DUMBUN SHINKAFA
dafarko kisamu shinkafarki iya adadin dakike bukata, kikai a barzo miki. Kizuba amadanbaci, kirufe ruf da leda sannan kidaura
awuta kikawo murfi kirufe dan ba'aso tiririn yadinga fita. Kitabbatar kinxuba ruwa a kasan tukunyar daidai yadda baxai koneba.
Ki wanke zogalenki, kisaya busheshe yafi Sai kijeka Attaruhu da albasa kiyankasu suma yadda kike bukata,Anaso albasar tayi yawa. Hantarki kitafasa da idan kina bukata isasshen maggi da dan gishiri, kiyanka gutsi-gutsi. Bayan tsakinki yayi laushi saiki sauke kizuba mai
yakamashi, sannan kikawo kayan lambun su zogale nan kixuba, kicakudasu yadda xasu hade jikinsu da tsakin
hakama attaruhu da albasarnan hadida yankakken hantarnanan kihada kisake juyawa, sannan kidan daka maggi da gishiri kadan yadda baxaiyi yawaba kicakuda kimayar wuta.
Kibashi lokaci xakiji yana fidda kamshi sosai kitabbatar yayi kamshi kuma ya dahu sosai yadda akeso,
ki sauke. Xa'a iya ci a haka, kokuma kiyi masa miyar kayan lambu...NANADISO
Bushashen zogalen fa,za'a tafasa shine kafin a hada a ciki?
ReplyDeleteBa sai kin tafasa ba da kin zuba ruwan zafi ki ka bashi lokaci zai Yi laushi.
ReplyDeleteBut shinkafar da an barzo zaki saka a madambaci bazaa dan sa mata ruwa ba hakanan a dry ne?
ReplyDeleteTiririne xay dafa shi baa sa mai ruwa
Delete.good
ReplyDelete