina Amina!! Ke macece da kowanne namiji ya kamata ya mallaka! Kina hakuri da abubuwa da dama kina bani hakkina kina sona kina kuma kula dani abunda yake kuma jan hankali na bai huce gyara da kuma hakuri da halina da kikeyi kuma kin zauna Da *mata nah* lafiya...
" kazama abun alfahari a rayuwa ta! Ina sonka mijina ina kaunar ka uwa uba ma bansan yadda zan misilta son danake maka ma! Cikin kuka ta rungume shi...
" bakin sa yake kokarin kaiwa nata nan da nan taja baya..
" bafa girke na baniba?
" dan nayi kissing nake lifine?
" Amma dai me..
" amma dai me actually am in need so be ready to night ayiwa intee sister...
" ni ba yanzu ba ta shiga toilet..
" intee muahh sai nadawo..
Lokacin da ya isa office mukhtar ya tarar, ya akayi maza...
" gaskiya haris kabatan rai 3 hours ina jiranka kashanya ne!
" am sorry maza kasan yanzu *Mata nah* basa sakena da huri kai maza aure is sweet ooo...
" mukhtar yasa dariya sai yanzu kasan haka..
" ai indai Allah ya hadaka da mace tagare to yayi maka babbar ni'ima...
" ai gashinan sai tumbi kakeyi nema kuma matata tana kula dani sosai...
" Bani files din nacike zan shiga market anso kuda din nan, ya kaga sabon members?
" yup zancen sa zanmaka hes so nice fa yama anso kuda din ya cike some files..
" kai haba dai ....
" yes am serious...
" good thats what we want barakallhu fihm..
" oga sai anjima akwai inda zanje..
" okay bye!
Amira ce ta shirya zataje asubuti takira auwal awaya amma bai dauka ba, dak'in Amina ta shiga da sallamar ta, mum intee please aron key din motarki zaki bani!
" okay gashi but babu mai sosai aciki..
" no prob zan tsaya nasaka thanks...
" a hanyar ta ta zuwa asubuti ta shiga tunani lallai Amina daban take dan indai itace wallahi bazata bayar da aron mota ba, hmm tace tayi packing din motar number ta ansa ta zauba jiran shigarta kamar daga sama taga Alhaji nata yayi baki ya rame..
" hankali tace anya wannan Alhaji ne?
" juyawar dayayi yace Amira?
" Naam ina yini??
" zama yayi yace ya barikin?
" subhnallahi barikin lafiya alhaji ai natuba tuntune yanzu ina gidan mijina ....
" Alhamdulhi naji dadi dajin maganarki kiyafemin duk abunda na taba yimiki arayuwa DanAllah danAnnabi domin nine sanadin lallacewar ki yau gashi ta faro da diyata!
" me yafaru alhaji gaba daya ka canja kayi baki kamar bakai ba?
" wato Amira duk abunda akace zunubi ne to yakamata mutum ya gujeshi zina ba abar so bace kuma tana cikin alkaba'ir aikata zina tana rushe ibadarka ta shekara saba'in, kuma annabi ya hanemu da aikata ta, yanzu ke duba ke gani yata nayiwa aure ranar da akakaita yan fashi suka shiga suka yimata fyade gatacan an kwantar da'ita...
" innalillahi wa'inna illahir raji'un Allah ubangiji yayafe mana..
" ki zauna da mijinki lafiya kuma kuyiwa wasu fadan saka kaya masu fito da siffofin jikin su, abunda yafara rudata kenan kuma kukuje abun duniya mutuncin ka yafe kudinka duk namijin da yake yawan kallon surar jikin ki to wallhi kuna cikin matsala domin ahaka shedan yake rudar al'umma zunubin zina daban ne...
" hakane alhaji inshaa Allah zamu kiyaye yanzu nema kayafimun danAllah...
" nema na yafe miki bari naje na buga buga naga kozan samu kudin magani?.
" alhaji wai kana nufin ka samu karayar arzuki ne?
" Amira zina nace Miki gashi yanzu takarar dani astagfirullahi Allah ya yafemana natuba, kikalle tufafin jikina...
" kuka tafashe dashi ciki da tausayin kanta tace Allah ya ganar da wayanda basu gani ba Allah ya shiryemu ga dubu 5000 nan ita kadai gari ne kasiya mata magani...
" amira ba ayi haka ba?.
" nema kanwata ce....
" nagode...
Lokacin data koma gida bilkisu ta tarar a palour har kindawo?.
" nadawo ban ma samu ganin likitan ba, intee ce ahannun ki?
" eh itace gata azaune muna wasa..
" aikam uwar fara'a..
" Amina ce tace sannu da dawowa..
" yauwa ga key din..
" okay
" Amina akwai abubuwan da Arayuwa sai kayi hakuri idan mutum yayi maka nayi miki abuvuwa da dama nakuma gane kuskurw na yanzu ki gafarceni zamu zauna tamkar ya da kanwa inshaa Allahu...
" bakomai ai abubuwan ne sukeyi mun ciwo wane sa'in niban zauna dan nakuntata muku ba Amma kwata kwata kunki kugane wataran, kuma biyayya ce tasa kuke ganin kamar asiri nayiwa haris, narasa gane kan mutane in biyayya tayi yawa ace kagama da miji inkuma kaki kulawa dashi abarka abaya!
" to nidai kiyafemun zan zauna da ku kishoyoyi na tsakani na da Allah..
" Allah yabamu iko bari na dura girke..
Bata bar kitchen ba sai kusan 7 tana gama jira abincin a dinning ta anshi intee a hannun bilkisu sannan ta shiga yin sallah..
" lokacin da haris yadawo direct dakin Amira ya shiga zai dauke wasu takardu..
" sannu da zuwa my sugar..
" yauwa!
" naje asubutin banga likita ba!.
" garin yaya?
" ta bashi labarin duk abunda yafaru..
" to Allah ya shiryemu ya kuma tsare mana zuciyo-yin mu!
" Ameen..amma kayi hakuri nayi hira da ba maharra mi na ba!
"Bakomai Amira komai kamawa takeyi..
" nagode mijina...
Amina tana kwance adaki alamun bacci takeji sallamar taje tayi sauri ta amsa acikin ranta sannan ta rufe idon ta..
" haris yana kallonta amma kawai yaje ya kwanta intee ya dauka yasata agadonta tare da yi mata addu'a, a hankali ya fara shafa Amina...
" jiyowa tayi tace yaya bacci nakeso..
" kallonta yayi idon sa ciki da tausayi muryar sa kasakasa yace meena Akwai wanda yafine agurinki? Dazu k'i kagama gayamin kina sona ashi ba har cikin zu...
" rufe bakinsa tayi da hannun ta haba yaya yazakace haka?
" ta yaya bazance haka ba kinaso ki sakane awane halin ne?
" ba haka bani ba!
" to nunamin ingani...
" cikin kunya ta rungumesa nan salo ya canja!
Da safe Amina zatayi wa intee wanka sai ga haris ya shigo...
" Yaya ina office din?
" ke am tried yau bazanji ba sai dai gobe kawo intee nayi mata wankan!
" haba wanka ai sai mata!
" ai nema mahaifinta ne..
" yaya ak'wai mutane dayawa da suk'e son su samu sana'a, wa suma su samu lafiyar fita, wasu sun buga koina amma basu samu aikinyi ba, Amma kai Allah yabarka da lafiyarka da kuma aikin ka ka girma ma shi sai Allah yasa maka Albarka...
" hmmm hakane meena amma..
" kayi hakuri in maganata ta bata maka rai..
" haba meena Allah yayi miki albarka bari na tafi..
" bayan ya shirya yafito Amira tace my sugar babu cubes fa!
" okay ku gayawa auwalu wanda kukeso sai ya siyo muku!
" okay adawo lafiya..
" bilkisu dake gife tace Allah ya tsare mana kai maigidan mu!
" wata dariya yasaka mai cike da kayatarwa sannan yafita..
" bayan karfe sha daya bilkisu ta fito daga kitchen,mum intee wannan dan naman yau aka kawo ne, gaskiya yayi mana kadan!
" A gaskiya mudinga godewa Allah ku duba wanda suke kasa da kai, Allah yabaki lafiya wasu nema sukeyi Allah yabako dukiya, uwa uba kinsamu miji nagare!
" bilkisu tace Allah dai kawai ya shirye mu!
" Ameen sukace Atare...
Ayayin da haris ya'isa office yatarar da Alhaji isa har yazo cikin mamaki suka gaisa yace Alhaji wai yanzu bakada matane!
" ina da su mana haris kasan tara matan ne sai hakuri kullum rigima kawo kara da sauransu yanzu nazama alkalin dole..
" yahaya yayi dariya haba alhaji ai ingaya muku akwai shekarar nema da matanah suka kusa haukata ne bansan lokacin dana dakko bulala ba nace kowacce tafita tabarmun gida ko ranta ya bace!
" to ya kayi da yayan naka cewar haris?
" kanwar hajiyar mu na dakko ta zauna dasu sukuwa sai da sukayi wata 2 a gida lokacin da suka dawo ma daina kulasu nayi da kansu suka shirya...
" Lallai Allah yakara mana kaunar juna!.....
" ameen
Amina tana kitchen tana hada zogale bilkisu ta fito tanata Amai aguje kuma ta koma bandaki sai zawo...
*Urs Nana diso*
http//:nanadisoo.mywapblog.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[12/2/2016, 1:31 PM] Cvrieh sier verbier✨: _100-105_
*MATA NAH*
_NA NANA DISO_
Amina tana kitchen tana hada zogale bilkisu ta fito tanata Amai aguje kuma ta koma bandaki sai zawo..
Agigice Amina tafito tana lpya?? Amira ma tasakko tace mum intee what wrong?
" kinga dai kamar amai kuma naga tashiga toilet da gudu..
" lah ai shine ma subhnlhi..
" bilkisu ce tafito tana ruke ciki, nan ta wadi akasa kukaine asubuti cikina..
" amina ce tace ni banida kudi ahannu na wallhi..
" amira tace nema dazu nayi kyauta, gashi asubutin suna da matsala..
" ahankali bilkisu tace akwai acikin jakata..
" Amira bata jira watawata ba ta bude dakin, bude jakar da zatayi taga kudade ba adadi hakan yasa tayi tiress chan kuma ta dakko tafito..
" key din mota amina ta basu directly asubutin suka huce...
" Amina dake faman shirya abunci a dinning ga intee sai kuka takeyi zaunar da ita tayi sannan tafara neman number haris bugo daya ya dauka..
" meena ya'akayi?
" bilkisu suna diamond babu lafiya!
" subhnlhi mai yasameta?
" kaje suna can..
" okay Bari na tafi..
Bayan sallar isha'i suka dawo gida cike da tausaya wa halin da Bilkisu take ciki..
" a carpet suka zauna haris ne ya rungumeta sannu my billy zakice Abincin ne?
" kada masa kai tayi Alaman aa!
" haba billyna kice ko kadanne sai na baki magani!
" Amina ce tatashi ta zubo mata gashi nan kabata!
" Amira yanaje kinyi shiru?
" hmm wallhi bakomai kawai dan tunani nakeyi rayuwar nan tsoro take bani yanzu kake akwance anjima Allah zai mikar da kai, yanxu zakaci wa wane mutunci anjima kaima a cimaka, shiyasa zaman lafiya yafi komai!
" haris ne yayi mata wane kallo mai ciki da kauna sannan yafara bawa billy abinci..
" a hankali bilkisu tace cweety na koshe bacci nakeji!
" okay bari na kaiki ki kwanta cak ya dauketa sai kan gado..
" takara duban sa tace kayan jiki na sunyi mun nauyi!
" a hankali yashiga rabata da na jikin sannan ya saka mata wasu jikinsa duk babu kware! Zai fita kenan..
" tariko hannun sa please ka barni naje dumin jikin ka ta hakan zanje sa'ida!
" to yace mata ya rungumeta a kirjensa har tayi bacci..
" duk da ba girken Amira bani ba Amma taji haushin dadewar da haris yayi cikin dakin bilkisu Amma sai ta sare sakamok'on Amina da taga bata damuba..
" haris ne ya dauke intee kinga tafara kokarin rarrafi!
" Amira tace ai dama girman ba wuya!
" uhm ni kwanace mi yake damun bilkisu ne?
" haris yana wa intee wasa yace basu bada result ba sai gobe!
" eyyah Allah yabata lafiya..
" sukace Amin..
" yanzun ma banso rabuwa da itaba jikin nata zafi!
" Amira ce tayi masa wane kallo tace ne sai da safenku!
" Amina tace Ai da sai ka koma!
" dariya yayi sannan ya hau sama tare da intee system dinsa ya dakko yayi wane aiki sai gurin 2 ya dauke intee suka shiga dakin Amina!
" tsayawa yayi yana kallon yadda takara cika! Addu'a yayi sannan ya ajiye intee Akan bed dinta shi kuma yanufi Amina yasan zai yi wuya Amina ta yarda dashi Amma ina yakasa runtsa idanunsa..
" matso daita yayi sannan yafara lalubarta nan tayi maza ta tashi..
" kada ka kara tabani kaje gurin wacce bakaso karabu da'ita maba!
" haba my meena menene yajawo haka?. " kallon satayi ciki da takaice tace ai kasan ba girken ta bani ba Amma kaje kazauna a dakin ta wayasan ma me kukayi??..
" haba meena menene yajawo zancen nan duk tausayinki?
" au komai aka gaya maka tausayi ne?
" amma dai kinsan batada lafiya kuma..
" katse shi tayi ai daman baka sona..
" sauri yayi yasa bakin sa anata sai da ya tabbatar jikinta ya mutu sannan yafara sarrafata!..
Da asuba bayan tayi wanka ciki da mamakin irin hali na mijinta takeyi da zarar yataba mace nan da nan zata susuce!
" haris ne ya katse mata tunanin ta, an aminci naje na duba billyta?
" wata irin harara tayi masa to to dana hanaka ne?
" aa ainaga jiya nayi lefi!
" kuka ne yafara kwanki idon ta tace ai naga baka damu da...
" stop it meena! Anya kisan irin son danake yimiki? Kice mace tak wacce sonta yafara darsuwa a zuciya ta!
" murmushi tayi sannan ta shiga toilet!
" haris kuwa dak'in bilkisu ya shiga tarar da'ita yayi tana shafa mai cikin wata siririyar murya tace ina kwana!.
" haris ya tafi cikin duniyar tunani me isa bilkusu take zautashi!.
" tashi yayi yace lpylou yajikin nake?
" nasamu sauke..
" okay yace sannan yabar dak'in...
Bayan sun karya suna zaune sunata hirar su..
" my sugar yau bazaja office ba?
" walhi mumy nake jira yanzu tace zatazo, kafin ya karasa magana ta shigo!.
" Duk suka tsuggunna suka gausheta!.
" cikin murna tace lafiya lou, inteesar yanaga kin kara wayo?
" haris yace ai rarrafe ma takeyi!.
" ah ai kuwa sai a yayeta na tafi da'ita!.
" haris ne yakalle amina da tayi shiru!...
" mumy tasaka dariya au Amina yayin ne baza'abani ba!..
" ai ban isa na hanaki ba mumy banason tai tayi miki rigima shiyasa..
" to ai ni nace zan iya!
" haris yace karki damu mumy za'a kawo muku ita soon!..
" yauwa yanzu naji magana!
" bari natafi office ana jira na!
" mumy tace Allah yayi maka albarka Allah yatsare ya kuma baka ikon yiwa matanka Adanci!.
"Ameen mumy ta sannan yafita..
Uhm muje Amira nayi alwala kada walha ta huce ne!
" tohm mumy , sama suka hau sannan ta biyota, bandakin ta bude mata, ita kuma ta shinfeda mata dadduma!
" ga sallayar mumy!.
" inkiya tayi mata da hannu!...
" tana ganawa smira tace mumy kada natsayar dake, wannan addu'ar dakikaye banyan kingama alwala menene falakarta?
Murmushi mumy tayi tace " Manzon Allah s.a.w yana cewa:Babu wani daga cikin ku da zaiyi alwala sannan ya kyautata alwalarsa, sannan bayan ya gama yace:
{اشهد ان لاإله إلا الله وحده لاشريك له واشهد انا محمد عبده ورسو له}
Face an bude masa kokofin aljanna guda Takwas,yana shiga ta inda yaga dama!@رواه.مسلم.
" kai Amma nagode..
" mumy tace ai bakomai...
Amira tana sakkowa tasamu guri ta zauna bilkisu tanata wasa da intee, bilkisu danAllah in tambayi ki mana!
" inajinki amaryar mu..
" murmushi tayi sannan tace jiya da bakida lafiya naga kudin da suka fi karfin kaina ajakarki aina kika samu!
" diris bilkisu tayi tace to me amira ta ke nufi ne? Amira kenan akwai kudadin da haris yakeyi mana amatsayin kyauta da kudin da yake bayarwa inze fita, a gaskiya ne bana kashewa inkika ga taba kudin to abune mai mahimmanci?
" hada baki sukayi sukace saboda me?
" gidan mu inada yayye da kanni akwai marayu aciki dan haka duk abunda nasamu sunake bawa, hakan yakan faranta ran mamana har tana shimin albarka, rayukan mu an halicce su ne dan su zauna na dan wane lokaci, bansan tsakani na da iyayena ba wazai fara mutuwa dan haka, dan kuwa danasani bayan mutuwa abune mai ciwo da zuciya ke wahaltuwa akanshi, shiyasa nake taimakawa iyayena ina fatan murabu lafiya!
" Amira ce tace kwarai kuwa nema kin tunamin da tawa tsohowar inshaaAllah nima zan dinga faranta mata!
" Amina da hawaye ke kokarin zibo mata wasu maganganun ummin ta ta tuna, (Amina wata rana baza kiganni ba zakiyi kuka! Amma karki damu duk mai rai mamaci ne ki kyautatawa mijinki kije tsoron zalunci kiyi hakuri da zaman duniya kema wataran zaki muce.) Hawayen fuskarta ta goge sannan taga mumy har ta zauna..
" naji dadi tabbas da naganku a tare a duniya babu abunda yafi zaman lafiya babu abunda yafi hakuri, dan haka ku cigaba dayi! Allah yayi muku albarka!
" Ameen sukace tare da fadin ki gaida gida!
" bilkisu tace mum intee pls kibar mun intee takwana a dakina!
" shiru tayi can tace to..
" bari mushiga kitchen to..
" okay bari na shirya intee zamuje gida yau!
" to ki gaidasu.
Amina tana shiga daki takira haris bugu daya ya dauka!
" mum intee ya'akayi?
" zanje gida ne!
" okay tohm ga auwal nan zuwa ku tafi tare da daddare zanzo!
" tohm nagode Allah ya tsareka ya kuma kareka..
" Amin my meena...
" sallama sukayi sannan suka tafi! Suna isa ta hadu da ya sagir a waje tace lallai yau nayi gamo!
" hahaha kidai bari..
" gaskiya uncle baka kyautawa wallahi baka taba zuwa gidana ba!
" yi hakuri meena bari naje nadawo tace to tana hawa sama ta rungume mamie!.
" saukar yaushe amina?
" wallahi yanzu naji inason in ganki shiyasa nazo..
" aikuwa farida tana bangaran hajiya itama tazo!..
" lafiya dai mamie dady intee yana yawan cimun yaganta agida!
" wallahi farida tazama mara hakuri gaba dayanta bari dai tazo!
" uhm Allah yasawake..
" tana shigo wa tace aa kaga uwargidan yaya haris kinga yadda kika kara kiba!
" kidai bari yaya ne kison kibar wallahi, kinsan duk Abunda yakeso dole naso shi!
Mamie kinsan me?
" sai kin fada!
" wato ita rayuwa hakuri ne acikin ta, mijina yana kula dani kamar yadda nake kula dashi!
" farida sai duk taje wane iri..
" ya sagir ne ya shigo da intee!
" uncle har kun dawo ina anty ta?
" mamie ta anshi intee..
" eh mun dawo,!
" farida tace ai ingaya miki sadiya rigima sukeyi da ya sagir sosai!
" garin ya ya uncle..
" kidai bari meena nagaji wallahi hakuri na ya..
" haba uncle bakace haka ba!
" mamie tace yimun shiru kaima ai da laifin ka baka cin abinci da ita abubuwa dayawa bakayi mata! Bari naji dak'in baba..
" Amina tace haba uncle kyakyawar mu'amala ai tana da dadi baka maida gidanka kamar jahannama ba! Haba uncle ai na mijin kirki yaso yace abinci da matarsa! Mace mur-mu-sas-shiyar leda ce babu abunda yake jawo hankalin ta sama da murmushi da magana me kyau! Ko yar fita kayi sai ka dan siyo mata dan Abu, uncle kai dakake tafiye tafiye ba kowacce macece zata iya zama dakai ba, Amma anty sadiya babu ruwanta!
" Amina kenan inshaa Allahu zan chanja!
" yauwa uncle kagaida ta!
" zama tazo tagaida ke yauwa inajera..
" ke kuma farida meke shirin faruwa?
" ai munshirya nagane kuskure na, ga zuma da miski hajiya ce tasiyo mana tsaraba!.
" kai amma mungode..
Kisane fari hakurin zama da bakin ciki ko damuwa na tsawon shekaru dubu wallahi yafi sauki akan zaman minti guda acikin jahannama!..
" hakane yaruwa tawo muje kigaida baba sai na ajiye ki agida..
" tohm shikenan
Bayan ta dawo gida wanka tayi tafito palour tana kallo, haris ne yayi sallama kowa yace sannu da zuwa!.
" Amina kuwa wane kallo yayi mata da Alamar bazai amsa tataba!
" tsarguwa tayi aranta me tayi masa?
" rungume bilkisu yayi tare da shafa cikib ta hope kina kular mun da baby na!. ..
" gaban Amira ne ya buga cikin karfi hali tace aa munkusa samun baby kenan!
" Amina tace aikam ankusa ayiwa intee kani!
" kunya taje sannan tabar palour after sunci abinci..
" Amina tana shirin kwanciya haris ya shigo mekika maidani badai danaci kitsaya mutawo tare ba?
" haba yaya menene nafada kayi hakuri pls kuma baba naji yace yana naimanka!
" ai yayi miki kyau hakan!
" washe gari sunyine suna waya da grandy da khalil nan suke sanar mata da zai tafi madina karatu!
" waya biya masa grandy?
" mijinki ne!
" Mijina kuma..
" adaidai lokacin haris ya shigo rungumesa tayi tana murna!
" bakomai my meena nema kanina ne nan tafara kissing dinsa salo ya canja!
Akwana atashi babu wuya yau cikin bilkisu wata tara dakyar take takawa!
" wata safiya Amira tasha kuka da istigfari akan Allah yabata ikon cin jarabawar da Allah ya tsara mata, ahaka haris ya sameta yadinga bata baki har tayi shiru!
" bayan haihuwar bilkisu ta haife mace kamarsu daya!
" nan Amina tafara laulayi haris yayi yayi taje asubuti amma tace ita sam bazata ba!
Ran suna anyi budire sosai da sosai!
" haris yana office sai yafara dariya bakomai yake tunawa ba illah kishin da matansa sukeyi mai ban sha'awa yau in wannan tasa kaya masu kyau gobe wata zata saka wanda yafisa kyau girke kuwa ba'a nagana shiyasa ya'ajeyi wane tumbi kowacce farin cikin tafaranta masa takeyi!
" akwai lokacin da Amira taje gida babu Abunda takeyiwa hajiyar ta sai kuka!
" Amira ki kwantar da hankalin ki zaki haihu kema!
Shekaru sun fara shudewa intee harta shiga primary 2, kaninta haneef yana nusery2, sai abubakar kanin ta shi pre nusery yake..
Haris yazama babban mutum duk inda ya shiga kirar sa akeyi!
Yanzu tafiya da daidai yakeyi..
Cikin ikon Allah Amira ma ta samu ciki abokanan zamanta sun tayata murna sosai!
" haneef yana kusa da babansa yace dady zansha ice cream!
" intee tace mumy jiya tayi mana yana frige! Yakalli mamansa bilkisu yace wai haka ummi?
" eh yana frige..
Yau da gobe babu wuya Amira har ta haihu ta haife yarta fatima mai kama da haris...
A kwana atashi yara duk sun girma rigima gidan haris sai da babban dalili..
Kamar kullin yau yana shigowa gida yace! Intee, haneef, abubakar, fatima...
" sukace yes dady duk suka rungumesa fatima kuwa tafiyar batayi karfi ba!
" nan su Amina suma suka fito suka rungumesa!
Kallonsu yayi yace Allah yabarmu tare *mata nah* kunza mimen abun alfahari *MATA NAH*...
Suma sukace Allah yabarmu tare yakuma karamana zaman lpya!
*Ameen MATA NAH*
Sauri sauri nakeyi domin jiyowa zuwa wane page din! ina ashe ne na karar da bairon! Murfi ne ya wado kan littafin ban ankara ba naga ashe saura bango littafin ya Kare! Dariya nayi sannan Na rufe ciki da tunani kamar haka-:
- Hakuri yana gyara zaman iyali,yana karfafa zumunta,yana
maganin fitina da tashin hankali yana kawo sulhu da yafe laifi,yana gadar da halaye nagari,yana inganta zaman ma kwabta,yana haifar da alheri mai yawa duniya da lahira...
- Hakika Ba wanda kuskure ko matsala ba zata riskeshi ba cikin
harkokin rayuwar sa a tsakanin sa da iyalan sa, ko ma kusantan sa, ko al’ummar da yake raye a cikin ta maganin kowacce irin damuwa
shine hakuri, addu’a da mayar da al’amarin ga Allah...
- *Mayar da komi ga Allah yana sanya natsuwa da kwanciyar Hankali,da kawar da gaba,ko adawa ta zargi da yawan fada da juna Zafin nema baya kawo samu, kuma wayo da dabara ko yaudara basa zama sanadi sai da amincewar Allah*
- *mu natsu mu koma ga Allah wajen nema, addu’a,rantsuwa, dogaro,kwadayi da tsammani Yalwa da falalar Allah tana da yawa, kowa Allah yaso zai bashi daga ni’imar sa, ko a jarrabeshi gwargwadon imanin sa*...
- *kada ka dorawa kowa laifi in ka rasa, kuma kada kayi alfahari in ka samu Abinda ka rasa tabbas dama ba rabonka bane, abinda ka samu hakika dama kai aka qaddara-wa shi*...
*KISHI*
*Abin da wasu matan yanzu keyi da sunan kishi sam sam baza a iya kiran shi kishi ba, sai dai a kira shi da abin tir da Allah wadai!!!*
*Wasu matan kan bi hanyar ’yan tsubbu da bokaye (wa’iyazubillah) wai don su samu biyan bukatun su na kada a yi musu kishiya*...
*Manzon Allah (SAW) fa ya gaya mana cewa duk wanda ya je wurin boka ko dan duba, kuma ya tambaye shi kan wani abu har ya gaskata shi, to ya kafirta da abin da aka saukarwa (Annabi) Muhammad sallalllahu alaihi wa sallam.*
*A wata riwayar kuma ba za’a karbi sallarsa ta kwana arba’in ba!*
*Wannan wanda ya gaskata kenan, ba tare da ya aikata sihirin ba*
*Haba baiwar Allah, ga mahaliccinki, mai kowa mai komai, wanda ba bu abin da zai faru cikin halittarsa sai da saninsa da izininsa, wanda shi ne Mabuwayi, babu wanda ya gagare shi, babu mai iya ja da shi, ga shi da kansa yana ba ki alwashi cewa in kin dogara da shi to ya isar maki, wato ya isar maki daga wata cuta da ta shafe ki daga wani dan Adam ko aljan sai da izininsa, ya isar maki daga abokin gabarki, ya isar maki daga zaluncin azzalumi cikin sammai ko kassai, cikin duhun dare ko ido-na-ganin-ido, ya isar maki daga mai nufin jefa miki bakin ciki a zuriyyarki...*
*ko a dukiyarki ta hanyar raba ki da abin kaunarki, miji ko da ko dan uwa ko makaman tansu, ya isar maki daga dukkan sharri daga dukkan mai nufin sharri Don Allah ki daure ki dogara da shi, za ko ki ga cika alkawari _ “Wa ya fi Allah cika alkawari?_” (Suratut Taubah: 111)*
*Ma'aurata*
- zaman lafiya yafi komai arayuwa farantawa miji zama dashi cikin amana da jindadi, hakuri da halinsa ...
*The Messenger of Allah (peace be upon him) said: "Any woman who dies, and her husband is pleased with her, will enter Paradise." [Ibn Majah, Book 1 Hadith 59....*
- *Dress pleasantly/attractively karki manta mijinki ne Mostly women dress properly in zasu fita and at home they wear worst clothes..!*
*Ya kamata kisa Kaya mai kyau so that ur husband will feel good when he looks at u, yaji dadi....*
- *Encourage him to do good deeds ,Hakan zaisa yaji dadi ya kuma yi alfahari dake*...
- *Send your husband a text message out of the blue with a message of love!♡♡♡ kin dai gane!*
- *May god bless all of us and open our minds and hearts so that we can help each other; regardless of who they are;remember blessing has no color*...
ALHAMDULILLAHI ANAN NAKAWO KARSHEN LITTAFINA MAI SUNA *MATA NAH*
Time:-1:26
Date:-friday 2nd December 2016
*Biyu ga watan rabiul-auwal 1438*
GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATA GA MANZON RAHAMA (SAW)
ABUNDA MU KAYI BA DAIDAI BA ALLAH YA YAFE MANA!
WANDA MU KAYI DAIDAI ALLAH YABAMU LADA!
KU DINGA DAUKAR ABUBUWA MASU AMFANI...
_SAI MUN HADU ASABON LITTAFINA MAI SUNA_
*K'ANDE*
inkiya:- Ni ta dabance!!!
INSHAA Allah Nan ba da dadewa ba!
ﺍﻟﺸﻜﺮ ﻭﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﻟﻠﻨﺎﺱ
ﺑﺎﺭﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ
ﺃﻧﺎ ﺑﺎﻻﻣﺘﻨﺎﻥ ﻟﺬﻟﻚ ﻣﻦ ﺃﺟﻞ ﺣﺒﻚ
♡♡♡masoya na♡♡♡ Allah yabiya muku bukatun ku na alheri
TAKU HAR KULLUM!!!
*NANA DISO (MUTAN MADINA)*
*Urs Nana diso*
http//:nanadisoo.mywapblog.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
No comments:
Post a Comment